← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 57

Sashe 11

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

08.....juye-juye kamal yake yi a tsakiyar parlourn kaman wuyan shi zai tsinke. Ba don shi da ƙafar shi ya shigo ba zai iya rantsuwa cewa ba a Najeriya yake ba amma wai ƴan uwan shi Hausawa ne ke rayuwa a irin wannan aljannar duniya.

Sallamar Hajiya Fauziyya ne ya maida hankalin su duka biyu gare ta, tana tafe da jaririyar ta rungume a ƙirjin ta, kamar kullum fuskar ta ɗauke da murmushi.

"Mama Bismillah ku zauna, sannun ku da zuwa" tace yayin da itama take niman wurin zama a kujeran dake kallon nasu.

Parlourn tsit babu hanayiya ko kaɗan sai ƙarar na'urar sanyaya wuri dake aikin sa babu gajiyawa. Har goggo saida tayi mamakin saurin fitowar hajiya Fauziyya don ta ɗauka sai sun gama shanya ta kafin ta fito kaman yanda sauran matan ƴan uwan Tahir ɗin ke yi.

Gyara zaman Reina tayi a cinyar ta cikin kiyayewa saboda kada ta tashe ta daga baccin da aka samu tayi da ƙyar bayan ta gama ihun ta ta gaji, sannan ta ɗan zame kaɗan daga kujerar ta gaida Goggo Halime.

"Mama Ina wuni, kun iso lafiya?" Kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara ganin ta yasa tayi tunanin ba a nan cikin gari suke ba, domin bata san kamal ba bata taɓa haɗuwa da shi ba don haka bata san shi waye ba, masu aikin ta dai sun shaida mata ƴan uwan mai gidan ne, sai dai fuskar shi yana mata kaman ta san shi a wani wurin amma ta rasa ina?.

A take Goggo Halime ta saki fuska ta ɗauko murmushi ta yafa ganin kirkin matar Tahir. "Sannu dai ƴar nan, mun same ku Lafiya? Yaya kishiyar tawa?"

Miƙewa tayi da nufin ta miƙa mata Reina ta ganta, tana amsawa da "lafiya ƙalau, an gode Allah" karɓan ta goggo tayi "Masha Allah, kishiyar tawa jajawur abin ta"

Komawa Hajiya Fauziyya tayi ta zauna tana dariya "Ai da shirin ta tazo na ƙwace mai gida"

"Ta makara ai, tunda har rai yayi halin sa, saidai mu jira wanda zata dirje ta zaɓo mu aure shi tare"

"Allah sarki, Allah yayi mishi rahama" tace cikin alhini.
Goggo ta amsa da "ameen ƴata"

Daidai lokacin masu aikin gidan guda biyu suka shigo kowa ɗauke da tray a hannun ta suka dire a gaban su.
Na farkon na ɗauke da ruwan gora mai sanyi ɗaya da mara sanyi kuma, sai juice ɗin kwali da kuma glass cup. Sai ɗayan mai ɗauke da soyayyar naman kaza anyi pepper ɗin shi da kuma kayan ƙwalam na fulawa irin su donut.

"A'a har da wahala haka?" Tace tana washe baki, murmushi kawai hajiya Fauziyya tayi "Kamalu kaga zuba min ruwan nasha" ya durƙusa ya bude lemon kwali ya tuttuɗa mata a kofi domin da hankalin shi ba zai bata baƙin ruwa ba bayan ga mai kala nan a kusa.
Shima ya cika nasa kofin kafin ya koma ya zauna sannan suka shiga gaisawa da Hajiya Fauziyya yana yi yana kurɓan lemo, kana ya shiga mata bayanin daga inda suke don akwai buƙatar hakan.

"Ban san ko kin gane ni ba, mijin Saudatu ne da tazo miji barka Ranar Alhamis"

kaikaitar da kai tayi tana son tuna wata Saudatu ce, domin yawan wa'inda suka dinga zuwa mata barka a kullum ba zata iya kiyaye su ba.
Daga ranar suna ne ma Alhaji Tahir ya samu saran dawowa da wuri suna cike a gidan sai yayi musu kora da hali ko kuma ya ɗauke Hajiya Fauziyya su yi ciki ba zasu sake ganin ta ba, toh fa shine suka shafa musu lafiya yau babu wanda yazo.

