← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 77

Sashe 14

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita Hamma Umar ya kawo hannun Usman d'in cikin tsantsar kulawa ,
kan kujera ya ajiye shi sannan ya d'auki maganin shi yazo ya bashi yasha,
a hankali yace.
"Usman gobe zamuje gun Ammin mu."
murmushi Usman yayi sannan yace.
"Toh Allah ya kaimu."
"Amin"
yace sannan suka she ga bedroom d'in a tare sukayi shirin baccin su.

Washe gari da safe bayan sun gama shirin su tsab sannan suka shiga cikin gida a parlour Nenne suka zauna bayan sun gaida Nenne suka fito parlour Hajjajo suka wuce suna zuwa Hamma Umar d'in ya shiga kitchen d'inta da niyar zai d'auki cup,
Sai kuma yayi baya a hankali ya tsaya a bakin kofar yana jin abinda Ummul ke fad'a,
ya Adam da Hajjajo dake bayan kitchen d'in ma suna jin abinda take fad'in ta window ita kuwa cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Nayi alk'awarin har Abadan.....

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 🔟

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'Yan KADUNA duk Nisan da nayi musu Amman dani sai al'fahari suke in sunga novel na ko a fushi suke farin ciki gurbi nasa zai shige da zana jeni mu zauna so suke basu da niyar tsigen fiffige,💃🏻🤝😘 da gaskiya nunan k'auna suke dan sun kirani sunai mini magiya, na jinjina muku mutan Kaduna domin kuna da karamci hakan yasa na sadaukar da wannan page a gareku*

*C*ikin kuka murya na rawa tace.
"Habibi Mustapha nayi ma al'kawarin ni taka ce har Abadan bazan bari wani yayi nasarar rabamu ba,
nayima alk'awarin zan adana maka kaina zan killace maka jikina ba wani mahaluk'in da zai zama hijabi a tsaka nin mu."

Sai kuma tayi shiru tare da sheshshek'an kuka murya na rawa tace.
"Hamma Umar zai rayu cikin bak'in cikin rayuwa tunda har ya kasance a sanadin shi za,a rabamu ,
bazai sake samun farin ciki da konciyar hankali ba gidan shi zai zame mai tamkar kurkuku zai rayu cikin k'unci da bank'in ciki ta yadda shida kanshi zai sauwa k'amin ba tare da neman shawarar kowa ba,
Mustapha tun jiya duk wani tsoron Hamma Umar ya fita a raina na tsaneshi ji nake kamar na kashe sa."

Sai kuma ta saki kuka mai sanyin sauti,
shi kuwa Mustapha lallashin ta yake cikin raunin murya yake cewa.
"Kiyi hak'uri Ummul ki daina kuka ki sani har Abadan kina cikin raina bazan dena sonki ba,
amman kuwa duk yadda nake sonki bazan so sanadi na ki sab'awa iyayenki ba,
Ummul kiyi biyeyya ga mahaifan ki."

Cikin raunin tace.
"Mustapha zanyi biyayya ga iyayena amman bazan yi biyeyya ga Hamma Umar ba zan d'and'awa zuciyarshi bak'in ciki mai tarin yawa sai yaji irin d'acin da ya jiyar dani,
tabbas sai zuciyar shi ta raunatu jinin shi sai ya hau hankalin shi bazai sake konciya ba."

Haka ta rink'a fad'in irin uk'uba da cin fuskar da ta tana darwa Hamma Umar d'in yana jinta,
Hajjajo kuwa da ya Adam bushewa sukayi suna kallon juna cikin jin tsoron furucin Ummul d'in da mamakin yadda take k'ok'ari da niyar cusawa bawan Allah bak'in ciki.

