← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 77

Sashe 39

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

A kwana a tashi ba wuya yanzu sun kusan wata uku cur tareda Hamma Umar, a kullum idan taki ta amince da bukatar sa sai yayi threatening nata yace zai fad'a wa su Ya Adam, ta k'ara haske sosai sai dai ta d'anyi rama, ga wani son cin abincin da take yanzu tana cin abinci yanzu anjima kad'an zata fara jin yunwa, koh cikin dare idan taji yunwa zata tashe Hamma Umar ya had'a mata tea taci da snacks ta koma bacci, da sassafe tana sallah'n Subh zata ci abinci sai kuma ta koma bacci cikin kasala yau kam kamar abin yafi na kullum dan yau tunda ta tashi bacci take ta bin bayan Hamma Umar d'in tana rirrik'eshi dan jiri takeji dan tsabar yunwar dake kwakwularta,
kallon ta yayi a hankali yace,
"tsaya a nan Ummul bari in shiga kitchen in kawo miki abinda zakici".
yana fad'in haka ya janye hannun shi ya shige kitchen d'in,
ita kuwa a take duhu ya rufe mata idanun da wani irin jiri ya kwasheta lokaci d'aya k'afafun ta suka rink'a rawa sai ko tayi wani irin...

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 2⃣3⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Kuyi hakuri sisters da jinkirin da muke samu na Rashin yin typing hakan ya farune bisa wasu larurai da sukasha kaina nasan ku kanku readers kun san ba haka na sabayi ba so nasan zakuyi min uzuri ngd da addu'ainku gareni Allah bar zumunci da k'auna*

