Sashe 35
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yau Saturday tun safe Usman bai lek'a ko k'ofar parlour suba,
Nenne kuwa gaba d'aya hankalin ta na kanshi ganin har bayan la'asar bai shigo ba yasa ta mik'e ta nufi part d'in nasu,
a hankali tayi sallama,
shiru bai amsa ba dan yana zaune a k'asa a bak'in gado ya kifa kanshi a jikin gadon yana kuka mai cushe numfashi,
a hankali Nenne ta rink'a jin sautin kukan nashi,
tare da tari mai yanayin ciwon zuciya,
a hankali ta shiga cikin d'akin kai tsaye bakin gadon taje ta zauna cikin sanyi tasa hannun ta tadafa kanshi,
da sauri ya d'ago kanshi yana goge k'ollah dake bin fuskar shi,
cikin k'arfin hali yayi murmushi ,
ido ta zuba mai cikin tuhuma tace,
"Usman a zaton ka bansan meke damun ka bako?"
kai ya jinjina tare da yin murmushi yace,
"Nenne bani da matsalar komai".
ido ta sake tsura mishi sannan tace,
" Ummul ce matsalar ai".
cikin sauri ya rink'a juya kai yana jin kunya na ratsashi ya za'ayi ya k'asa control d'in k'aunar Ummul a ranshi har mutane su gane yana son matar d'an uwanshi,
ita kuwa Nenne kafad'an shi ta dafa a hankali tace,
"Ban tab'a zaton shak'uwar ka da Ummul ya zama so a tsaka nin kuba har aka d'aura auren Ummul da Farouq duk a zaton shak'uwace kawai a tsaka ninku,
Usman na fara Azargin kana son Ummul ne bayan Umar ya tafi da ita gidan shi,
tun lokacin da ka fad'i ka suma na gane akwai abinda kake b'oyewa a ranka,
ban gaskanta hakan ba sai randa kukaje gidan Ummul kuka dawo nanma kai ta aman jini sai kuma randa su Umar d'in suka zo manna ka birkice,
sannan tunda suka tafi baka samu sukuni da kowa ba kuma doctor ya shaida mana akwai abin da kakeso kuma kana b'oyewa,
Usman ni yanzu nasan Ummul kake so".
tunda Nenne ta fara magana yayi shiru yana kallon ta,
saida ta furta "Ummul kake so".
sai ya kife kanshi kan cinyarta ya saki wani irin kuka murya a hargitse ya rik'o hannun ta ya rink'a juya mata kai a birkice yace,
" Asiri na ya tonu naji kunya har gaban Ubangiji na tunda matar aure zuciya ta ke so ina zankai wannan zunubin? naji kunya a idanun duniya na rasa wacce zanso sai matar d'an uwana shak'ik'ina wanda bayi da b'uri a duniya daya wuce farin ciki na".
sai kuma ya kuma kife kai yayi ta kuka mai tarin firgici cikin rawan murya ya durk'usa gaban Nenne a hankali yace,
"Nenne ki rufa min asiri ki tayani b'oye wannan sirrin nawa kodako zai zama ajalina dan Allah karki gayawa ko daga ni sai ke ".
itama Nenne kuka takeyi sosai dan Usman ya zama abin tausayi,
a hankali tace,
" kana ganin a haka zakaci gaba da boye abin a ranka ne?"
Kai ya jinjina a hankali yace,
"Nenne taima kona zakiyi kisa baki Abba da Hamma Umar su barni intafi India inbar k'asar gaba d'aya na tabbatar zan samu sauk'in abin a raina in nayi nesa da Ummul".
kallon shi tayi a hankali tace,
in dai haka zai sama maka sauk'i toh ba matsala".
Haka kuwa akayi Nenne ta ajiye Hamma Umar da Abba tayi ta rokawa Usman d'in a barshi ya tafi ai yace ya samu lafiya kuma daga can zai k'ara ganin doctor,
shi kam Hamma Umar har cikin ransa baya son tafiyar da d'an uwanshi zaiyi amman Abba da Daddy sun yarda dole shima ya yarda,
shi kuwa Usman ya fara shirin tafiya cikin happy da kewar d'an uwanshi da Ammin su abar k'aunar su ji yake kamar ya fasa tafiyar dan gani yake kamar shike nan ya rabu dasu kenan har abadan,
haka dai ya d'aure ya tafi.
Gidan Alhaji Bello kuwa mahaifin Mustapha gaba d'aya rayuwar Mustapha ta juya ta canza Mustapha ya zama abin tausayi dan tabbas har cikin ransa yake son Ummul mahaifin shi kuwa ganin ya rasa Ummul d'in ne yasa yace zai had'a shi da y'ar k'anwar shi,
yau tun safe aketa fama da Mustapha iyayen shi sun sashi a gaba kan batun auren amman sai ya d'ago ya kallesu fuska cike da k'ollah yace,
" Daddy ni ba zanyi aure ba Daddy dan Allah kuyi hak'uri ni bana son auren ,bazan iya auren bafa".
