Sashe 25
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
shi Usman har ga Allah a zaton sa ko laifin tayiwa Umar d'in ya d'an razanata shiyasa take kuka,
Aliyu kuwa tunda yaga yadda take kukan kawai sai ya nufi d'akin da take ta nunawan,
ya shiga ya haggo Hamma Umar d'in yadda yakeyi da gudu ya juyo parlour cikin tsoro yace.
"Ya Usman Hamma Umar baida lafiya fa zo kaga yadda yake."
dai-dai lokacin kuma su Inna da Anty Halima da Hajjajo suka shigo jin abin da Aliyu ke fad'a yasa suka nufi cikin d'akin,
suna shiga Usman ya tallabo d'an uwanshi a jikin shi cikin rawan murya da bugawan zuciya yace.
"Hamma na! Hamma Umar ! d'an uwana ! me yake faruwa da kai Hamma Umar kayi min magana Hamma Umar meke faruwa?."
Anty Halima ce cikin rawan jiki ta kira doctor Abbas abokin Hamma Umar d'in,
sannan ta juya ta kalli Ummul dake ta zare ido jiki na rawa alamun rashin gaskiya cikin tuhuma Anty Halima ta buga mata tsawa tare da cewa.
"Ki baryi mana kuka ki gaya mana meke damun shi me ya sameshi?."
jikin Usman ta kuma matsowa ta kalli Hajjajo da inna da suke ta kuka,
Aliyu kuwa gaba d'aya jikin shi rawa yake ganin yadda jikin Hamma Umar d'in ke rawa,
tsawa Halima ta kuma buga mata cikin watsa mata harara,
k'ara rik'e hannun Usman tayi,
shi ma Usman da yake rugume da d'an uwanshi cikin rawan murya yace.
"Ummul me ya samu Hamma Umar?
meke matsa ciwon?."
k'ara rik'e hannun Usman d'in tayi cikin rawan murya tace.
"Ya Usman idonshi ne yake mai ciwo."
cikin mamaki da k'arin tuhuma Anty Halima tace.
"Me ya samu idanun nashi? yaushe ya fara mishi ciwo? me a cikin idanun ? nasan dai Hamma Umar baida ciwon ido,
Amman ji yadda yakeyi kamar Wanda maciciji ya tsirta mishi dafi a cikin idon,
me ya samu idon ina tabbayarki kinyi shiru."
baki na rawa tace.
"Turarene a cikin idon."
gaba d'aya kusan a tare suka zare ido woje cikin tsoro sukace "turaren kuma?."
"Ehh."
ta basu amsa tana rawan murya.
jin haka Usman ya rugumoshi cikin sauri yace .
"Aliyu jeka bud'e min mota mu tafi asbitin su."
Aliyu har ya mik'e Hajjajo ta kalesu cikin sauri tace.
"Usman ajiye shi maza d'auki makullin motarka yanzu kaje laying FULANI ka seyo mana madarar shanu wanda ba'a tafasa ba daga nan ka biya Islamic kemis ka seyo zam-zam."
cikin juya kai Usman yace.
"Hajjajo wad'an nan abubuwan me zasuyi mu tafi asibiti kar turaren nan ya kashe mai ido."
Inna ce ta kalleshi cikin k'arfin guiwa tace.
"Ajiye shi ka gudu yanzu ka seyosu."
toh yace tare da kontar da Hamma Umar d'in sannan suka fita da sauri shida Aliyu,
kai tsaye layin filoli sukaje sukayi sa'a kuwa suka samu d'anyen madarar shanun daga nan suka seyo zam-zam sannan suka nufi gidan,
a gidan kuwa doctor Abbas yazo tun bayan fitan su Usman amman Hajjajo ta hana a sa mishi komai,
dole Dr ya hakura yana jiran dawowan su Usman ,
su Inna da Hajjajo kam gaba d'aya basuyi tunanin ya akayi turaren ya shiga idanun shi ba,
Anty Halima kuwa tun tuni ta zargi k'anwarta bare da taga kolban turaren a tsakiyar d'akin.
Su Usman na dawowa Hajja tace,
a had'a zam-zam d'in da madarar shanu a bashi yasha ,
haka suka had'a suka bashi yasha,
a hankali ya fara jin zogin da zuciyarshi keyi yana raguwa,
sannan ta kamo hannun shi cikin sanyi tace.
"Farouq."
cikin rawan murya yace.
"Na'am."
"Alhamdulillah."
