← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 57

Sashe 38

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai bata yi rabin hanyar ɗakin ta ba Reina ta cin mata ta sake shaƙurota ta haɗa da garu sannan ta kunna lighter ɗin ta kai saitin bakin ta da nufin ta tsorata ta, kaman yanda itama Jamal yake mata duk lokacin da tayi yunƙurin tona masa asiri ko kuma ita Auntyn ma take razana ta idan tayi Ashar har sai tayi kuka ta bada hakurin ba zata sake ba.

"Me zaki faɗa mata munafuka! Ni babu abinda nayi algunguma!" Baki ɗaya jikin ta rawa yake yi.

Amma a rashin wayo sai ta kai lightern daff da laɓɓen bakin Maama wanda zafin wutan ya saka ta sakin razanannen ƙara cikin azaba wanda ya karaɗe ilahirin gidan.

Ba zata ce daga ina Auntyn ta faɗo ba, gigitaccen marin da ya sauƙa a fuskar ta shi kawai ya sanar da ita zuwan ta. Har ƙasa marin ya kai ta, lightern ya faɗi daga hannun ta shima yayi gefe, haka ma jin ta da ganin ta lokaci ɗaya suka ɗauke.

Abin bai ishe Fauziyya ba ta saka ƙafa ta hanƙada ta wanda a sanadin tsautsayi da ƙaddara ta fara gudundulowa daga kan benen tun daga na sama kan ta da jikin ta na buguwa tana ihu!.

Lokaci ɗaya hankalin Fauziyya ya dawo jikin ta, fushi da ɓacin ran da suka makantar da ita suka yaye. Ta ma manta da ƙaramin ciki a jikin ta don haka da gudu ta fara sauƙa daga benen domin ta je ta ceci ƴar ta.

Sai dai ƙaddara ta riga fata, Mugun ganin da tayi ya saka ba don ta riƙe handrail na stairs ɗin ba to da itama kifawan zata yi.

Reina bata tsaya a ko ina ba da fasasshen goshi, sai a saitin ƙafar Alhaji Tahir!.

Rana ta farko kenan da Fauziyya zata ce ta ji abinda ake ce ma tsananin tsoro ga kuma tashin hankali, nadama kuwa ya lulluɓe ta kaman bargo.

A take jikin ta ya kama kyarma gashi idanun ta ya gagara fita daga cikin na Tahir da take hango wutar dake ci a cikin su.

Ba zata ce ita take sauƙo da kanta ba domin ƙafan ta rawa suke yi amma a haka suka kawo ta har gaban shi yanda har yanzu Reina take yashe, babu tabbacin ko tana cikin hayyacin ta amma ya gagara ko sunkuyawa ya ɗaga ta ya nima mata agajin gaggawa.

"T..... Dan Allah...."

Ji yayi kaman ta ɗona mishi wuta yayi saurin ƙwace hannun shi ya matsa daga jikin ta yana mata kallon tara saura kwata.

"Kin kashe min ita kin huta ko Fauziyya?" Da mamakin ta muryar shi da sanyi.

Girgiza kai ta shiga yi lokaci ɗaya hawaye na wanke mata fuska.

"Wallahi T Maama ta..."

"Ya ishe ni!! Ko yaushe kika buɗe bakin ki Maama! Maama! Maama!!!. Haba! Wata iriyar uwa ce ke?!" Ya faɗa cikin ɗaga muryar da saida ta rintse idanun ta.

Zuba tayi a kan guiwowin ta ta rungumo Reina jikin ta tana kuka "Don Allah kayi haƙuri T, wallahi nayi nadama, ba zan sake ba Allah kayi haƙuri!"

Jin haƙurin da take bashi yake yi kaman tana zagin shi, don haka ya sunkunya ya fincike ƴar shi daga jikin ta hade da faɗin "Tunda zama ya gagare ki da ƴata, Na sauwaƙe miki ki je gidan ku ki baje, ke ba dole na bane su ne dole na"

Ya juya zai bar cikin gidan da Reina a hannu. A kiɗime hajiya Fauziyya ta sha gaban shi "Na shiga uku, mai kake nufi T?"

