Sashe 15
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ya d'an d'ago ya kalli kawun nasu da Ammin shi sannan ya kalli Inna da Usman a hankali yace.
"Dama nazone in shaida muku batun,
ashe Abba har yazo."
sai ya juya gun Ammin shi murya can k'asa yace.
"Ammi ban nemi auren nan ba su Abba bani kawai sukayi shiyasa baki tab'a jin na miki zancen ba ko Usman ban gaya mishi ba dan nima a satin daya wucene suka gaya min,
amman Ammi ya kika gani kina son abin ko a barshi?."
Murmushi tayi tare da shafa kanshi cikin kula tace.
"INA so Farouq ina al'fahari da wannan had'in fatana Allah ya baka ikon rik'e amanar da suka baka ka kular musu da d'iyarsu fiye da yadda suka kula da kai da d'an uwanka."
Cikin rauni yace.
"Insha Allah Ammi yadda kikace haka za'ayi."
Shi kuwa Usman murmushi ya rink'a yi cikin jin dad'i da wani yanayin da zuciyarsa keyi ya kalli Hamma Umar d'in yace.
"Ko zakayi zurfin ciki ga kowa a duniya ni ban canccanci kayi zurfin ciki a gareni ba."
Kan Usman d'in ya dafa cikin sanyi yace.
"Ba wani abu nawa wanda zan boye maka a duniya,
Abba ne ya hanani in gayawa kowa shiyasa B'iyaye na ka gafar ceni."
Rik'e hannu Hamman nashi yayi cikin happy yace.
"A duniya zanyi fushi da kowa amman banda kai da Ammin mu ina farin ciki in nagan ka cikin farin ciki."
Murmushi yayi sannan ya kalli kawun nashi cikin sanyi yace.
"Kawun in nayi Aure zan d'auki Ammi na da Usman su koma gidana nima na samu ladan mahaifiya ta da k'anina."
Kai kawun ya juya mishi alamar a,a sannan yace.
"Banzan hanaka ba Umar amman kaga auren naku kamar auren cushene akayiwa yarinyar nan dan haka sai kaga ya yana yin zaman naku zai kasan ce."
cikin sauri Ammi tace.
"A duk inda kake kana samun ladana ni kam d'an uwanka kuma ai kaine jigonsa,
nima zan kula da tawa mahaifiyar."
Shiru kawai yayi dan shi kam a ranshi ya kudurta yana son mahaifiyar shi ta kasance kusa dasu.
Daga nan sukaci gaba da hirarsu,
haka suka wuni cikin farin ciki,
sai dare suka tafi.
A gida kula Ummul tunda matan su Kawun suka kawo kayan auren,
yayin da su Mama matar Daddy da Anty Halima da k'annen Nenne suka tarbi bak'in Ummul ta shige d'akin Hajjajo ta rink'a wani irin kuka ,
haka ta wuni kuka baci ba sha ta k'aura cewa kowa ta k'aura cewa komai gani take duk ba masoyan ta bane .
Haka tayi ta kuka har dare,
Anty Halima ce ta shigo tare da Ya Usman cikin takaici tace.
"Ummul kiji tsoron Allah ki tausayawa kanki yanzu wannan kukan maganin me zai miki?."
Kuka ta k'ara sakewa cikin dashewar murya tace.
"Anty kiji yadda Hamma Umar yake harkokin sa shi ko a jikin sa ni aka cusawa bak'in ciki,
na tsani Hamma Umar bana sonshi ko a matsayin d'an uwa bare abokin rayuwa."
Tsaki Anty Halima taja sannan ta juya ta fice tana cewa.
"Tunda bakya jin magana kiyi duk yadda kike so,
Aure ne dai saura kwana 6 nima daga gobe zanzo su Anty Shuwa kuwa suma gobe zasu zo dan su fara shirya ki."
Tana kaiwa nan ta fice abinta,
ita kuwa Ummul sai hawaye,
Ya Usman ne ya matsota cikin sanyi yace.