Shi kuwa Hamma Umar a hankali ya juya cikin sanyi fuskar sa a raunane lips d'in shi ya kamo ya ciza cikin jinjina kai ya juya ya fita,
a parlour suka had'u da su ya Adam da Hajjajo cikin mamaki ya Adam ya kalleshi ganin daga kitchen d'in ya fito ita Hajjajo kallon shi take,
shiko ganin kamar zasu zargi wani abu yasa ya d'an yi murmushi cikin yanayin sanyi ya gaida Hajjajo sannan ya kalli Usman dake tsaye gefen Hajjajo yana mik'a mata hannun shi da alamar ta d'aure mai agagon hannushi ,
Ita ko sai kiciniya take ta kasa,
matso su yayi cikin sanyi ya matso ta ya d'an bugi k'eyar Usman cikin kula yace.
"Kai komai baka iyaba agogo ma bazaka iya mak'alawa ba sai da taima kon tsohuwa."

Murmushi yayi yace.
"Toh Hamma Umar ai kaine ka b'atani haka komai kace bazan iyaba banda lafiya kai zaka min."

Dariya sukayi baki d'aya shiko Umar murmushi yayi daga nan suka sallami Hajjajo suka fita suka tafi kai tsaye dicency super market suka wuce suna shiga suka yiwa Ammin su shopping komai na buk'atan rayuwa suka had'a mata kamar yadda suka saba,
daga nan gidan su Ammin su suka nufa.

Suna isa bakin gate ko parking Hamma Umar bai k'arisa yiba,
Usman ya b'alle marfin motar cikin jin dad'i da raha ya d'an d'aga murya yana.
"Ammi ! Ammina ! Ammiiiiii ! Ina kike ne?."

Shi kuwa Hamma Umar murmushi yayi ya juya gun mai gadin ya mik'a mishi key d'in motarsa cikin sanyi yace.
"Isah shigo da kayan cikin gida."
cikin mutuntawa Isah ya karb'a, sannan shi kuma yabi bayan Usman d'in.

Ita kuwa Ammi tunda tajiyo muryar Usman tayi wani irin murmushi mai cike da jin dad'i da k'aunar y'ay'an nata,
ido ta lumshe tare da shak'ar kanshi turaren da ta sani na Hamma Umar ne,
dan shi kafin ya isa wuri turarenshi keyin sallama.

Kai ta jinjina tare da ture y'ar roban da ta k'wab'a lallen gargaji da nufin zatasa a k'afafun ta,
tana k'ok'ari tashi taga Usman har ya iso,
kawai sai ta koma ta zauna cikin yin dariya,
cikin happy tace.
"Lale marhabin da yaran kirki yara na gari y'an albarka abin alfaharin Ammin su."

Da sauri ya k'arisa gaban ta cikin k'aunar mahaifiyar tasu ya zauna gaban ta ,
hannu ya mik'a mata itama hannu ta mik'a mishi sukayi musabaha,
sannan ya zame gefen ta cikin lumshe ido da yana yin shogoba ya konta a hankali ya d'aura kanshi kan cinyarta tare da sauk'e ajiyan zuciya murya a tausashe yace,
"Ammina ina sonki'
Ammina munyi kewar ki."
Kanshi ta shafa cikin kula da k'aunar irin ta uwa da d'anta tace.
"Allah ya muku albarka."

"Ameeen ya rabbi Habibi Ammin mu."

Inna dake cikin d'akin ne ta fito jin muryan jikan nata da kuma k'amshin turaren babban jikan nata,
cikin sauri ta fito,
tana zuwa ta kalli Usman yadda yake zuba yarinta a gaban mahaifiyar tashi ,
dariya tayi sosai tace.
"Shin wai kaika kam Usmanu baka ganin ka girma ne gankafa tsoho da kai."

Kallon ta yayi cikin dariya yace.
"D'a baya girma a gaban iyayen shi,
na rasa d'umin jikin Abba na tun ina da shekara d'aya kinga ko dukda haka Hamma Umar na ya zame min madadin Abba na."

Murmushi sukayi dukan su,
dai-dai lokacin kuwa Hamma Umar yayi sallama cikin sanyi,
fuska a sake Inna ta amsa mai gami da cewa.
"Umaru sanda kafi mata yanga Umaru kafi k'arfin kabi mace sai dai ta bika Umaru sanda mai k'amshin al'miski Umar mai yawan kyauta da tausayi."

Murmushi yayi cikin sanyi yace.
"Bakya gajiya da surutu ne ke kam?."