*I*tako atake duhu ya rufe mata idanu da wani irin jiri ya kwashe ta lokaci d'aya kafafuwan ta suka ringa rawa sai kuwa ta fad'i kasa a sume. Hamma Umar ba k'aramin birkice wa ba yayi daya fito a kitchen ya ganta cikin irin wannan halin, a rikice ya cincib'ota ya kaita d'aki ya kwantar da ita akan gado. Ruwa ya d'auko da sauri a fridge ya yayyafa mata nan take tayi wani irin ajiyan zuciya tareda bud'e idanuwan ta, cikin tashin hankali Hamma Umar yake tambayar ta lafiya tareda shafo fuskan ta, wani irin kuka ta fashe dashi tace "Yunwa nake ji ga kuma ciwon kai". Take ya d'auko mata Indomie'n da ya dafa ya mik'a mata, cikin five minutes sai gashi ta cinye shi tas ta wani tura bakin ta tace "Hamma Umar nifa ban k'oshi ba", bud'e baki yayi yana kallon ta da yasan Ummul bata iya cinye indomie k'anana biyu gashi yau ta cinye shi tas kuma tana kukan bai ishe taba, yace
"Toh bari naje na k'ara dafa miki wani", turo bakin ta tayi tace
"Ni yanzu
wainan kwai nake so na.." bata k'arasa taji wani irin mai na zuwa mata take ta tashi tana son fita a d'akin taje toilet da gudu nan take Hamma Umar ya rik'e sai kawai ta fara aman a jikin sa, yi take har sanda ta amar da Indomie'n gaba d'aya a jikin sa, hankalin sa tashe sai sannu yake jero mata, a hankali ya kaita band'aki ya mik'a mata towel ta cire rigan jikinta ta wanke fuskan ta da hannun ta, bayan ya kwantar da ita akan gado shima ya fad'a toilet yayi wanka. Bayan ya fito ya saka jallabiyar sa sai baza k'amshi yake amma kallo d'aya zaka masa kasan hankalin sa a tashe, matsowa yayi kusa da Ummul dake kwance ta lumshe idanuwan ta, shafo fuskan ta yayi yace
"Ummul bakya jin dad'i ashe, meh da meh yake miki ciwo?", hawaye tafara tace
"Hamma ciwon kai kuma ni yanzu yunwa sosai nakeji ni gaskia ka kaini gida", shafa fuskan ta yayi yace
"Yi hak'uri zan kaiki gida kinji yanzu meh kike so kici", shuru tayi na d'an wani lokaci tace "Bread da shayi", Allah ya so shi akwai biredi a gidan ya had'a mata da shayi taci. D'akin sa yaje ya d'au kayan aikin sa ya k'ara dawowa d'aki, cire allura yayi ya lallashe ta kan ta yarda ya d'au jinin ta, canza kayan sa yayi ya saka ash shadda wanda ya amshe sa ya masa kyau sosai yace "Ummul yanzu meh kike so kice dan ni zanje na bada jinin ki a lab suyi test"
Take tace masa "D'anwake da alale", fita yayi ya siyo kan ya dawo har ma tayi bacci, ajiye mata yayi a d'aki a flask na tea ya fita.
Direct lab ya wuce ya bada jinin ta ma wani abokin sa yace a mata test na Widal, Mp da PT emergency neh yanzu yake so.
Cikin awa d'aya kaf aka gama masa tests d'in yana zaune a office na abokin sa aka kawo masa gaba d'aya uku tests result d'in. Karb'a yayi ya bud'e Widal result d'in yaga bata dashi gaba d'aya 40% da 80% wanda yake nunin batada typhoid, sannan ya bud'e na Mp yaga +1 tana da malaria'n amma ba sosai ba, a hankali ya bud'e result na pregnancy tests d'in idon sa yakai ga Positive, bai yadda da abunda yake gani ba har sanda ya k'ara bud'e idon sa da kyau harda goge idon sa, matar data kawo masa results d'in tayi dariya tace
"Tabbas idon ka bai maka k'arya ba congratulations matar ka tana da cikin wata uku", nan take ya d'aga eyes nasa yana kallon ta nan take ya tashi a kujeran da yake zaune yayi sujada ya d'ago ya d'aga hannayen sa sama hawaye ya cika fal a idon sa yace "Allah nagode maka! Alhamdulillah Yaa Allah!"
Take ya fita a d'akin yaje parking lot inda yayi parking motar sa, shiga yayi cikin motar yana murmushi yaja motar sai wani babban restaurant, abinci fried rice ya siya da Ice cream ya wuce gida.
Da sallama ya shiga d'akin ta a lokacin Ummul tana kan sallaya ta idar da sallah, rungume ta yayi sosai ta baya yana mai shakan k'amshi ta, tura bakin ta tayi tace "Hamma Umar please ka barni k'amshi turaren ka na tada mun da zuciya", murmushi yayi ya raba jikin sa da nata yazo gaban ta yana kallon ta with so much tenderness in his eyes yana murmushi yace
