← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 77

Sashe 44

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye parlour Abba suka nufa inda gaba d'aya gidan suke zaune a parlour sunata hira,
suna shiga su duka uku suka zauna gaban Abba da Daddy cikin Happy Abba ya kallesu tare da amsa gaisuwar su,
sannan ya kalli Hamma Umar yace,
"Farouq ya gidan naka ba wata matsala ko?".
kai ya gyad'a a hankali yace,
"Abba matsalar dai cikin yayiwa Ummul nauyi".
ya Adam ne ya watsawa Ummul d'in harara tare da cewa,
"Toh ai haka kowa ke haifar yaranshi har in ba, ayi daceba yar ta nuna bazata yiwa iyayen nata biyayya ba".
hararan da Hamman ya mishine yasa ya kame bakin shi,
ya Sadik ma sai hararan Ummul d'in yake yana jin tana gaida shi yak'i amsawa,
ya Usman kuwa Hajjajo ya kallah cikin murmushi yace,
"Hajjajo kingafa na girma na zama baba da haka kar ki kuma cemin yaro".
dariya sukayi baki d'aya
sai kuma suka juyo gun Aliyu da yake hararan Ummul yana janye piket d'in abincin gaban shi yana cewa,
"mitssss wallahi ke dai kin bonu da kwad'ayi kina ta kallona salon na kware ni ba baki zanyi ba tunda ai ke yanzu ba yar gidan nan bane".
Hamman ne ya kalleta cikin kula yace,
"Zakici abin cin ne".
Kai ta gyad'a a hankali tace,
"eh yunwa nake ji".
Adam ne ya tsuke fuska tare da cewa,
"Uban me ya hanaki kiyi girkin a gidan ki kici?".
hawaye ta fara k'ok'arin zubdawa ganin haka Hamman ya mik'e tare da cewa,
"Taso mu tafi gidan Ammina zata miki duk abinda kike so bar musu abincin gidan su".
mik'ewa tayi dan tasan inya tafi ya barta zasu iya mareta,
shiko Hamma Umar hannu yasa ya kamo na Usman sannan yace,
"tashi mu tafi".
dariya yayi sannan ya mik'e suka fita,
Nenne ko kallonsu take cikin k'aunar yadda suke k'aunar juna tace,
"ku gaida min Ammin kuce sai gobe Aliyu zai kawo mata aiken nata".
"toh ". Sukace sannan suka fita,
suka nufi gidan Ammin nasu,
suna fita Abba ya kalli Adam dake bin bayan ummul da harara yace,
"Adam me kuma Ummul ta aikata? dan na lura fushi kake da ita".
zama Adam d'in ya gyara sannan ya kwashe labarin yadda sukayi da Ummul da Hamma Umar d'in ya fad'awa Abban,
gaba d'aya parlour shiru sukayi dan yadda Abba da Daddy suka hatsala fad'a sukeyi sosai tamkar zasu bugi babu daga k'arshe fad'an ya dawo kan Nenne cikin tsananin fushi Abba yace,
"khadija na lura kece kike d'aurewa Ummul gindi takeyin abinda taga dama shin dan na had'ata da d'an d'an uwana ai bawai yana nufin tayi ta tozartarmin da shiba,
ashe ban saniba ban isa da Ummul ba toh wallahi zan d'auki mataki a kanta".
ita kam Nenne gaba d'aya takaicin Ummul ya isheta,
tunda gashi laifinta ya shafeta,
dama in yaro yayi abu mara kyau tofa koya uwa zatayi sai anga laifinta,
shiko Abba da Daddy kan Adam d'in suka haura da fad'a,
"ai kaima baka da wani amfani tunda ka kasa d'aukar mataki a kanta kuma tunda na dawo baka gaya min ba sai yau yau d'inma saida na tabbaye ka,
to daga yau ni na baka izini da Umarni in Ummul ta sake yin abu makamancin wannan kayi mata duka sai ta konta jinya tunda bata jin magana".
Hajjajo ce taja tsaki tare da cewa,
"yarinya sai taurin Kai kamar Arnan forko,
a mata dukan shine maganin ta".
ita ko Nenne,
shiru kawai tayi tana jinsu sunata fad'a,
haka dai sukayi ta fad'a daga bisani suka watse.

