Sashe 43
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haka suka kwana mak'ale da juna,
koda gari ya waye yana dawowa masallaci kai tsaye d'akin Ummul d'in ya wuce ya kwashi garar kafi shayi dad'i,
haka rayuwa tayi ta juyawa tana tafiya gaba d'aya yanzu Hamma umar ya jarabe ya yaraba Ummul d'inshi wasu lokutan har yana jin tsoron kar dai cikin ya zube dan shida kanshi yasan jarabarsa tayi yawa,
cikin ko yana nan daram sai k'ara k'awari da lafiya da wintsil-wintsil da yake yawan yi,
Ummul ko har kwanan gobe bata tabajin son Hamma Umar d'in ba haka kuma bata tab'ayin wani abu dan ta faranta mai raina.
A gida kuwa randa Hamma Umar ya mari Adam suna tafiya,
Adam ya koma parlour Nenne cikin takaici da jin haushin k'anwar tashi ya shafa kumatun shi ya kalli Sadik dake gefen shi rai a b'ace yace,
"Ni Hamma Umar ya mara a kan na daki Ummul dan tayi mishi laifi".
dogon tsaki Sadik yaja cikin ta kainci yace,
"wallahi tallahi da a bare Hamma Umar ya auro Ummul wallah sai ince ta asirce mana d'an Uwanmu Kalli fa yadda ta maida Hamma kamar bawanta inajin bak'incin yarinyar nan wallahi duk randa na kamata sai na b'allata".
ya k'arishe maganar yana nuna yadda zai b'allatan,
Tsaki Adam ya ja cikin ta kaici yace,
"Duk ta meda Hamma Umar shanyeyye soko ya zama tamkar sakarai".
Aliyu ne ya dan yi k'asa da kanshi yace,
"Ni ina jin tausayin Hamma,
Ummul na wahal dashi".
Ajiyan zuciya Nenne ta sauk'e cikin kallon yaran nata a hankali tace,
"Ba Ummul ke wahal da Farouq ba soyayyar Ummul ce ke wahal dashi".
cikin mamaki Adam yace,
"Son Ummul Kuma Nenne Hamma Umar yana son Ummul ne ai ba sonta yake ba had'asu fa akayi ko kin manta ni dai inaga girman al'k'awarin daya d'aukane ke wahal dashi ko?".
Kai Nenne ta kuma juyawa cikin sanyi tace,
"Farouq yana son Ummul Adam baku gane hakan bane kuma sonda Umar keyiwa Ummul na asaline tun randa aka aifi Ummul".
sai kuma tayi ajiyan zuciya taci gaba da cewa,
"Tun randa aka haifi Ummul,
Umar ya bata matsayi mai girma a rayuwar shi,
bayan na haifi Ummul Umar shine mutun na forko daya d'aga Ummul yana d'agata ya ruggumeta cikin tsananin farin ciki sai kuma ya kalleni yace,
"Nenne da d'a namiji kika haifa da anmin takwara Nenne yarin yar nan dana mijine da na samu magaji,
amman yanzu ma bai b'aciba Insha Allah zata haifomin takwarana kuma Yerimana".
inajin abinda Umar ya fad'a sai nayi dariya nace ai itama takace,
haka daga wannan ramar Umar ke d'awainiya da Ummul renonta kab shi yakeyi a kwana a tashi har ta fara girma so shiko a lokacin an kaishi karatu India bayan ya gama ya dawo kuma,
sai ya zama basa shiri da Ummul sabida shi mutunne mai nitsuwa ita ko Ummul tana da kaud'i da tsiwa ga yawan fad'an da takeyi da Aliyu tana cin zalinshi shiko Umar baya son zalumci da sowa kuma ya zama shine matsayin mahaifinku in Abban ku baya nan shiyasa yake bada kulawarshi akan Ummul sosai yayinda ita ko ta d'auki hakan a mizanin k'iyeyya,".
kai suka jinjina su duka ita kuma taci gaba da cewa,
"Kuma duk da haka dole ku d'auki mataki kan halin Ummul dan a samu ta gyaru,
amman fa karkuyi a gaban Umar".
toh a haka fa daga ranar suke cike da takai cin Ummul d'in a rayu kansu,
kwanaki sun ja makonni sun ja watanni sun ja ya Usman kuwa kullum sai yasa ranar dawowa sai ya d'aga a haka har cikin Ummul ya cika wata 7 ,
yayin da a gefen Umar kuwa kullum cikin tashin hankali yake da matsamai da Ummul take akan a cire cikin ya samu dai yanzu ya lallab'a ta a kan sai cikin ya cika wata 7 da kwana 7...
