Sashe 33
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*H*annun ta tasa ta damk'o siterin ta rink'a juyashi tare da murza shi da k'arfi tana.
"Allah ka tsaya ni in sauk'a ehe,
ni bazan koma gidan kaba ka sauk'e ni a nan zan tafi gidan Anty Halima."
murza kan motar take da k'arfin ta,
tuni motar ta fara yawo a tsakiyar titi ga ababen hawa dake ta gaban su da bayan su da gefe,
gaba d'aya motar kanta ya kufce,
a firgice yace.
Innalillahi Ummul kin san abinda kikeyi kuwa?."
fizge hannayen ta yayi da k'arfi cikin tashin hankali ganin ya nufi kan wani mai a dai-dai ta yana k'ok'arin hawa kanshi ita kuwa tak'i sakewa sai murzawa take tana.
"Ka sauk'e ni a nan bazan koma gidan kaba bana sonka na tsaneka."
Ido ya zaro cikin tashin hankali ganin saura k'iris ya taka wani mai reke da yake gefen titin gaba d'aya mutanen wurin sai rik'e kai sukayi suna.
"Innalillahi subahanallahi."
shi kuwa Hamma Umar cikin firgici da tsoron ganin zata sashin kisan kai gaba d'aya jikin shi sai rawa yake yi,
cikin b'acin rai ya fizge hannayen ta sannan ya tura ta jikin sit d'in ta koma ta bugi jikin marfin motar sannan ta sake tasowa tana k'ok'arin sake rik'e kan motar,
tsawa ya buga mata cikin zafin rai ya ware tafin hannun shi ya zuba mata mari d'aya wanda saida taga taurari na yawa a sararin samaniya kunnen ta saida ya bada sautin kiuuuu sannan ta kuma jin yayi dum lokaci d'aya zanen yatsun shi suka taso a farar fatarta tuni fuskar tayi jazir gaba d'aya ta rasa ina take dan marin ya gigitata,
shi kuwa da k'er ya samu ya tsaida motar jikin shi na rawa zuciyar shi cike da tsoron karta sashi kisan kai yayi parking a gefen titin cikin sauri ya fito ya nufi gun mai reken da mai a daidaitan hak'uri ya rink'a basu,
da sun hatsala amman ganin yadda yake basu hak'uri yasa sukace.
"ba komai Allah ya tsare gaba a rink'a kula."
"Toh nagode."
yace dasu sannan ya koma cikin motar ya shiga ya zauna fuska a tsuke tamkar bai tab'a dariya ba,
jan motar yayi da gudu ya kama hanyar damaturun,
ita kuwa tunda ya zabga mata marin ta kife kanta kan cinyoyin ta ta rink'a kuka mai cike da takaici,
bai kulata ba,
ita kuwa kukan taci gaba dayi tana sheshshek'a,
a haka har suka isa cikin damaturu a inda suna shiga hadari na tashi iska mai sanyi ya rink'a busawa tako ina sai walkiya ake da d'an rugugi alamu irin hadarin karshen damuna ce,
suna isa yayi parking sannan ya koma ya zauna ya jingunu da jikin kujerar yana jin yadda take kuka,
a zahiri mamaki yake irin tsanar da Ummul ke mishi sannan itace da laifi itace da kuka kuma
har cikin ranshi yaji zafin marin da yamata,
ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yasa hannu ya d'an dagota ya jingina ta da jikin shi hannun ta ya kamo cikin sanyi ya cusa hannun kan k'irjin shi sai kuma ya kalleta a hankali yace.
"Kiji yadda kikasa zuciya ta bugawa dan tsoron karki sani nayi kisan kai Ummul nine ba kyaso amman k'iyeyyar har tana k'ok'arin saki in kashe wasu a banza."
sai kuma yayi shiru sannan yasa tafin hannun shi yana shafa fuskar ta a hankali yace.
"Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi sabida sai inga kamar na k'asa rik'e amanar dana d'auka ne kiyi hak'uri ki gafar ceni banyi niyar tab'a lafiyar jikin kiba."
tureshi ta rink'a yi tana janye hannun ta,
shi kuwa rik'e hannun yayi a hankali ya bud'e d'an durowan gaban motar wani d'an k'ara min kontena ya d'auko bud'e wa yayi sannan ya d'auko wani zoben Diamonds sai shek'i yakeyi tamkar tauraro yatsarta ya d'an d'ago a hankali ya zira mata zoben cikin sanyi yace.
"Kinyi kyau matata yatsarki ta haska zoben."
fizge hannun tayi dai-dai lokacin da ruwan sama ya fara sauk'a ,
bud'e motar tayi ta fice cikin kuka ta koma can tsakiyar harabar gidan ta tsaya tana kuka,
ganin haka ya fito ya rufe motar cikin sauri yaje gabanta hannun ta ya rik'o tare da cewa.
"Kiyi hak'uri zomu shiga cikin gida kar ruwan ya tab'a mu,
kinsan ni bana son ruwan sama ya tab'a ni zai sani zazzab'i."
cogewa tayi fir tak'i shiga daya kamo hannun ta sai ta dasa mai ihu,
ganin haka ya rufe gidan sannan ya wuce ya shiga cikin gida a zaton shi ko zataji tsoro ta biyoshi,
Abu kamar wasa ya shiga,
ita kuwa sai tsuguna wa tayi a wurin ruwan yana ta sauk'a a kanta duk ta jik'e tayi jilik sai d'iga takeyi ga tsawa da walkiya da akeyi,
parlour ya fito rik'e da leima ya nufi gunta,
yana zuwa ya jawota jikin shi cikin rawan sanyi yace.