"Kiyi hak'uri kibar kukan Ummul kina soyamin zuciya da kukan ki,
Ummul ko so kike zuciyata ta fashe."
Shiru tayi cikin tausaya mishi baki na rawa tace.
"Ya Usman kasha maganin ka."
Murya a raunane yace.
" ko nasha maganin
ba zaiyi aiki ba in har baki bar kukan nan ba."
Cikin tsoron halin da zai iya kasan cewa,
tasa hannun ta share hawaye ta,
murya na tace.
"Nayi shiru ya Usman."
"Toh" yace sannan ya kamo hannun ta suka fito parlour abinci ya bata ta d'an ci .
Haka abu yake tafiya ba mai iya lallashin Ummul sai Usman kuma ba wanda take saurarawa sai shi bata cin abinci Sai in ya Usman d'in nata ne matsamata bata shiri da kowa sai shi shiko Usman shi kad'ai yasan cikin halin da yake rayuwa yana boye sirrinshi a zuciyar shi,
abinda bamu saniba shin zuciyar Usman zata iya jurewa kuwa? .
Yau talata tun da sassafe gidan su yake cike tib da bak'in haka yasa Ummul ta takure kanta cikin d'akin Hajjajo akan gadon ta mai rumfa,
ko k'awayen ta tak'i su ganta,
tana konce a hankali taji k'amshin turaren Hamma Umar d'in a take taji wani irin tsanarsa na ratsata,
shi kuwa kai tsaye bak'in gadon ya nufa yana zuwa ya tura hannu shi a k'asan.....
By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
page 1⃣1⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*Zan abbato mutanen sokkoto su y'an kwaraine basu da tsoggoma idan kaje ka sanya fad'a musu zasu rik'eka da kyau harda lallamah k'warai-k'warai na gane duniya mai sonka shike yi maka hiddima masoya na na sokkoto kun gaman gata gaisheku ðŸ¤ðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ‘ðŸ»ðŸ¤nakeyi domin kuke raba gardamaðŸ‘ðŸ»ðŸ¤ sokkotawa ina al'fahari daku domin baku da hassada a zuk'atan ku shiyasa na sadaukar da wannan shafi gareku sokkotawaðŸ¤ðŸ˜˜ðŸ‘ðŸ»*
*Ha*nnushi ya tura kasan pillow dake gefen ta da niyar zai jawo laptop d'in shi daya bari a wurin,
lalubawa yakeyi aman baiji inda laptop d'in yakeba dan d'akin yana da duhu gashi kan gadone mai rumfa duk yasha gyara da shimfid'a da labulaye sai ya k'ara duhun,
Ita kuwa Ummul tana ganin shi dan ita ta dad'e a d'akin so duhun yabi idonta shi kuma yanzu ya shigo d'akin shiyasa yake ganin duhun sosai,
tab'e fuska tayi cikin ko in kula tasa hannu ta turo laptop d'in nashi k'asa dai-dai sautin kan yatsunshi ta turo shi,
shi ko da sauri ya sunkuya da nufin yasa hannu ya taro laptop d'in kar ya kai k'asa gudun karta lalace,
amman ina cikin rashin sa'a ta fad'o kan yatsunshi tsinin aggil d'in jikin marfinta ya caki kan farcen babbar yatsarsa,
cakar da a take farcen ya tsage lokaci d'aya jini ya fara zuba a take k'afar ta fara wani irin b'ari dan azabar daya ratsashi gaba d'aya yatsar kuma sai motsi take kamar zata fice a jikin shi,
cikin wani irin azaba dayaji ya ziyarci k'ahon zuciyarshi ya dafe kanshi da k'arfi hannun shi sai rawa suke gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka taso ida nunshi sukayi jazir ya kasa magana sai harshen shi ya d'an zaro ya rink'a d'an kad'awa yana furza numfashi tuni zufa ta keto mai ta sashoshin jikin sa,
harshen yake d'an kad'awa yana fidda sautin.
"Shihhhhhhhh ahhhhshhhhhh."
