← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 77

Sashe 17

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

murmushi Anty Halima tayi tare da kamo hannun Ummul d'in ta d'aura cikin tafin hannushi,
wani irin nanauyan ajiyan zuciya ya sauk'e tare da
rumtse idonshi da k'arfin,
yatsun hannushi ya cusa cikin nata ya rik'o hannun ta sannan ya mik'e tsaye ya fara taku a hankali itama Ummul takun takeyi tamkar hawainiya a haka har suka isa gaban kujerar da zai zaunar da ita suna zuwa ya kamo kafad'unta ya juyota tana fuskantar shi yayinda ta bawa kujerar baya,
cikin sanyi ya zaunar da Ita kan kujerar dake manne data Hamma Umar,
a hankali ya fara tasowa daga sunkuye da yayi a kanta,
Ita kuwa Ummul kanta ta kuma sunkuyarwa tare da sakin wani narkekken sautin kuka can k'asa,
Sai kuma tayi shiru cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Ya Usman d'in nata jin kamar y'an watsa mata ruwa,
abin mamaki da Ummul ta gani ba ruwan bane ya Usman ke watsa mata ,
Hawaye ne ke bin fuskar sa har yana diga cikin tafin hannun ta ,
ido ta zuba mai cikin yanayin tabbaya da tsantsar. mamaki a fuskar ta,
shi kuwa cikin jarumta yasa tafin hannushi ya goge k'ollah dake zuba a idanun shi,
murya na rawa yayi murmushin da yafi kuka k'una a zuciya murya can k'asa yace mata.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi cikin zubda k'olloh murya a disashe tace.
"Ya Usman ina son ka".
ido ya lumshe da sauri cikin raunin murya yace.
" Ummul nima ina sooonki."
Ido Ummul kam ta kuma rumtsewa dan tasan ba haka suka saba cewa juna ba,
Ita tasan in tace mai ya Usman ina sonka shiko sai yace Allah ya d'aiyiba Amman Yau kuma shima sai yace mata "Ummul nima ina sooonki " a madadin yace Allah ya d'aiyiba Sannan ga hawaye dake bin fuskarsa,
tana cikin nazarin ne taji ya fara yi mata lik'in da Sabin kud'i na gudan dubu-dubu'
gaba d'aya wuri aka fara tafi marok'a na .
"Kaji k'anin aggo Usman d'an Maliki mai ruwan nare."
lik'in sosai Ya Usman yayi mata yanayi yana zubda k'olloh cur-cur sai yasa tafin hannushi yana gogewa ganin haka yasa Ummul tayi murmushi cikin d'an d'aga murya kad'an yadda zai iya jinta tace.
"Allah ya d'aiyiba min ya Usman dina."
jin haka sai ya rink'a murmushi tare da kallon fuskar ta,
a haka ya gama yi mata lik'in sannan Ya Adam da ya Sadik tare da Aliyu auta suma suka shigo sukayi mata lik'in ,
daga nan manyan abokan Aggo kuma jarumai suma suka fito sukayi lik'in ban girma,
daga nan y'an uwa da abokan arzik'i sukayi nasu. lik'in,
bayan duk an gama kowa ya koma mazaunin shi wuri yayi haske,
cikin wani irin yanayi Hamma Umar d'in ya mik'e tare da juyowa gaban Ummul d'in sannan kanshi a sunkuye cikin sanyin muryar shi ya kalli marok'an yace.
"Ku shaidawa Jama'a yanzu zanyiwa Ummul lik'in ne a matsayina,
na babban Yayanta d'an uwanta."
aiko a take marok'an nan suka rink'a shela suna fad'in.
"Aggo yace a shaida muku yanzu zaiyi lik'in ga Amarya a matsayin shi na babban yayanta kuma d'an uwanta."
gaba d'aya sai wuri ya ciki da shauk'i ,
abokan Hamma Umar da matan su sai murmushi suke,
shi kuwa Hamma Umar lik'in kawai yake mata da rafa-rafa na dubu-dubu,
haka ya rink'a zubawa Ummul kud'i tamkar ruwan sama,
bayan ya gama ne sai ya kuma komawa kan kujera ya zauna,
sannan k'awayen Amarya suka rink'a tattara kud'ad'en.

Bayan sun gama ne Hamma Umar d'in ya sake tashi tsaye cikin cikar haiba da kamala gaban Ummul d'in ya kuma tsayawa cikin k'asaita yace.
"Yanzu a matsayin aggo zanyi lik'in."
marok'an ko tuni suka cika wurin da kirari suna.
"Ummaru sand'a babuga mai nera Ummaru mai ado da zinari Ummaru Farouq mai K'amshin al'miski
kunji Umaru Farouq babban adali doctor mai tausayi da jink'ai."

Shi kuwa Hamma Umar Dolas ya zaro ya rink'a yiwa Ummul b'arinsu a kanta,
Ya Usman kuma na tsaye a gefen shi rik'e da turaren mai suna *du'a'ul jannarh* mai tsananin k'amshin,
bayan Hamma Umar ya gama lik'in sai ya kuma mik'a hannu ya karb'i turaren dake hannun Ya Usman,
sannan ya d'an sunkuyo kan Ummul d'in ciki kallon fuskar ta ya fara fesa mata turaren yanayi yana k'ara matsota har ya isa gab da Ita sannan ya mik'ewa Usman turaren ,
a hankali ya rokk'fo gaban ta sannan ya sunkuye dai-dai kanta,
mutanen wurin kuwa gaba dayasun maida hankalin su sukayi kan Hamma Umar d'in domin son ganin me zai aika ta,
Hajjajo kuwa da Inna tuni sun fara mamakin abinda Umar d'in yake shirin aika tawa,
sauran mutane kuma gaba d'aya kallon shi suke cikin tarin mamaki dan gano abinda yake shirin aika tawa,
Ammin kuwa lokaci d'aya taji wasu siraran hawaye na bin fuskata tana kallon Abin da Babban d'an nata zaiyi,
Abokan Hamma Umar kuwa ido suka zuba mai cikin mamaki su Hamma Yusuf duk an cika da mamaki sai k'ara rik'e hannun Ayshan sa yake.