A gidan Ammi kuwa suna shiga gidan ya Usman ya nufi parlour Ammin yana,
"Ammmmmi! Ammi! Ammina ina kike ne ".
Ammi dake kitchen cikin tsananin mamaki da jin muryar autan nata ta fito,
Inna ma da sauri ta fito daga bedroom nata,
a parlour suka sameshi yana ganin Ammin nashi da sauri ya k'arisa gaban ta cikin tsananin kewar juna ya ruggumeta itama kuwa sai murmushi take tare da hamdala,
Hamma Umar kuwa da yanzu ya shigo tare da Ummul mamaki yake yadda shi Usman ba ruwanshi ba kunya ko nauyi yake ruggume Ammin tasu abinda shiko bazai iyaba,
ita ko Ummul cikin sanyi ta matso kusa da Ammin a hankali tace,
"Ammi ina kwana? ".
Da sauri Ammin ta ture Usman sannan ta kama hannun Ummul suka zauna kan 3 str Inna ko ta zauna kan 1 str tana fuskantar su,
shiki Usman d'aya gefen Ammin ya zauna kamar yadda ya saba,
shiko Hamma Umar a hankali ya matso gaban Ammin ya zauna a k'asa kan carpet sannan ya rusunar da kanshi tare da cire hular kan nashi,
ya sunku yar da kan nashi,
murmushi Ammin tayi sannan tasa hannu ta dafa kan nashi kamar yadda suka saba cikin tsananin farin ciki tace,
"Allah yayi muku Al'abarka Allah ya tsaremun ku da zuk'atanku da imaninku Allah ya jibanci lamuranku".
"Amin Amin".
suka amsa baki d'aya sannan shiko Usman ya juyo ya gaidata cikin happy tace,
"Usman ya jikin naka "?.
da sauri ya kalli Hamman nashi dake shirin yin magana sai ya kuma kalli Ammin yace,
"Ni na samu lafiya plxx adena yawan cemin ya jiki,
indai ba so kuke yaron da Ummul zata haifa shima ya fara cemin ya jikin ba".
dariya sukayi baki d'aya sannan ya kalli Ummul d'in yace,
"A cici akawo miki abincin ko? ".
kai ta sunkuyar itako Ammi tana jin haka ta koma kitchen ta had'o musu abincin ta kawo musu,
Inna ce ta kalli Usman tace,
"Kai aggona tare zamuci fa dan yau amarci zamuyi".
duk dariya sukayi,
shiko Hamma Umar abin cin ya had'a musu a pilet sannan ya kalli Ummul da Usman yace,
"ku sauk'o kuci abincin".
sauk'owa sukayi suka fara ci dan ita Ummul da Ammi tamkar uwa da ya suke,
shiru Ammi tayi ta zuba musu ido ganin Usman da Ummul kecin abincin shiko Umar sai in sunci ya k'ara musu sannan ya had'a musu tea a hankali tace,
"Farouq kai bazaka ci bene? ".
kai ya jinjina sannan ya kalli Ummul d'in da Usman yace,
"Ammi na nafi buk'atar inga su d'in sunci".
murmushi Usman yayi ya kalli Ummul dake ta faman d'uri ko a jikinta,
itako Ammi sai ta had'a wani tea d'in sannan ta mik'owa Umar d'in tace,
"karb'i kasha kai kullum kan kula da Usman kake k'arewa sam bak'a kula da kanka".
murmushi yayi ya karb'a yana sha tare da cewa,
"To Ammina nagode".
itako Ummul tana gama cin abincin tayi mik'a tare da kallon Ammi tace,
"Ammi bacci zanyi".
cikin jin dad'i Ammin tace,
"taso muje ki hau gadona kiyi baccin ki".
haka taje ta konta,
suko sukayi ta hira,
anan suka wuni har yamma sannan suka sallamesu suka koma a gidan ma suka d'anyi hira bayan sallan ishane Hamma Umar d'in ya kwashi Ummul d'inshi suka koma gidan su cikin damaturu.

