← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 77

Sashe 48

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Itako Ummul a gida Hamman nata yana fita ta koma d'akin shi ta zauna haka nan ta tsinci kanta da yin abinda bata tab'ayi ba duk da zazzab'in da take ji amman taji k'arfin guiwar jikin ta d'akin ta fara tattarewa ta kimtsa duk abinda ya watsa kafin ya fita zanin gadon ta canza mai ta nad'e wannan d'in sannan ta share ko ina ta goge komai ta killaci d'akin sannan tasa turaren wuta mai k'amshi daga nan ta koma d'akinta ta gyara ta fito parlour su har dinning area da kitchen nasu kab ta gyara komai sannan ta shoga kitchen d'in,
karo na forko kenan da tayi niyar tayi girki tare da rebon Hamma Umar d'in dan takanyi girki kam amman bata tab'ayi da rebonsa ba,
shiko in zaiyi itace forkon ci kuma duk inda yake zai dawo ya mata abinda zataci ko yana office yakan dawo yayi girki ta kuma ci,
amman yau da niyarta a cikin ranta zata yi girkin dan inya dawo ya huta,
bayan ta kammala aiki ne ta koma d'akinta wonka tayi mai rai da lafi sannan tana fitowa karano na forko a da ta zauna tayi kolliya na gani na fad'a sannan ta zira doguwar riga a jikinta duk ta feshe jikinta da turaruka tare da murje humra a jikinta,
k'arfe 2:00 pm ta fito parlour bayan tayi sallan azahar,
a k'asa ta konta kan carpet tayi matashi da pillows d'in kujerun
lokaci d'aya kuma gajiyar aikin da tayin ya rufeta sai mik'a takeyi,
shiko Hamma Umar a gidan govnr yayi sallan azahar ana idarwa ya koma ya sallamesu sannan ya nufi gida,
da saurinshi dan yana tunanin Ummul ba lafiya,
yana yin parking ya fito ya nufi cikin gidan a parlour ya sameta tana konce abun mamaki ko ina fes gashi ta raggad'a kolliya sai shek'i takeyi,
cikin mamaki ya zauna gefenta yana kallon dinning table nasu daya ga an shirya kuloli a hankali yace,
"Hmmmmm Halima ce tazo? ".
kai ta juya ba tare da ta fahimci manufar tabbayar ba,
shiko a zatonshi Anty Haliman ce tazo tayi musu wad'an nan aiyu kan,
k'ara matsota yayi yana shak'ar k'amshin jikin ta a hankali yace,
"Kinyi kyau Ummu na wannan kolliya haka duk ni akayiwa ko?".
hararan shi ta d'anyi sannan ta juya kai,
shiko matsota ya kumayi yace.
"Naga kamar kin gyara gidan kamar har da girki ko?",
tureshi tayi sannan tace,
"Kamace ma kenan? ,
kuma ai dama ina wonka ni dai ba k'azama bace girkin ma ai inayi dama banayin mai yawane yau kuma naga baka dawo da wuri bane kuma naga kamar ka gaji shiyasa nayi girkin da rebonka".
wani irin murmushin jin dad'i yayi wanda har a fuskarsa za, a ga tsantsar farin cikin sa ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa tamkar wanda aka cirewa abu mai nauyi,
Ita kuwa mik'ewa tayi ta koma gefenshi a hankali tace,
"ni fa yunwa nake ji".
mik'ewa yayi da sauri hannun ta yaja sukaje suka zauna,
kamar wasa Ummul ta had'a mai komai sannan ta sawa kanta,
ta faraci ba tare da ta kalleshi ba,
shi kam gaba d'aya ya cika da mamaki a haka sukaci abinci,
sannan ya wuce bedroom nashi a nan ma yasha mamaki wonka yayi sannan ya zira jallabiya parlour ya fito ganin bata nanne ya lek'a d'akin ta sai yaga tana sallan la'asar haka shina ya wuce masallaci,
koda ya dawo bata parlor kamar zai lek'a
d'akin nata kuma sai ya fasa ya zauna dan yayi zaton ko tayi bacci,
itako tana jin motsin shigowar shi ta mik'e a hankaki ta fito yana ganin ta ya zuba mata ido dan wani irin kyau tayi wanda bai tab'a ganin tayi irin wannan kyawun ba,
kanshi ta nufa a hankali har tazo gaban shi,
shiko sai ware ido yake yana kallon ta,
kauda kai tayi sannan ta zame a hankali ta zauna a jikin shi,
gaba d'aya yau Ummul ta cikashi da mamaki donko duk abubuwan da takeyi bata tab'a yinsu ba ,
ita kuwa lafewa tayi a jikin nashi tana rik'e da hannun shi duk motsin da zaiyi ta k'ara shigewa jikin shi ta kanainayeshi,
ganin hakan shima ya wore hannun shi ya ruggumeta sannan ya tallabo kanta ya manna bakinshi kan nata,
ido ya bud'e ya tsurawa ma tasu jin yau ba musu Ummul ta bud'e mai bakinta,
idonshi kan nata idanun ya lalubo harshenta yana mata wani irin salo mai tafiya da hankali,
itako sai lumshe nata idanun tayi tana k'ara narkewa a jikin shi,
abu kamar wasa gaba d'aya salon Ummul na wunin yau ya canza ko motsi mai k'arfi ta hana shi yayi duk yadda zai juya tana mak'aleshi,
shi kam har yanzu mamakin ta yakeyi.
Chapter 48 · 0% Book details