Itako Ummul gaba d'aya jikin ta sai kerma yake ido kawai ta zubawa Hamma Umar d'in fuskar ta cike da k'olloh,
Nenne ma ido ta zuba mishi dan gano abinda zaiyi.

Shi kuwa Hamma Umar cikin wani irin yanayi yasa hannushi ya cire hular kanshi sannan ya k'ara sunku yowa kan Ummul d'in tare da manna....

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1⃣2⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*H*ularshi ya cire daga kanshi sannan ya kuma sunkuyowa kanta,
yayin da gaba d'aya mutanen wurin kuwa suka zuba mai idanu,
shi kuwa Hamma Umar kanshi a sunkuye cikin lumshe ido ya manna mata hular tashi a kanta sannan yasa hannu biyu ya dai-dai ta zaman hular a kan Ummul d'in hular tayi ras,
ita ko Ummul ido ta zaro cikin tarin firgici gano cewa Hamma Umar al'adarsu ta biyun zaiyi a take zuciyarta ta rink'a buga wa a saba'in,
Ammin shi kuwa sai murmushi take a ranta tana al'fahari da d'an nata,
Abokan Hamma Umar kuwa kallon shi suke cikin sha'awa da burgewa,
Ya Usman kuwa k'irjin shi ya dafe da k'arfi sannan yasa hannun shi d'aya ya damk'o hannun abokin shi Nuru dake zaune kusa dashi a sashin zuciyar sa kuwa yana al'fahari da hallaci irin na Hamma Umar d'in nashi yana jin dad'in yadda a gaban dubban al'ummah zaiyi al'k'awarin da d'aukar amana,
Shi kuwa Hamma Umar bayan ya gyara zaman hulan nashi a kanta sai ya kuma sa yatsunsa biyu ya zaro siririn gilashin dake manne a fuskarsa cikin lumshe ido ya kuma mannawa Ummul gilashin tare da ajiyeshi ras a fuskarta ,
ita ko Ummul zuwa yanzu hawayen ta tuni suke d'iga kan tafin hannun ta tol-tol,
ganin haka yasa cikin furza sassauk'an numfashi Hamma Umar d'in ya d'an rok'k'ofo ya zauna gabanta suna fuskantar juna zama yayi dirsham a gabanta ya tok'k'oshe k'afafun shi sannan ya had'e guiwowin sa,
A hankali ya sunkuyo kanshi yana kallon k'afafun ta da su kasha zane ,
hannun shi yasa a hankali ya d'ago k'afafun nata sannan ya zare takal manta ya ajiye gefe cikin kula ya tallab'o k'afafun nata da tafin hannun shi cikin tabbacin abinda zaiyi ya d'ago k'afafun nata ya diresu kan guiwowin shi sannan ya had'a yatsun k'afafun ya rik'e yana d'an matsawa kamar mayi mata tausa sai kuma ya sunkuyar da kanshi cikin yanayin bugawar zuciya dan tabbas yasan hakan da yayi d'aukan babban al'k'awarine firgincin dake ranshi shin ko zai iya cika al'k'awarin da ya d'auka?,
mutanen wurin kuwa gaba d'aya aka kaure da tafi maroka na gud'a cikin yin kirari ga aggo Umar Farouq,
dan ba wanda yayi tunanin Hamma Umar zaiyi wannan abun,
Hajjajo kuwa hamadala ta rinkayi cikin jin dad'i Inna kuwa sai k'ollah dake bin fuskata a fili tace.
"Farouq na Allah
Umar Farouq adon gari Farouq mai zuciyar taimako Allah ya baka ikon cika wannan al'k'awarin da ka daukarwa kanka."

Anty Halima kuwa da Anty Shuwa
farin cikin su baya fad'uwa ita kuwa Nenne kuka takeyi sosai a ranta tana ganin al'barkacin sune ita da Abba Ummul ta samu wannan karramawar a gun Hamma Umar d'in,
Matar yayan Ammin Anty Nafeesat ce ta kalli Hajjajo dake gefen ta cikin mamaki tace.
" Hajjajo me Wannan abinda Umar yayi yake nufi?."
Murmushi Hajjajo tayi cikin al'fahari da jikan nata, ta kalli Anty Nafeesat tace.
"Anty Nafeesat Wannan abin da Farouq yayi shi muke kira da nad'in uwar gida sannan mutu ka raba ,
Anty Nafeesat wannan abin da yayi d'aukar al'k'awarine mai k'arfin gaske na rik'e mace da amana da gaskiya."
Numfa sawa Hajjajo tayi tare da ciga da cewa.
"Anty Nafeesat idan namiji yayi wannan abin toh ya d'aukarwa kansa indan zai kashewa kansa dubu 50 toh zai kashewa matarsa dubu 100 ninkin ba nashi kenan kuma ba abinda zaici ba tare d'aya ciyar da matarsa ba kodako tsagin dabino ne sannan ya bata matsayin sarauniya shin ki kalli yadda yake zaune a gabanta mana kuma ya d'ora k'afafun ta a kashi tamkar itace sarauniyar shi."
Kai Anty Nafeesat ta jinjina cikin jin dad'in abin tace.
"Allah ya bashi ikon cika alkhairi."
"Amin Amin."
Hajjajo da Inna suka amsa.
Chapter 17 · 0% Book details