Sashe 9
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai Saudatu ma akwai raki, abun nan da an saba yanzu yabi jiki, aida saidai kawai kiyi abin ki ke kaɗai in yaso da anzo yanke cibi sai ki kira ni in ya gagare ki" abin da kamal ya fara jiyowa kenan yayin da yake wuce gadajen mata masu sabbin jarirai don zuwa wurin tashi matar da abinda ta haifa.
Saudat kuwa murmushi kawai take don ita tasan azabar da ta sha, tunda dai an sauƙa lafiya falillahil hamdu, ita karan kanta Danejon saida ta yabi ƙoƙarin ta a daren jiya amma gashi ba'a je ko ina ba ta sauya magana.
Sallama yayi musu ya ɗaura da "Sannu Saudatu, yaya daɗin jikin?" Da alhamdulillah ta amsa. Yace "Allah ya ƙara lafiya, sannu da ƙoƙari" kafin ya amshi babyn da Yaseer ya rungume tsaff a ƙirjin shi.
Yana da haske irin na jariran nan amma fatar kunnen shi nada ɗan duhu, ya murmusa tunawa da yanda mahaifiyar shi ke ƙulafucin ƴa mace gashi haihuwa uku har yanzu Allah bai ga daman bata ba.
Dabinon da ya siya yanzu a bakin asibiti ya ciro daga aljihu ya gutsura ya tauna sannan ya tura shi a bakin babyn dake barcin shi hankali a kwance. Ya ɗau lokaci yana mishi addu'a kafin ya ɗago kai yace, "nayi magana dasu goggo sunce suna hanya zuwa azahar in sha Allah sun sauƙa, sai mu hanzarta mu koma don tarbar su."
Basu ƙara ɓata lokaci ba suka tattara komatsan su kasancewar an tabbatar da cewa daga uwar har abinda ta haifa suna cikin ƙoshin lafiya don haka basu jira hutun awa shidan bayan haihuwa ba ya saka matan a keke napep sannan mazan kuma suka shiga motar gawan su suka koma gida.
.....
Idan ka shigo hall ɗin kafin idanun ka yakai kan allon sunar dake kan stage zaka ɗauka wani gagarumin event ɗin biki ake a cikin ta.
Babu kowa a wurin bayan event planners wanda ke sanye da uniform ɗinsu na aiki, amma an gama shirya wurin an tsara shi tun daga kan decorations, DJ, abinci da abin sha, dessert station, sannan ko wani table akwai numbobi a saman shi haɗe da jakar suna mai hoton baby don ba za'a kira shi da laidan suna ba, bayan snacks da drinks da aka saka a ciki suna ɗauke da jotter hard cover, biro da kuma turmin zani ko sallaya irin masu kauri da laushin nan, Wanda ke ɗauke da laidoji sune tables ɗin baya-baya amma shima sallaya ko turmin zani ya bambanta su sai kuma nasu laida ne ba jaka ba amma kuma komai yaji.
Numbobin dake kan table ɗin shi zai taimakawa kowa gane inda aka amince masa ya zauna wanda yake matsayi by matsayi, don haka duk wacce aka bata Katin gayyata zata shigo dashi sai ta nunawa masu aikin wurin su kuma zasu taimaka mata wurin samun mazaunin ta cikin tsari.
Zuwa ƙarfe huɗu da rabi na yamma hall ya kusa cika Dj da abin motsa baki suna taya baƙi hira, uwar gayya kawai ake jiran isowarta.
Saida aka saka musu kiɗan da ya dace dasu sannan aka buɗe musu ƙofar suka fara takowa cikin hall ɗin sanye da ashoben su lace mai tsadar gaske na iyayen jaririya, sun sha kyau harda makeup kowa ta zuba gold a wuya, hannu da kunne iya yanda nauyin ta zai iya ɗauka sai faman hura hanci suke, amma Duk wankan su basu Isa su dishashe Hajiya Fauziyya ba wannan alƙawari ne alhaji Tahir yayi musu, kayan da yake jikin ta kawai yayi kuɗin nasu na mutum uku gashi tasha makeup da ya karɓi fuskar ta haɗe da fara'ar da ya ƙara mata kyau da kwarjini, Baby Hafsatu kuwa na cikin wani hand basket da Hajiya lubabatu ke riƙe dashi ba zasu ma iya riƙeta a hannu ba saboda abu irin na bidi'a.
