← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 77

Sashe 26

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ita kuwa Ummul a parlour tana shiga taji Hajjajo da Inna suna.
"Wai ni abin mamaki Farouq ya akayi ka fesa turaren a idanun ka? kaiba yaroba."
baiyi magana ba sai latsa woyar shi da yakeyi,
Ita kuwa Ummul gaba d'aya jikin ta ya d'auki b'ari tana jin tsoron kar Hamma Umar ya fad'i abinda ke faruwa a tsakanin su,
Inna ce ta kuma kallon shi cikin tausayawa dan ita tasan Umar da zurfin ciki koma menene ba fad'a zaiyi ba a hankali tace.
"Ko garin fese-fesen turaren nan shine yaje ya fesa a idanun shi,
tunda shi mutun ne ko yaushe ka jishi da turaren a jikin shi."
Usman ne ya girgiza kai cikin kula yace.
"A a kam ba yadda za'ayi ya fesawa kanshi turaren a cikin idanun shi ai ba yau ya fara mu'amalan tuwa da turaren ba ."
ido Ummul ta kuma zarowa dan ganin kamar duk sun ganeta,
sai kallon Hamma Umar d'in take cikin yanayin ya rufamata asiri,
stool ta jawo gaban shi shida ya Usman ta ajiye musu pilet d'in fruits d'in sannan ta d'an dago cikin rawan ido da suka ciki da k'olloh alamar ka rufamin asiri,
shi kuwa fuska ya tsuke cikin kauda idanun shi a kanta,
gaban su Hajjajo taje ta ajiye musu nasu sannan ta zauna tana fuskantar Hamma Umar d'in da alamun neman al'farma,
Hajjajo ta kalleshi tare da cewa.
"Farouq ana maka magana kayi shiru ya akayi ka fesa turaren a idanun ka."
Kai ya juyo cikin sanyi yace.
"Ummul ce....!"
ido Ummul ta zaro woje cikin rawan jiki sai hawaye car-car a idanun ta,
Su Hajjajo kuwa suma ido suka zaro cikin kallon shi sukace Ummul ta fesema turaren?. "
Fuska ya tsuke tare da cewa.
"Ni kam bance ba kaji tsohuwa fa ki tsaya kiji me zance mana."
Usman ne ya tsura mishi ido sannan ya kalli Ummul dake ta rawan jiki ya kuma kalli Hamma Umar d'in da yake kallon ta sai yace.
"Toh Hamma Umar muna jinka."
Tsuke fuska ya kumayi sannan yace.
"Cewa zanyi Ummul ce zata gaya muku yadda akayi na fesa turaren a idanuna."
Ummul d'in suka kallah cikin son jin zance sukace .
"Ummul garin Yaya akayi ya fesa turaren a idanun shi?."
Tsuru-tsuru tayi da ido shi kuwa kallon ta yake yana d'an murmushi yana jiran me zata ce musu,
abin mamaki sai yaga Ummul ta gyara zama ta tokk'oshe k'afafun ta ta d'auki apply ta fara ci a hankali sannan tace.
"Hajjajo waifa yaje yayi wonka ne ya fito ya zauna gaban mirror toh sai nazo ina taje mishi sumar kanshi ina d'an goge mishi sumar da towel,
shine shi kuma yana ta kallona ta cikin madubin ya d'auki turaren wai zai fesa a sumar kan nashi ,
ya kuma zuba min ido ta cikin madubin a haka ya fesa turare kam cikin manyan idanun shi."
Gaba d'aya su Hajjajo kam dariya sukeyi Aliyu ma sai dariya yakeyi,
Usman kuwa anan take ya gano akwai wani abu a k'asa,
shi kuwa Hamma Umar mamaki ne ya rufeshi sosai yake kallon fuskar Ummul yana mamakin yadda ta zame kanta a abin ta kuma maida abin da salon so
lallai mace bata kad'an,
Ita kuwa Ummul kallon shi tayi tare da d'aga mai girma d'aya sannan ta tab'e baki.
Anty Halima kuwa baki ta cije tare da juyawa ta koma kitchen d'in ta kwaso abinci ta kawo sukayi suka sha sunata jira da dariya.