Mummunan harara ya watsa mata yace "Ina nufin na sake ki Fauziyya!, ko baki gane Hausa ne inyi miki da wani Yaren?!"

Girgiza kai tayi "don Allah kada kayi min haka T. Da ciki fa a jiki na!" Ta rungume shafaffen cikin ta ko zai tuna ya janye maganar shi.

"To ki ajiye sakin idan kin Haihu sai ki ɗauka!"

Da faɗan haka ya fita ya barta daskare a wurin.

.....

Ko sallama bata iya ba ta isa cikin gidan janye da akwatin ta tana kuka Wiwi.

Ummi dake kitchen tayi saurin fitowa haka ma amarya Sajida dake wanke-wanke a bakin famfo ta miƙe.

Ganin akwatin ya saka gaban Ummi faɗi.

Daman ta sani ta kuma saka ma ranta cewa rana irin wannan na zuwa, ba fata take yi ma Fauziyya ba amma a yanayin da aka yi auren, ta sani kaman dole ne ko ba daɗe ko ba jima rana irin wannan na tafe, amma bata yi tsammanin idan yazo zai girgiza ta haka ba.

Jefar da akwatin Fauziyya tayi ta rugo ta shige jikin mahaifiyarta ta saki kuka mai tsuma zuciya.

"Ummi Tahir ya sake ni, na shiga uku Ummi, Reina ta kashe min aure"

Ɓanɓarota tayi daga jikin ta tana kallon fuskar ta. "Kaman yaya?!" Ta tambaya a kiɗime.

Cikin kuka Fauziyya ta cigaba da cewa "ummi ban yi mishi laifi ya sake ni ba, mutane ko ƴan uwan shi basu shiga tsakanin mu sun saka ya sake ni ba, banbancin dake tsakanin mu bai saka mun rabu ba Ummi sai ƴar shekara tara! A kan ƴar shekara tara Tahir ya zaɓi ya haƙura da ni."

.....

Sallama Yaseer yayi a parlourn, cikin wanda ke zaune a kujerun cin abincin aka samu masu darajar amsa shi.

Sai kawai ya gaida su a tsatstsaye kafin su yi tunanin ya zo ya saka su a gaba suna cin abinci, daman mahaifin shi ne ya wajabta masa gaisuwan ma shi ba ra'ayin ta yake da shi ba don duk takura ne.

Har zai juya ya tafi Muryar ta ya dakatar da shi.

"Laaa kai ne?!!" Ta tambaya da mamaki tana durowa daga kujerarta ta nufo shi, sai ji kawai yayi ta ƙaraso a guje ta faɗa jikin shi ta rungume kunkumin shi.

Kallon ke kuma daga ina yayi mata, nata idanun ma na cikin nashi tana faman washe masa baki.

Babu ɓata lokaci ya gane ta, saidai kuma kamannin ta da komai ya canja, ta yi tsayi ta ƙara haɓɓaka.

Ɓanɓare ta daga jikin shi yayi ga idanun kowa a kan su, yace. "Yaya kin warke yanzu ko?"

"Bayan ma baka dawo ba tunda ka tafi? Kuma kace zaka kawo min abun daɗi nayi ta jiran ka."

Ta turo baki amma idanun shi na kan ɓarin goshin ta dage rufe da bandage, ga sauran raunukan fuskar ta da suka warke sun bar ƙananun tabo.

Wato ita wannan yarinyar ko yaushe a cikin jin ciwo take.

"Toh yayi kyau" Juyawa kawai yayi tafiyar shi ya barta tsaye a wurin, har zata bi shi Hajiya Hauwa tayi saurin kiran ta tazo ta ƙarasa pancake ɗin da ta azabtar dasu a kai.

.....