Sai kuma k'afar tashi daya d'an d'ago yana yarfawa,
Ita kuwa Ummul sai murmushi mugunta ta rink'a yi tanaji dariya nason kufce mata murmushin takeyi tuk'uru cikin jin dad'in azabtar dashi da tayi sai wani kad'a kai takeyi tana magana a ranta.
"Kad'an ma kaji Hamma Umar wannan shine makullin wahalar da zakasha a hannun na,
kaida azabtuwa kun kullah,
Sai kayi kuka cur-cur da hawaye ka sai ka gommace kid'i da karatu sai ka sakeni saki mafi muni wanda zan haramta maka har sai inna nasake wani auren an sakeni."
Kai ta jinjina taci gaba da maganar zuciyar da bata saniba na yanzun ya fito fili cewa take.
"Tabbacin da nake dashi ko ince yak'ini na sani Mustapha bazai sakeni ba har Abadan zamu rayu tare."
Da sauri Hamma Umar d'in ya bud'e idanun shi daya rumtse jin sautin Ummul d'in kan gadon ya tsurawa ido cikin wore idanun shi ,
fuskar ta ya tsare da ido cikin zafin nama ya mik'a hannushi kan gadon,
ita kuwa ganin haka tayi wani irin dira daga kan gadon a guje tayi woje a parlour ta samu ya Usman da su Hajjajo da Inna tare da Anty Halima da Anty Shuwa k'anwar Nenne,
cikin rawan jiki ta koma gefen ya Usman ta zauna cikin tura baki da tsuke fuska,
Anty Halima ce ta kalleta cikin tuhuma tace.
"Me kika aikata? kika fito a guje haka?."
fuska ta k'ara tsukewa sannan ta kalli Anty Shuwa dake ta danna mata harara cikin son yin kuka tace.
"Nayi ai ban sani bane."
Hajjajo ta bud'e baki zatayi magana kenan sai kuma tayi shiru ganin Hamma Umar d'in d'aya fito cikin d'akin nata ,
tafiya yake yana d'ingisa k'afar tashi duk inda ya taka sai jini dake zuba gaba d'aya jijiyoyin kanshi sun taso kanshi a k'asa yake tafiya hannushi rik'e da laptop d'in nashi yayinda d'aya hannun kuma yake rik'e da iPhone d'in shi,
Ya Usman ne da Anty Halima sukayi kanshi da sauri cikin rawan baki Ya Usman yace.
"Hamma Umar me ya fasama yatsa yaushe ya fashe kalli yadda jiki ke zubafa."
Anty Halima kuwa gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin duk jini ya wonke mai k'afarsa cikin sanyi murya na rawa tace
"Hamma Umar a tsaida jinin nan mana ya dena zuba."
kai ya gyad'a musu cikin jarumta da dauriya ya nufi hanyar fita yana ce musu .
"Ba komai fa."
har yake bak'in k'ofar fita,
Hajjajo da Inna sukayi kanshi da sauri cikin kula da tsananin k'aunar jikan nasu suka kalleshi,
kusan a tare suke magana.
"Kai Farouq me ya fasama k'afar?
kayi magana kayi shiru ?."
kai ya jinjina a hankali yace.
"Tuntub'e nayi."
fad'in haka da yayi ne yasa suka rink'a jeromai "sannu-sannu Amman kaji azaba kam ai abinda ya fasa farce ba k'ara min abu bane."
Su tsoppin sun yarda Amman Anty Halima da Anty Shuwa kam sun gane sarai Ummul ce taji mai ciwon dan ganin yadda take zare ido da alamun rashin gaskiya Ita,
kuwa Ummul har cikin ranta take jin dad'in ciwon da taji mishi,
a wani sashin zuciyar ta kuwa tana mamakin yadda Hamma Umar d'in ya rufa mata asiri yak'i cewa Ita ta fasa mishi k'afar,
dan ta tabbaya d'aya fad'a Ita kuwa da ta shiga 9 nema ba 3 ba.