Har kan stage suka yi musu rakiya aka cire Reina daga ƙaramin hand basket ɗin aka saka ta a babba da aka kafa shi a wurin yasha ado da su flowers ya ƙawatu sosai ga wasu manyan teddys da idan ɗaya ya faɗi a kanta bisa kuskure hala sai dai a ɗauki gawar ta.
Aka gyara mata kwanciya kowa sai ƙoƙarin cusa kai yake a cikin su kafin aka zaunar da Hajiya Fauziyya a haɗaɗɗen kujeran dake gefen basket ɗin bayan su kuma ƙaton allo ne da aka rubuta 'Welcome to the world Hafsatu Tahir Kamal (REINA)' shima allon ya ƙawatu abin sai wanda ya gani.
Basu ɓata lokaci ba Mc ya gaida baƙi ya bawa Hajiya Fauziyya mic tayi musu godiya da halarta kafin aka fara gabatar da agenda na gaba wanda shine gabatar da kayan sunan da aka kawo wa sarauniya Reina da mahaifiyar ta.
Na mahaifinta aka fara shigowa dasu a jere masu kawo akwatin ma t-shirt ɗin jikin su da hoton Reina mai nanannen hanci a jiki.
Kowa ya zuba idanu don ganin yawan su, amma abin yaso basu tsoro ganin sai shigo da akwatuna kawai ake sunƙi ƙarewa. Duk wanda yake na Reina ne a gaban gadon ta suke jerawa na hajiya Fauziyya ma a nata gaban ake jere mata mutane tuni an fara shooting da wayoyi bayan wanda photographer yake yi domin a samu na yaɗawa a yanar Gizo.
Saida aka jere akwatuna set uku-uku guda sha biyar kenan ma kowa a cikin su kafin aka ƙara ma Reina da baskets na baby care, bargon yara, da sauran abinda ba zasu shiga cikin akwati ba.
Baki ɗaya sai jikin su Hajiya hauwa yayi sanyi dukda dai sunyi tsammanin hakan ga Mc kuwa sai washi yake ma uwa da uban Reina dama ita jaririyar dake cikin tsumma, nan aka mishi albishir uban yarinya yayi mishi kyautar Naira miliyan biyu, saida ya taka rawar murna.
Ba'a buƙatar ɓata lokaci wurin bubbuɗe wannan kayayyaki don haka aka kira wanda suka shigo dashi don su fita dashi a saka a mota a maida shi zuwa gidan mai jego ba yare da ɓata lokaci ba gudun kada a samu matsala, Su Inna larai suna can suna gadin gidan.
Nanfa aka fara gabatar da gudumawar ƴan uwa, da manyan baƙin da aka gayyata. Ƴan uwan Alhaji Tahir mata kowa tayi nata kayan sai da ta saka mijin ta yayi nashi shima don haka akwati set bibbiyu suka dinga jerewa a wurin, huɗu na hajiya Fauziyya huɗu na Reina. Baƙi ma sun gwada tasu bajintar matuƙa don babbar baƙuwar mu matar gwamna sabuwar dalleliyar mota ta bawa baby.
......
*Toh Reina da an tashi daga suna sai ki tuƙa mu a motar ki zuwa gida😹💔*
*Lallai sunan wannan littafi na shan pronunciation 😂😂😂 daga masu Reena, Raina har su Rayina😂 Ina godiya da ƙoƙarin bin labarin dai🥰*
*Ku cire 'I' ɗin idan kuka zo furtawa saboda silent ne, sai ku karanta shi a matsayin RENA. ma'anar REINA kuma a yaren Spanish shine Sarauniya. Ana yawan amfani dashi a matsayin nickname ko endearment haka tsakanin mata da miji ko saurayi da budurwa*
*REINA 💍*
07... Kan uban chan! Lallai uwar makirai ta tashi kaina, wato sunan yarinya Hafsatu?" cewar Hajiya Farida tana bushewa da dariyar ƙeta yayin da ta juya kan motar suka ɗauki hanyar fadaman mada zuwa gidan Hajiya Hauwa tunda shi yafi kusa da Hall ɗin da aka yi event.