Ganin bata gane ba yasa ya canza akalar bayanin nasa "Ai ni ɗan uwan su Alhaji ne. Goggo nan da kika gani ƙanin mahaifin su ne uba ɗaya"

Da sauri ta gyaɗa kai "Kai ne baban Yaseer kenan?"

Ya ƙara washe baki ganin yanzu ta gane "eh wallahi Hajiya"

"Yaya jikin umman Yaseer ɗin? Don tace bata ji daɗi ba ranan"

"Ai ta sauƙa ai, an samu ɗa namiji" goggo ta amshe zancen,
Hajiya Fauziyya ta ƙara washe baki."Ah Masha Allah, Allah ya raya, yau kenan ko jiya?"

"A'a yau kwana uku kenan, suna barin nan gidan abun yazo"

Tunawa tayi da alƙawarin da tayi musu na za'a maida su gida, ashe baiwar Allah kanma na cikin halin naƙuda, Allah dai yasa da suka fita sun samu abun hawa ba wai a sanadin ta haihuwar ta taso mata ba.

"Allah sarki, ai kuwa bamu ji ba, zamu je muga baby in Allah ya yarda"

"Shiyasa ma muka zo ƙafa da ƙafa domin mu sanar da ku don ma kada kuce baku jin ba" Goggo Halime ta amshe. ina amfanin zumuncin ɓangare ɗaya kawai? Idan ɗaya bangaren suma suka sada nasu zumucin ai abun zaifi armashi- Take tunani a ranta.

"gashi kuwa baban ta bai dawo gidan ba tukunna, zaku jira shi ina babu matsala?"

Goggo da ta shanye lemon ta tass ta miƙa wa Kamal kofi ya ƙara mata sannan ta tambayi "zai kai dare ne?"

"Eh gaskiya amma zan kira shi in sanar da shi, in sha Allah zai dawo da wuri"

Ta tashi da niyyar taje ta ɗauki wayar ta ta kira shin a ciki dai-dai lokacin da Reina ta tsalla wani ihu kaman wanda aka mitstsine ta.
Sauƙe numfashin ƙosawa Fauziyya tayi tare da juyowa tana kallon jaririyar dake ƙara sautin kukan ta har wani sassandarewa take yi idanun ta kuwa a rufe ruff.

Goggo ta riƙe baki ganin abun nata na yi ne"Kaji min ƴammatan zamani wato tun ban tare a gidan ba kin ba har kin fara kishi da ni"

Cikin ƙosawa tace "Ni da ku tafi tare ma kawai Mama ko zan samu in ɗan huta da rikicin Reina, bata gajiya da kuka wallahi"

Dariya Goggo Halime tayi irin nasu na manya tana faɗin "ƴar nan mai aka yi da maza? Har kin gaji?"

Taɓe fuska tayi ta koma ta zauna, Allah ya gani ita ainihin ta ba mai son yara bane balle ta saba da fitinar su, wannan ma don nata ne daga jikin ta ta fito don haka babu yanda ta iya amma ko ƴaƴan yayun ta ba ɗauka take ba idan taje musu, tafi gane yaro yayi hidiman shi itama tayi tata kawai.

"Allah mama kukan banzan ta yayi yawa, ban isa in saka kafaɗa na da nufin in huta ba. Raya dare take tana kuka kaman abun jin baki".

Shawarwari ta fara bata na yanda zasu ke mata idan taƙi yin barci yayin da kamal ya maida hankalin sa ga talabijin wanda ake nuna wasan ƙwallon raga(tennis).
Bayani take mata tun daga kan yanda ya kamata ake mata wanka da gasa jiki da kuma kwanciya duk da wasu abun fauziyya jinsu kawai take yi amma tasan ba zata iya ba, kalan taje ta karya ma Alhaji Tahir ƴa ko ta kashe ta? Yanda taga yana ji da Reina kamar ƙwai?.
Har salon shayarwa saida Goggo Halime tayi ma Fauziyya gyara ta fara gwada mata kalan riƙon da zasu dinga yi ma Reina ta dinga samun nutsuwa ai kuwa kaman an kulle bakin sai ƙifi-ƙifi kawai take da idanu.