Lokaci ya juya yanayi ya canza a cikin sati 3 da dawowar Usman yayin da yanzu cikin Ummul yake da wata bakwai da sati 3
tsakanin Hamma Umar kuwa da Usman wani irin shak'uwane da son juna me tsanani yake k'ara ratsasu
Usman baya iya yin kwana 2 baije damaturu ba inko ya kwana 1 bai jeba toh Umar zai d'auko Ummul su zo,
Itako Ummul da Hamma Umar zuwa yanzu abu yaci tura ko gaban Usman Ummul cewa take aje a cire cikin ya isheta ita ta gaji dashi,
a gefen ciwon Usman kuwa Allah ne yasan halin da Usman yake ciki dan gaba d'aya shida kanshi yana jin rayuwarshi ce tazo k'arshe shiyasa yake jin son Umar a ranshi kar yaya yakan zauna yayi ta kuka yana tuna halin da Hamman na shi zai shiga randa labarin mutuwarsa ta riskeshi,
yau ma kamar kullum bayan Adam ya fitane shiko ya tashi ido cike da k'ollah pictures d'in Hamman shi da na Ammin shi sai na Ummul ya tattarosu kan carpet ya zauna ya watsa pictures en a gaban shi kamar zaucecce ya fara magana da surutai,
"Kaito na ni Usman tir da halin zuciyata mara d'aukar k'addara tir da zuciyar da take son matar d'an uwana mafi soyuwa a gareni d'an uwan da yake sona fiye da kanshi amman zuciyata ta gaza bar mishi matarshi tir da halina,
Hamma kana gujemin mutuwa a ganina itace mafita fargaba na d'ayane,
Hamma na ya zakaji randa idanun ka zasu ganema gawata wazai lallasarmin kai wazai dawo madadina a gareka Hamma zan barka da Ammin mu kai kad'ai ko ya Ammin mu zataji randa zata ga ba Usman sai Umar Ummul sonki shine mafi munin fargaba a gareni zuciyata ta kasa barin sonki a matsayin ki na matar d'an uwana wayyo ni Usman naji kunyar rayuwata,
son matar aure me zance da uban gijina Allah kai kajarabci zuciya ta da son Ummul Allah ka yayemin kar d'an uwana Umar ya gane inason matarshi".
a haka yayi ta kuka da surutai har zuwa wani d'an lokaci
sai kuma kawai ya kife kai yayi ta kuka tare da tari mai tsanani cikin layi ya mik'e ya tattara pictures d'in,
ya juyo Kenan idanun shi suka sauk'a kan fuskar......

*by*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL, AMARI*

Page 2⃣7⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*A TRUE LIFE STORY*

```Masoya na makaranta ina mai baku hak'uri dan naga k'orafe-k'orafen ku amman ku sani cewa wallahi wannan littafi nawa RUBUTACCEN AL AMARI NE MIN IND'ILLAH wannan labarin Allah ne ya tsarawa mutanen wannan littafin rayuwarsu a haka ba k'age wlh duk abinda kukaji na Al'ajabi gaskiyane ya faru har kuma wanda zakuji a gaba hatta dai-dai da ruwan tea da Ummul ta watsawa Hamma Umar a ido wallahi gskya ne hatta soyayyar Hamma Umar ga Ummul da ciwon Usman, ku bini
a hankali wallahi tallahi akwai darasi mai girma a labarin nan```
Chapter 44 · 0% Book details