Jinjina kai Hajiya lubabatu tayi tare da yin ƙwafa kana tace "Aini tunda naga ana tambayar Tahir sunan da ya raɗa mata yana wani noƙe-noƙe nasan da wata a ƙasa."
"Ba dole yayi noƙe-noƙe ba yana jin tsoron ya saɓa ma uwar shi Fauziyya ta tsine mai" Hajiya Hauwa dake seat ɗin bayan Hajiya lubabatu a ɓangaren mai zaman banza ta taɓe baki.
Kyalƙyala dariya hajiya Farida taci gaba da yi ta kuwa yi nasara wajen ƙara ƙular da su "Aini nace miki an goge min hadda a lamarin nan, kamata yayi ma muje muna ɗaukan darasi don mu ba zaman aure muke yi ba tunda sai yanda mazajen mu suka yi damu, ita uwar sarauniya kuwa kunga ita ke waina shi kamar tayar keke"
Muskutawa a seat ɗinta Hajiya jummai tayi tace "Ni abun da ya bani takaici wani sunan Nasara da suka ɗoɗara mata Wai Raina ne ko menene? Abun ki dai da matsiyaci bai iya samun wuri ba"
"Reina aka cewa ku kuma ƙauyawa, ƴan gayu suna abu kuna ɓata musu" saboda dariya har hawayen da ya kwanta a idanun ta ya fara saka ta ganin hanya duru-duru dama ga duhun maghriba, don haka ta zari tissue daga cikin kwali ta goge hawayen ba tare da ta bar ƙyaƙyatawa ba.
"Wallahi Farida zan mari bakin ki idan baki ƙyale mu munji da abu ɗaya ba." Hajiya lubabatu wacce ta gama ƙufula ta harare ta "Ah-ah, asiri hauka ne? Don kawai mun zuba mata idanu sai ta maida mana ƙani boyi-boyin ta? Ki kalli fa yanda Tahir yake rawar ƙafa a kan haihuwar nan fisabilillahi, Haihuwar ƴa mace wanda ba zata amfane shi da komai ba saidai ya gama gina ta ya bawa wani ya aura."
"Shi yasa muke so abun ya dawo gida ai, ta ginu ta auri ɗan dangi ko ba komai munci ƙarfin dangin matsiyata" Hajiya Hauwa ta ƙarashe tare da murguɗa baki kaman Fauziyyar ce a gaban ta, Wanda idan ita ɗin ce a tare da ita yanda take nan-nan da ita zaka ɗau ciki ɗaya suka fito.
Ƙanƙance idanu cike da bala'i Hajiya jummai tayi tana fuskantar Hajiya Hauwa "Ke a tunanin ki zata bari ne? Ko dan ba a gaban ki yazo ya tsuguna yana kuka da hawayen shi shar-shar na aje a roƙa mishi Hafsatu da Ahmadu su amince su bashi Fauziyya ba?! Kwanar uwar mu 9 fa a cikin ƙasa lokacin, shine yaya Zuwairah ta tsinke shi da mari don ya dawo cikin hayyacin sa toh tun daga lokacin suka ɗaura gaba shi yasa baki ganta ta ɓata ƙafar ta zuwa suna ko barka ba. Amma kuma Tahir ya Haihu ya manta da tashi uwar a barzahu ya saka sunan wata tsohuwar najadu"
Mamaki ne matuƙa ya kama Hajiya Hauwa ta riƙe baki tare da zaro idanu "Hasbunallahu wa niimal wakeel. Shine kuma kuka bari ya aure ta?"