Yau Monday tun sassafe Hamma Umar ya shiryo da Ummul enshi suka nufo gida dan Ya Usman yau zai dawo a cewarsa yau kam bazai d'aga dawowar ba dan jin kewar Umar yakeji tamkar sun shekara 10 basu had'uba,
Abin mamaki suna isa gida a harabar gidan Hamma Umar ya haggo Usman d'in ya nufo gunsu cikin sauri yana murmushi mai cike da farin ciki,
Hamma Umar kuwa da Ummul har rigerigen fitowa sukeyi,
a motar suna fita Ummul ta ruga a guje cikin ihun farin ciki da sowa da rakad'i tana,
"Oyoyo ya Usman na ya dawo Hamma Umar Kalli ya Usman nawa ya dawo".
shi ko Umar zuciyar shice ta rink'a bugawa da k'arfi yana kallon yadda Usman ya rame sai farin daya k'ara shiko,
Usman ganin Ummul da yayi da k'aton ciki a take jikin shi ya Kama rawa cikin tsananin firgici da tsinkewar zuciya gaba d'aya gabban jikin shi suka rink'a rawa zuciyarshi na harbawa da karfi,
dafe k'ahon zuciyarshi yayi a da-idai lokacin da Ummul ta fad'a jikin shi dai-dai lokacin kuma Hamma Umar ya k'araso garesu bud'e hannayen shi yayi ya had'asu gaba d'aya ya ruggume su,
Lokaci d'aya yaji wani irin karaya a zuciyarshi abin mamaki saiga Hamma Umar yana kuka cur-cur ruggume da k'aninshi da matarshi kuka sosai yakeyi yana shinshina wuyan Usman ,
kukan Hamma Umar d'in ne ya k'ara tono dafin zuciyar ya Usman d'in cikin wani irin yana yi yace,
"Hamma kuka Kuma? ".
sai kuma tari ya sark'a fe mishi tarin yakeyi da k'arfi yana numfashi sama-sama,
a gigice Hamman ya tallabo d'an uwan nashi dai-dai lokacin usman yayi wani irin yunk'uri da kakari sai ga....
*by*
*GARKUWAR FULANI*
ðŸ“ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*RUBUTACCEN AL, AMARI*
Page 2⃣6⃣
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*INA KUNE MATAN group d'in TABITAL FULAKU tare da AYSHA ALI GARKUWA FANS da kuma GARKUWAR FULANI Group tare da GARKUWA AYSHA&UMMEE ina Al'afahari daku ina sonku har raina ko a cikin groups na ku din nan da banne a gareni Fatan Allah ya k'addara saduwarmu a jannatul firdausiðŸ¤ðŸ˜ðŸ˜˜*
*S*aiga tari ya k'ara turnu k'eshi tarin ya keyi sosai har ida nunshi na firfitowa woje gaba d'aya jijiyoyin kanshi dana hannun shi suka taso rud'u-rud'u, sai k'ara ruggume Hamma Umar d'in nashi yake yana wani irin murmushin k'arfin hali,
ita ko Ummul gaba d'aya jikinta rawa yake ta rik'o hannun ya Usman d'in tana zaro ido murya a hargize tace,
"Wayyo Allah na Hamma Umar kalli ya Usman".
sai ta kuma fara kuka itama tana,
"ya Usman har yanzu kana wannan tarin da aman jinin ko shin doctors basu duba lafiyar ka bane?".
kai ya rink'a juyawa jikin cushewar numfashi da zufa dake tsatstsafo mishi duk ta inda hutar gashin jikin sa yake,
hannun na rawa ya tallab'o hab'ar Hamma Umar da hawaye ke zuba tamkar an bud'e pompo idanun shi kamar zasu fad'o k'asa yana kuka harda sheshshek'a,
ido ya kuma tsurawa Hamma Umar d'in nashi cikin dauriya Ya rink'a juya mishi kai cikin tarin yace,
"A zatona zuciyar Hamma Umar na tana da k'arfin da zata iya jure mutuwata ma bare dan tarina,
amman kach sai gashi ina rayema kana min kuka,
ashe in namutu gatan da zakayi min kenan Hamma na? ashe bazaka iya cin jarrabawar da Allah zai maka ba,
Hamma Umar ka dai sani dole watara zan mutu ko".
Kai ya rink'a juyawa cikin kuka yana k'ara ruggume shi yana cewa,
"Usman bani da kamarka kullum cikin fargaba nake nima da kaina bansan ya rayuwata zata kasance min ba inba kai,
Usman bazanyi maka gatan kukaba bazan zubdama hawaye ba zan zamema mai gatan yima sutura da addu'a Usman inajin tsoron jinin da kake amayarwa".
cikin sauk'e ajiyan zuciya dan tarin ya dan lafa sai ya kuma yi murmushi ya kalli Ummul ya kuma nuna k'aton cikin ta sai ya Kuma kalli Hamman nashi cikin salonshi na abin dariya ya d'an ture su yaja baya kad'an sannan yayi gyaran murya ya gyara zaman hulanshi ya dan bud'a kafad'a cikin salon girma yace,
"Na zama Baba yanzu na wuce yarinta a dena jimin tsoron mutuwa ko namutu ga magaji na".
sai ya kuma sunkuyowa saitin cikin yace,
"Ni Baba zaka kirani".
cikin jin dad'i Hamma Umar ya kalleshi tare da cewa,
"ai dama kaine baban shi na bar makashi ni dai mahaifinshi ne kawai amman kaine babanshi".
murmushi yayi cikin farin ciki sannan ya kalli Ummul da ta tura baki tana hararan cikin a hankali yace,
"Allah ya d'aiyiba min Baby maman Baby".
cikin zubda k'ollah tayi murmushi tare da kallonshi tace,
"ya Usman ina sonka yayana".
dariya yayi sannan yaja hannun Hamman nashi suka nufi cikin gaida, yana cewa,
"Allah ya d'aiyiba".