"Guess what?", tura bakin ta tayi tace "Hamma Umar I ain't good at guessing kawai ka fad'a mini menene?", k'ara rungume ta yayi sosai cikin rad'a a kunnen ta yace "Ummul kina da cikin wata uku"
Zuciyan tane taji ya wani irin tsinkewa cikin k'arfi ta raba jikin ta da nasa hawaye fal kwance a kan kuncin ta tace
"Na shiga uku nah ni Ummul Khairi", tareda aza hannu biyu a kaa, take ta fashe da wani irin kuka tace
"Wallahi bana so bazan yadda ba sai dai a cire cikin nan, wallahi bazan bar cikin nan a jiki na ba", kallon ta yake yana ga yadda ta zauna ta mimmik'e k'afafu tana dukan cikin da k'arfi,
ransa a b'ace yace
"Hak'uri zakiyi Khairi dan ni wallahi inason cikin nan",
tasowa tayi tana kuka taci gaba da dukan cikin da k'arfin da Allah ya bata tana,
"Wallahi Allah sai dai ya zube ni bazan bar cikin nan ba sai dai ya zub'e" Tana mai buga cikin da hannun ta, nan take Hamma Umar ya rik'e hannun ta cikin lallashi yace
"Ayyah Khairi yanzu baza kiyi hak'uri ki rungume k'addara ba, mata nawa suke neman haihuwa a duniyan nan Allah bai basu ba dan Allah kiyi hak'uri ki haifa min yaron nan ina matuk'ar son cikin nan fiyeda komai na rayuwa ta".
Kuka take tana mai zubda kayan gaban dressing mirror'n ta tana wasar dasu a k'asa tana
"Wallahi Allah bazan bar cikin nan ba, wayyo Allah na nashiga uku kowa baya so nah zasu d'aura min hawan jini, wayyo Allah nashiga uku", tana kuka sosai
Kama ta yayi ya zaunar da ita akan gado yana mai rok'on ta Allah da annabi tabar masa cikin
"Khairi dan Allah ki rufa mini asiri dan darajan manzon Allah S.W.A ki bar min cikin nan, a yanzu inason cikin nan fiyeda komai a rayuwa ta dan Allah Khairi". Cikin kuka tace
"Bazan iyaba Hamma Umar kayi hak'uri nidai kam gaskia a cire cikin nan, idan kuma kaki koh ta yaya zan cire cikin nan"
Haka zai ta lallashin ta har dare, tun safe data ci abinci bata k'ara ci ba, sosai take jin yunwa har jikin ta rawa yake yana karkarwa, Hamma Umar rik'e hannun ta yayi hawaye fal a cikin idon sa yace
"Dan Allah Khairi kici abinci kiga jikin mi har rawa yake yi dan Allah", ganin yadda ya marairaice ga hawaye ciki a idon sa yasa ta d'an ji tausayin sa tace " Toh ka kawo min". Take ya taso jikin sa har b'ari yake yayi warming fried rice d'in ya kawo mata, sosai taci abincin tana gama ci ta fad'a toilet tayi wanka bayan ta fito tayi sallah, kwanciyar ta tayi a k'asa ba yadda baiyi da ita ta hau kan gado ba amma taki tace ita sam a k'asa zata kwana. Tsaban irin kukan da tayi koh minti biyar batayi da kwanciya ba bacci ya sace ta. Bayan tayi nesa a bacci ya d'auke ta cak sai kan gado tareda rufe mata jiki da bargo.
Alwala yayi yafara jera nafiloli bayan ya idar ya d'au Al Qur'anin sa yana reciting. Shi bai kwanta bacci ba dai kusan k'arfe uku da rabi.
Washegari da safe Ummul da wani irin yunwa ta tashi, Hamma Umar dake kwance akan cushion ganin ta tashi tana juye-juye ya taso ya same ta yace
"Khairi lafiya kuwa", kuka ta fashe dashi tace
"Ni Allah nagaji da cikin nan sai wani yunwa yake sa nakeji kamar wata mayya ni gaskia Allah bazan yarda ba sai an cire cikin", rik'e hannayen ta gam yayi yace
"Eyyah Khairi hak'uri zakiyi kinji, ciki ai rahama neh daga Allah"
Sabon kuka ta fashe dashi tace "Toh ni haka zan ta fama a yunwa kullum, ni kuma bason cikin nake ba gaskia dole ka cire shi". Sosai yake kallon ta idan tayi maganar zub da cikin ji yake kamar an tsoka masa kibiya a zuciya, shafo fuskan ta yayi yace " Yanzu bara na kawo miki shayi kici kinji?" D'aga kai tayi ba tareda ta amsa masa ba, tashiwa yayi ya had'a mata tea ya soya mata kwai ya kawo mata tareda bread. Sosai ta ci tana ci tana hawaye shi kuwa na kallon ikon Allah, bayan ta gama ci ya kwashe su flask d'in ya kai kitchen ya d'aura alwala itama haka sukayi sallah'n asuba. Suna idar wa ya fara karanta Al Qur'ani ita kuma tabi lafiyan gado ta kwanta dan wani irin bala'in bacci neh ke addaban ta, shi kuwa Hamma Umar sanda tana ta fito kan ya rufe ya kwanta a k'asa kan carpet shima cikin minti biyar bacci ya d'auke sa dan jiya bai samu yin bacci da wuri ba...
Chapter 39 · 0% Book details