"Khairi kiyi hak'uri mu shiga cikin gida kar mura ta kamaki d'an Allah mushiga ciki bana so ruwan ya tab'ani."
Jin haka ta fizgota leimar ta cillata gefe haka ko iska ya debeta yayi woje da ita,
shi kuwa da sauri ya d'ago hular rigar shi da take konce a kafad'an shi ya rufe tsakiyar kanshi dan in ruwan sama ya bugi kanshi yana sashi zazzab'i da ciwon kai mai tsananin,
hannun shi kuwa ya hard'e a k'irjin shi tuni ya jik'e cikin rawan sanyi da karkarwa ya jawota jikin shi a hankali yace.
"Toh aikin rama mu tafi cikin gida kiyi hak'uri k'anwata."
cikin kuka tace.
"Ban rama ba kam,
kuma bazan shiga gidan kaba sai in zan rama marin da kayi min."
murya na rawan sanyi yace.
"Na yarda mu shiga saiki rama."
baki ta tura sannan tace "toh."
hannun ta yaja suka shiga cikin gidan ,
suna shiga d'akin ta ya nufa da ita,
a gaban mirror ya tsaya da ita,
cikin rawan sanyi ya cire mata mayafin nata sannan ya zuge zip d'in rigar ta yasa hannu zai cire mata rigar tayi maza a juya tana hararan shi tana cewa.
"Ka barni in cire abina da kaina ."
"Na barki nima bari inje in cire nawa."
sai kuma ya bud'e durowa ya zaro mata riga da wondo wondon iya guiwa sai rigar mai d'an fad'in wuya ta yadda kafad'an ta yake fita inya ta saka kayane mai tashi da sulbi,
kan gado ya ajiye mata sannan ya fita ya koma bedroom d'in shi,
yana shiga ya canza kayan shi sannan ya fito ya nufi kitchen tea ya dafa musu mai zafi wai maganin sanyin,
d'akin shi ya koma da niyar d'auko woyarshi yana rik'e da cups d'in yana juyowa da nufin zai fita kenan ya ganta tsaye a bak'in k'ofar shigowan fuska a had'e tace.
"Zan rama fa ehe."
Ido ya tsura mata cikin mamaki ajiye cups d'in yayi kan mirror sannan ya juyo a hankali yace.
"Toh zoki rama."
shigo wa tayi ta tsaya a gaban shi ta d'an d'ago kanta tana kallon fuskar shi,
shi kuwa kollon d'an tsawonta yake tunda ko fuskarsa in zata kalla sai ta daga wuya da kai,
kuma wai shine tana ikirarin tazo ta rama marin daya mata,
cikin ranshi kuwa jira yake yaga iya rashin kunyarta zata mareshin neko k'ak'a,
ganin tana ta d'ago wuya da k'afafun ta dan ta isoshi tsawo ta kasa,
sai ya d'an rok'ofo kanshi ya sunkuyar dai-dai tsawonta cikin rumtse ido yace.
"Rama."
fuskar shi ta tsurawa ido ta d'ago hannun zata yarfa mai marin sai kuma tayi maza tayi k'asa da hannun sai hawaye car-car a idanun ta,
shi kuwa jin shirun ne sai ya bud'e idanun shi ganin tana kallon fuskar shi tana kuka yasa ya d'an yi murmushi cikin kula ya jawota jikin shi ya ruggume ta kanshi ya sunkuyar dai-dai kan hab'arta daya maran a hankali ya rink'a fese mata iskan bak'in shi mai sanyi sannan yasa tafin hannun shi yana share mata k'ollah,
ita kuwa cikin kuka tace.
"Ni dai sai na rama amman ba, a fuskar kaba."
murmushi yayi a ranshi yace.
"Gaskiyar bahaushe wata fuskar tafi k'arfin mari."
fahimtar da yayi bazata iya ramawan bane,
sai ya mik'o mata cup d'in tea shima ya d'auki d'ayan ya fara sha yana lumshe ido cikin lallashi yace.
"Kisha tea sai na goyeki a madadin marin."
ajiye cup d'in tayi tace ita bazata shaba kuma shima ya ajiye sai ya goye tan,
murmushi yayi ya ajiye cup d'in yana jin sanyi na ratsashi,
tsakiyar d'akin ya dawo kan carpet ya durk'usa ya mik'e tsawonshi kamar mai konciya sai kuma ya d'an taso ya k'afa hannun shi a k'asa sannan ya mik'e tsawonshi ,
cikin sanyi yace.
"Toh zoki hau."
murmushi mugunta tayi dan tanaga bazai iya d'aukar nauyin taba,
da sauri ta matso ta zauna a tsakiyar bayan shi sannan ta tonk'oshe k'afafun ta ta d'an ware hannun ta sannan ta had'a yatsun ta haka👌🻠tana ta murmushi mugunta ,
dai-dai lokacin woyarshi ta rink'a suwa ita kuwa sai gyad'a kai take tana lumshe ido,
yana kallon ta duk abin da takeyi,
a haka har
zuwa wani d'an lokaci sannan ya manna jikin shi kan carpet d'in ya kwanta yana maida numfashi,
itako murmushi tayi sannan ta mik'e zata tafi,
sai ya rik'o hannun ta ya fizgota jikin shi ya matseta gam cikin maida numfashi yace.
"An gaya miki ni dokine da zan goyeki a banza,
nima saina samu maganin sanyin da kika samin."
Baki ta tura tace.
"Toh ai ba ladan mari bane,
kuma ni bani da
maganin sanyi."
"Kina dashi mana."