Haka suka wuni har yamma sannan suka shirya suka fito,
a harabar gidan Ummul ta kalli ya Usman d'in cikin zubda k'olloh tace.
"Ayyah ya Usman nima zan koma gida."
lumshe ido Usman yayi yana maijin wani irin yanayi a ranshi a hankali yace.
"Toh ai bani zaki tabbaya ba ki tabbaya mijin ki."
Aliyu ne yayi maza ya karb'e maganar cikin tsokana yace.
"Ba inda zakije Hajia zauna a gidan ki haka kawai ki koma gida kiyi ta takurani,
mu yanzu gidan mu ba wurin zaman ki ehe,
Allah ko Hamma Umar karka barta."
hararan shi tayi tare da kai mishi duka,
shi kuwa sai zillewa yayi ya shiga mota,
Ita kuwa cikin zubda k'olloh tace.
"Hamma Umar inje ko?."
murmushi yayi tare da cewa.
"A,a kam in kin tafi wazai tayani zama a gidan?."
murmushi Hajjajo tayi tace.
"Toh kinji ko? kai Usman shiga mu tafi."
haka suka tafi suna yiwa Ummul dariya shiko Usman tun a cikin motar ya k'asa tsaida hawaye shi abin ya had'e mishi ga ciwon zuciya ga k'aunar abinda bazai samuba ga tausayin halin da d'an uwanshi yake ciki dan ya gane Ummul na azabtar mishi da d'an uwanshi a hankali ya fara jin numfashi sa na toshewa,
a haka suka isa gida, bayan sun sauk'e Inna a gidan ta
suna shiga part d'in su ya wuce kai tsaye kan gado ya fad'a kife kanshi yayi ya rink'a wani irin kuka mai cushe numfashi gaba d'aya jikin shi sai rawa yakeyi lokaci d'aya zazzab'i mai zafi ya rufeshi ciwon kai mai tsanani ya rink'a sarawa zuciyarshi sai har bawa take a d'ari 200,
haka ya rufe kanshi.

Anty Halima Ku suna shiga cikin gidan cikin sa'a ta samu ya Adam yana zaune a parlour Nenne suna hira da ya Sadik da Nenne Aliyu kuwa bayan Hajjajo yabi,
Nenne tana ganin su ta mik'e taje tayiwa hajjajo sannan da dawo ta kai mata abinci da ruwa sannan ta dawo parlour ta gun yaran nata shiko Aliyu tuni ya konta a parlour Hajjajo,
Nenne na shiga suka zauna sukaci gaba da hira har zuwa d'an wani lokacin,
a hankali Anty Halima ta gyara zama ta fuskanci ya Adam da Nenne a hankali tace.
"Nenne! ya Adam Ummul zata kashe Hamma Umar watarana in dai ba'a d'auki mataki a kanta ba."
cikin kad'uwa Nenne ta nemi k'arin bayani,
itako Anty Halima cikin nitsuwa ta yimusu bayanin zaman Hamma Umar da keyi da Ummul da irin azabtar dashi da takeyi.
ya Adam kam hatsala iya hatsala ya hatsala gaba d'aya ranshi ya b'aci ji yake kamar ya fire yaje ya tattaka Ummul d'in,
Nenne kuwa tamkar tayi kuka dan takaici,
ya Sadik ne ya yayi magana .
"Nenne Ummul bata da tausayi in an barta da tunanin ta zata lahanta mana d'an uwa,
kawai ya Adam ya gayawa Abba asan matakin da za'a d'auka a kanta."
rai a b'ace Nenne tace.
"Ni so nake Ku dakamin Ita sai ta dawo haiyacin ta."
haka sukayi ta fad'a bayan anyi sallan ishah ya Adam ya samu Abban su a parlour shi cikin nitsuwa ya mishi bayani,
sosai ran Abba ya b'aci cikin takaici yace.
"Adam ka shirya gobe bayan sallan la'asar zamuje gidan Farouq d'in zanyi maganin abin."
Haka suka yita tattaunawa kan lamarin.
Chapter 26 · 0% Book details