Fauziyya taji daɗin hirar sun don haka suka rashe a parlour suna ta zantawa sun ma manta da zancen kiran Alhaji Tahir, shikuwa yana ta tara mata missed calls waya na rufe a ɗaki babu wanda ya ji, sai gaba ɗaya hankalin shi ya tashi cikin gaggawa yake ƙoƙarin kammala aikin gaban shi don ya dawo ya duba ta ko lafiya.

Har maghriba ta riske su basu ankara ba saida aka sanar mata da lokacin wankan yamman su yayi.

"Mama kuyi haƙuri barin kira shin kafin kuyi Sallah ku ci abinci ya iso in sha Allah"

Bata yi mata musu ba don mutumin da ya karrama ka ya gama maka komai, da kanta ta kai ta ɗakin da suka yi alwala suka jira aka kira sallah kafin Kamal ya wuce masallaci goggo kuma tayi nata sallan a ɗakin, tana idarwa aka shigo musu da abinci mai rai da lafiya suka ci suka yi Isha kafin suka dawo parlour lokacin har hajiya Fauziyya tayi wanka ta shirya sun samu Reina tayi barci bayan ruwan ɗumi ya ratsa jikin ta, don haka ta barta a ɗakin.

Suna zama Alhaji Tahir na faɗowa gidan kaman daga sama, ko ƙwaƙƙwaran sallama babu. "Fauzah lafiyar ki?"

Da sauri ta miƙe ganin yanayin shi.

"Ina wayar ki?" Ya sake jefa mata tambayar a ɗan fusace ganin ƙalau take ta ɗaga mishi hankali.

Juyawa tayi ta ɗauko wayar daga matsugunin ta ta miƙa mishi, ya karɓa ya danna hasken wayar ya kawo sannan ya juya mata screen ɗin zuwa duban ta. "Kina ina nayi miki 13 missed calls baki ɗauka ba"

Karɓan wayar tayi tace "laa, banma gani ba sai yanzu, wayan yana ɗaki ne kayi haƙur.."

Saurin katse ta yayi da "ba nace miki ki daina ajiye waya kina tafiyar kin nan ba? Meye amfanin ta toh idan ba zai dinga kasancewa tare da ke a ko wani lokaci ba?"

Numfashi ta furzar ganin yanda yake masife ta a gaban jama'a, kaman ma bai lura da su ba don haka ta sauƙe murya kana tace "Allah ya huci zuciyar ka, ga Mama nan tazo duba mu."

"Na ganta ai" yace tare da ƙaramin tsakin da bai san ma ta fito ba, gabaki ɗaya ran shi a ɓace yake ganin a kansu ne ta manta da duniyar shi.

"Uhmm Tahir Ina wuni?" Goggo ta gaida shi ganin yanda ya tsaya musu ƙeƙam a kayi.

Bai so ba ya tsuguna har ƙasa kana ya gaishe ta da "Goggo ina wuni, kun iso lafiya? Yaya gajiyar hanya?" Duk a tare ya miƙa mata gaisuwar don haka sai ta amsa da lafiya kawai sannan ya miƙe ya zauna a kujera, Hajiya Fauziyya kuma ta tafi kawo mishi ruwa da basu wuri don su zanta tsakanin su.

Tace "Ashe an samu ƙaruwa"

"Eh wallahi, an samu Hafsatu Reina"

Jin ɗayan sunan tayi yayi mata banbaraƙwai tace "Allah yasa cikon addinin Muslunci ne. Shima matar shi Allah yayi mata sauƙa yau kwana uku."

"Allah sarki, Allah ya raya"

"Ameen"
Chapter 11 · 0% Book details