Ido Daddyn ya zuba mishi cikin sanyi yace,
"Mustapha shin kana fushi da hukuncin Ubangiji ne? ya za'ayi kace bazaki yi aure ba bayan kuma kana da damar yin auren ashe dan ka rasa Ummul bazaka so y'ar uwarka Amina ba shin ko zakaci gaba da son matar aure?"
kai ya rink'a juyawa yana zubda k'ollah yace,
"Daddy bana son Amina kona aureta bazata ji dad'in zama da niba Daddy bana son cutar da ita".
Mahaifiyar shi ce ta kalleshi cikin tausayawa tace,
" Mustapha wata rana zaka so Amina na kuma tabbata zatayi ma biyayya tunda dama ita tana sonka kuma indai mun isa da kai toh ka aminci da auren nan".
a hankali ya mik'e cikin rawan murya yace,
"Shike nan Daddy na aminci indai hakan zai saku farin ciki".
murmushi Daddy yayi cikin jin dad'i sannan suka bishi da Addu'a,
shi kuwa yana fita d'akin shi ya nufa a parlour ya konta a k'asa yayi shiru yana tuno irin shirin da yakeyi na auren Ummul kawai sai ya rink'a kuka yana istgifari dan tuno cewa Ummul fa yanzu matar aure ce,
haka akayi ta shirin auren Mustapha da Amina..
Gidan Hamma Umar kuwa tun randa Ummul taje d'akin Hamma Umar d'in ya kusance ta daga Wannan ranan ,
rayuwar Ummul ta fara canzawa wani irin abin al'ajabi da tsoro ya rink'a bibiyar Ummul,
tun daga yamma cin wannan ranar Ummul ta farajin hannun ta da akasawa robar family planning d'in yana mata wani irin nauyi sannan sai taji hannun kamar ba a jikinta yaje ba gaba d'aya sai zuciyar ta ta rink'a tsinke wa wata iriyar kasala ta rink'a rufeta,
a haka a daddafe tayi sallan maggariba da isha,
cikin kasala ta zame ta konta kan sallayar da nufin zatayi bacci ,
Amman sai ga wani sabon al'amari mai ban tsoro kuma,
bayan ta konta tayi Addu'a sannan ta lumshe ido a hankali bacci ya fara fizgarta,
lokaci d'aya bacci mai dad'i ya d'ebeta,
Amman cikin baccin sai taga Hamma Umar yana rik'e da jariri fari tas mai kyau yaron sai kuka yakeyi shi kuwa Hamma Umar sai ya mik'e mata jaririn ita kuwa sai ta ture ta juya ta gudu can gefen su,
shiko Hamma Umar d'in sai yasa yaron a kafad'an shi yana lallashin jaririn yana ta zirga-zirga shiko jaririn sai kuka yakeyi da k'arfi,
ganin haka ta tashi a firgice al'wala taje ta kumayi sannan tazo ta kumayi Addu'a sannan ta sake kwanciyar bayan kamar minti 30 bacci ya sake d'auke ta,
still cikin baccin ta sake ganin Hamma Umar zaune cikin jarirai sai kuka sukayi da k'arfi duk sun cika gidan da kuka,
a hankali ta rink'a ganin jariran sun dawo gareta sunata kuka shima Hamma Umar ya koma gefen su yana kallon jariran yana zubda k'ollah,
haka ta sake farkawa a firgice,
Toh fa haka Ummul take rayuwa ba bacci data rumtse idanun ta sai taga ana binta da jarirai suna kuka har abin ya fara zame mata ko a gyegyed'i takeyi sai tayi tajin kukan jarirai ga hannun ta kuma yamma nayi yake fara ciwo ta kuma k'i ta gayawa kowa Hamma Umar kuwa ko sabgarta ya dena shiga ,
sai ya kwana nafilfilin shi yana mai rok'on Allah ya azurtashi da haihuwa kullum Addu'ar sa Allah yasa Ummul ta samu ciki dan yana son haihuwa tare da ita
sai azumi da yake yawan yi dan ya rege k'arfin sha'awarsa tunda yasan ba kulawar Ummul zai samuba,
itako Ummul zuwa yanzu har tsoro take dere yayi da zaran yamma tayi bata da sauran kwanciyar hankali.
Yau juma'a tun safe Hamma Umar yake d'akin shi yana ta karatun qura'an har zuwa 12 sannan yayi wonka ya shirya sab cikin fararen tufafi sai k'amshin turaren shi na du'a'ul jannah yake yi sannan ya fito hannun shi rik'e da sallaya a parlour ya samu Ummul zaune cikin yanayin bacci dan yau koda safen da zaran ta rufe ido sai taga ana mik'o mata jarirai gaba d'aya baccin sai yasa mata ciwon kai ga hannun ta da takeji kamar ba nataba gashi dai ba kumbura yayi ba amman jin hannun take kamar dutsi,
tana ganin shi ta matso gaban shi cikin yin mik'a ido a lumshe tace,
"Hamma Umar a bani maganin bacci mana".
bai kalleta ba bai kuma yi magana ba har yaje bakin k'afa sannan yace,
" sabida me? zan baki maganin bacci?"
"Bana samun bacci ne shiyasa".
" baki da lafiya ne?"
"A a ni lafiya ta lau".