Inna tace sannan cikin jin k'arfin guiwa tace.
"Halima je kitchen nasu ki kawo roba mai d'an girma."
"Toh" tace tare da ficewa da sauri ,
tana kawowa Hajjajo ta ajiye mai robar a gaban shi sannan ta matso da koryar madarar shanun,
cikin kula tace.
"Ga madarar shanu k'asa hannun ka a ciki ka rink'a d'iba kana wonke idanun ka bud'e idon."
"Toh."
yace sannan ya sunkuya kan robar ya ciki tafin hannushi da madarar sannan ya sunkuyo da kanshi idanun shi ya manna cikin ruwan madarar shanun sannan ya bud'e kwayar idanun a cikin ruwan madarar,
wani irin zafi yaji ya ziyarci ruhinshi da zuciyarshi,
gaba d'aya saida ya rink'a karkarwa hannushi d'aya yasa ya kamo hannun Ummul dake durk'ushe a gefen shi wanda shi baisan waya rik'e ba,
sannu su Hajjajo suka rink'a jera mishi ya Usman kuma yana zuba mishi madarar shanun a haka duk wanda yasa idanun a ciki sai ruwan madarar yayi bak'i a hankali har ya fara yin ja har ya zamo inyasa idanun a cikin ruwan madarar baya canza launi haka kuwa a take idanun nashi sukayi fari tas,
har kaman sunfi da d'in fari,
sannan aka mik'a mishi goran zam-zam ya k'ara woke idanun sai gashi sun fito ras,
Dr Abbas ne ya kalli doctor Umar Farouq cikin kula yace.
"Kana ganina kuwa?."
Murmushi Hamma Umar yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa ganina normal har kamar yafi na da."
ajiyan zuciya dr Abbas yayi tare da cewa.
"Tabbas muna da manyan likitoci a kusa ga magani mai sauk'i gaskiya nayi mamaki tsoffi sun zama likiticin babban doctor Umar."
dariya sukayi baki d'aya sannan Hajjajo ta kallesu cikin yin k'arin bayani tace.
"Ko maciciji in ya tsirtawa mutun yawunshi a idanun haka akeyi kuma da izinin Allah mutun zaiyi ras haka kuwa ko turaren ko wani abu mai Carmichael zakaga gubar zatabi jikin nonon."
Dariya Usman yayi cikin jin dad'i yace.
"Aiko munga zahiri."
da haka Dr Abbas ya tafi,
sukuwa parlour suka dawo suka zauna suna ta jira,
Anty Halima kuwa gaba d'aya hankalin ta na kan UMMUL da Hamma Umar ta lura sarai da yadda Ummul ke yawan satan kallon Hamma Umar d'in shi kuwa kamar baima san da ita a wurin ba,
hakan yasa ta k'ara zargin Ummul d'in.
Anty Halima ce ta shiga kitchen ta fara yi musu girgi,
Sai daga baya ta kira Ummul dake zaune kan dinning table ita da Aliyu suna lallatsa laptop d'in ya Usman,
ta shiga kitchen d'in ta kalleta a fakaice tace.
"Sarauniya kece da bak'in nice da shiga kitchen ko kunya babu kin zauna kina danne-danne,
ga maggi ki b'are min,
sannan ki wonke fruits dinnan ki kaiwa su Hamma Umar d'in da su Hajjajo."
"Toh.'
tace cikin sanyi sannan ta fara b'are margin dan ta lura Anty Halima tana tuhumarta gashi sai harara take watsa mata,
kuma ta sani in Anty Halima ta gane itace ta fesawa Hamma Umar turaren a idanun shi tohfa ta shiga tara tasan ya Adam zaiji in kuma yaji Abban su zaiji inko sukaji shikenan sai buzunta.
tana gama b'are margin ta mik'a mata sannan ta wonke fruits d'in ta shiryasu a pilet guda biyu sannan ta nufi parlour dasu,
tana fita Anty Halima ta jawo robar da ta sa mata magin a ciki da niyar zata sa a girkin nata,
sai taji robar tana k'amshin turare,
k'ara shinshinar robar tayi aiko k'amshin kam rasa taji shi,
kai ta jinjina tare da cewa.
" ba shakka zargina ya tabbata Ummul ce ta fesawa Hamma Umar turaren a idanun shi."
kai ta kuma juyawa tare da cewa.
"Ummul banso had'a ki da ya Adam ba amman kin jawa kanki dole in gaya mishi."