"Ya zanyi in gani ance ma kowa irin Kane mai tsadan magana."

Kallon ta ya d'an yi cikin sanyi yace.
"Allah ko Ammin Inna ce ta b'ata miki yaro da surutu kinga Usman ko duk surutun ta ya d'auka."

"Ehh d'in na b'atashin."

Shi kuwa Usman dariya kawai yake dan yasan dama za'a rina,
itako Ammi murmushi kawai takeyi tana kallon fuskar d'an nata,
shi kuwa Hamma Umar a hankalin ya matso gaban Ammin nashi cikin girmamawa da tsananin k'aunarta ya durk'usa a gabanta guiwa bibbiyu cikin sunkuyar da kai ya cire hular kanshi,
ya k'ara matsota tare da sunkuyar da kanshi.
a hankali Ammi ta d'ago hannun ta cikin sanyi ta dafe tsakiyar kan nashi sannan ta kalleshi cikin kula tace.
"Allah yayi muku albarka rabbi ya karemin ku aduk inda kuke Allah ya tsare min imanin ku."

a hankali ya d'ago hannayen shi duka biyu ya dafe hannun ta dake tsakiyar kanshi cikin sanyi yace.
"Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati ,
Ammi Allah ya kare mana ke."
"Amin Amin"
tace sannan ya koma ya zauna gabanta ya tonk'oshe k'afafun shi yana fuskantar ta,
shi kuwa Usman yana konce kanshi na kan cinyarta shima yana fuskantar d'an uwan nashi.

Wannan shine d'abi'a ko once al'adarsu Hamma Umar muddin suka zo gunta.

Ita kuwa Inna sai murmushi take tana kallon d'iyar tata da yaranta,
itako Ammi ajiyan zuciya ta sauk'e cikin sanyi tace.
"Farouq ya jikin d'an uwanka?."
kai ya d'an d'ago ya kalleta a hankali yace.

"Ammi da sauk'i sai dai Usman sam baya son bin dokan likita komai ya samu ci yakeyi yayita d'ure-d'ure kuma yasan zuciyar sa nada rauni Ammi kiyi mishi fad'a bana son abinda zai cutar dashi."
ya karishe maganar cikin raunin murya

Hannu Ammi tasa ta kamo kunne Usman d'in cikin hukuntawa tace.
"Baka ji ko?."
k'ara ya d'an saki cikin d'an yarfa hannu yace.
"Kai Ammi ninefa banda lafiyar amman kuma wai sai Hamma Umar zaki tabbaya ya jikina d'in,
shiko ya fiye tsare-tsare."

Dariya Inna tayi tace.
"Baka dai ji shiyasa."
.dai-dai lokacin yayan Ammin nasu ya shigo shima dariya yakeyi d'an yana matukar k'aunar yaran k'anwar tasu.

Bayan sun gaggaisa ne,
sukaci gaba da hira,
Usman yana zaune gefen Ammin su yana bare banana yana mik'a mata tanaci inya bata d'aya sai ya kuma bawa Inna sannan ya mik'a wa kawun nasu pilet d'in,
shi kuwa Hamma Umar zaune yake kusa da Ammin nashi yana rik'e da hannun ta yana yanke mata farce,
abinda tunda Umar ya girma shike yanke mata farce,
yakan shirya sam musamman dan yaje ya yanke mata farce kuma hakan shike yankewa Usman ma fartatunshi.

Suna cikin hiran kawun nasu ya d'an yi gyaran murya cikin sanyi yace.
"Umar kwana ki su Abban ku sunzo sun min baya nin batun auren ka da d'iyar Abban naki,
mun tattauna maganar kuma yadda sukayi yayi dai-dai,
toh shekara jiya sunzo sun shaida min asabar mai zuwa za'a d'aura auren sun kuma cemin sun gama komai za'a fara bikin nanda kwana 3 ,
toh Amman duk da sunce sun gama komai mukuwa mun had'a kayan lefen ,
yanzu haka Antyn ku sun tafi kai lefen ne shiyasa kukaji gidan shiru."
Chapter 14 · 0% Book details