Yau saboda faɗan Hajiya Hauwa Jamal ya fito zuwa 9 da 40, amma tunda yazo yake faman chat a waya, ga apples da ya fito da su don yayi ƙwalele ma Yaseer ɗin yana ta gaftara kaman ƙarago.

Awa ɗaya Yaseer yana faman ɓaɓatu a banza don haka rai a ɓace yayi wurgi da markern ya dubi Jamal.

"Wai kana tunanin ni kake cuta ne idan kana rashin hankali?" Barin taunar Jamal yayi ya ɗago yana kallon shi sheƙeƙe.

"Wallahi idan zaka shekara ɗari da tamanin a gida ba sha takwas ba ni ko a kwalar riga ta. Sannan ba zaka rage ni da komai daga cikin ilimi na ba banza shashasha"

A fusace shima Jamal ɗin ya miƙe, amma ganin tsayin su akwai rata sosai tsakanin shi da Yaseer ya saka shi sassauta fushin kana ya nuna kan shi da yatsa yana faɗin "Nine banza shashasha? Ɗan ƙauye irin ka ne yake kira na banza shashasha??"

"An kira ka banza shashasha ko akwai abinda zaka yi ne? Na ƙara da wawa daƙiƙi!"

~~~~~~~~~~

*Hajiya Fauzah yau ba Tea ba ko buredi ne kina ruwa😂*

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

27......Gwada Yaseer da yatsa Jamal yayi kawai, ba tare da yace komai ba ya koma ya zauna. Sai da Yaseer ɗin ya juya bayan shi ne wurin da idanun Jamal ɗin suke kallo ya hango dalili, ashe mahaifin shi ne yake tahowa.

Ɗukar da kai Jamal yayi lokacin da Alhaji Salisu ya ƙaraso wurin ya zauna a hakimce, yana kallon Yaseer ɗin da ke ƙoƙarin daidaita fushin sa.

Sai kuma ya samu zuciyar shi da addu'ar Allah yasa kada su kore shi, domin har ya gama lissafin nauyin da yake son sauƙe ma iyayen shi da kuɗaɗen da za su dinga biyan shi.

Da haka kawai ne, tabbas da Yaseer ba zai ƙara ko minti biyar a gidan ba bayan zagin da ya ƙare ma ɗan shi, amma abinda ya faru satin baya ya sauya komai.

Fitan da yayi bayan zuwan Yaseer ɗin a wancan Ranar har mahaifiyar shi ta turo ayi mishi ƙaryar ta aike shi, bai tashi dawowa gida da ƙafafuwan shi ba sai can dare aka shigo masa da shi a buge a karo na farko.

Tabbas yana sane da cewa Jamal yana shan sigari da su shisha haka saidai ya ɗauki hakan ne a yarinta kuma da ya girma zai bari tunda shima ya ɗan taɓa a baya, amma samm ba zai lamunci shan giya ko kayan maye ba.

Domin haka yanzu burin shi ɗaya shine ya tura shi matakin gaba a karatu, ko zai fara sanin ciwon kan shi.

Fuska ya ɗan sake kaɗan yace "a yi haƙuri Yasiru, zai canza dolen sa. Akwai abubuwa da yawa dake jiran nasarar shi, dole zai nutsu yayi ilimi, wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗi?"

Sannan ya juya wurin Jamal yana watsa masa harara, ya fara gwada shi da yatsa yana kaɗawa "Wallahi wallahi, idan wannan karon baka ci jarabawa ba, na rantse maka babu inda zaka je. kuma zan tsame hannu na daga nima maka wani taimako, ba kuma zaka fasa maimatawa ba har sai ƙannen bayan ka sun ƙaraso sun riske ka."

Rau-rau da idanu Jamal yayi, ya ɗago yana kallon shi "Toh... Toh amma Daddy, karatu a waje ba'a buƙatar jamb fah, da tuntuni na tafi da wallahi na kusan gamawa ma yanzu, tunda ba'a daɗewa, balle har wasu suna min kallon banza"
Chapter 38 · 0% Book details