← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 57

Sashe 54

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku fice min a gida kafin in saka a fitar min da ku!" Hayaniyar wurin sai da ya ragu saboda ihun da Alhaji Tahir yayi, Reina dake jikin shi ta ƙanƙame jikin ta cikin firgici.

"Na faɗa a kunnen shi ya shaida, Allah ya shaida, ina so kuma ku shaida na yafewa Kamalu duniya da lahira. Idan hakki na ke bibiyan zumuncin yaran shi har suke cutar da junan su ta ƙarƙashin ƙasa na yafe, Wallahi na yafe har abada"

Ta riƙo Saudat dake kuka Kamal ya taya ta suka bar gidan, ba zasu iya tsayawa su ga yaya za'ayi da Yaseer ba. Sun bar musu shi suyi yanda suka ga dama, amma sun bada amanar shi ma Ubangiji Azza wa Jalla.

A wulaƙance suka ja Yaseer bayan iyayen shi sun yi tafiyar su. Meesha tayi yunƙurin bin shi a baya Hajiya Hauwa ta saka nauyinta ta danne ta.

......

Sai da ya tashi mutuwa musu a cell ranan kafin suka kai shi asibiti aka kula da raunukan shi suka bashi abinci.

Tun da ya samu kan shi kuma ya duƙufa ma yin taimama yayi sallolin nafila da tilawar Alkur'ani da addu'o'i kaman yanda iyayen shi suke yi a gida suma ba dare ba rana, Allah ne kawai zai iya fitar da shi daga wannan gadar zaren.

Kan kace mene har magana ya fara yawo, tunda burin Alhaji Tahir kenan ya tozarta shi. Ya mayar da hankali a kan biyan mutane a yayata Yaseer a social media a maimakon ya mayar da hankali ga lafiyar ƙwaƙwalar Reina kaman yanda likita ya shawarce shi.

Tana tsakanin buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa saboda kada a gaba abinda ya faru yayi mata sanadin trauma, har yawan suman da take fama ɗinnan ma yana da alaƙa da hakan sosai.
Sai dai suna zuwa sau ɗaya ta gwada mishi bata so ya ajiye zancen a gefe, domin yanzu lallaɓa ta yake yi kamar ƙawai shiyasa ya bar Maama a wurin ummi na wani lokaci.

A ranar da za'a fara shiga Shari'a kuwa yan jarida sun yi cincirindo don haska fuskar Yaseer a kafofin sada zumunta . Yawanci Alhaji Tahir ne ya biya su duk da cewa case ɗin ya jawo hankalin mutane sosai a kafofin sada zumunta , mutane nata tofa albarkacin bakin su jin alaƙar su da yarinyar da ya lalatawa rayuwa da kuma ƙarancin shekarun ta, kowa na mararin ganin yaya lamarin zai kaya.

Aka shiga zama na farko bayan an gabatar da shari'a guda biyu a gaban su sannan aka gabatar da Shari'ar su a gaban alƙali, lauyoyin da aka ɗauka ma Reina har guda uku, da ƙyar su Saudat suka haɗa suka ɗauki lauya guda ɗaya. Sannan sun buƙaci a ɓoye information ɗin Reina daga sunan ta da komai, haka ma babu buƙatar gabatar da ita a gaban kotu saboda karenta daga idon Duniya da kuma tattalin goben ta. bayan shi Yaseer mara gata an gama tagayyara shi.

A kan halin da Yaseer ya shiga sun kashe kuɗaɗe har sun ji babu daɗi, ƙarshe har gidan da Kamal ya samu ya mallaka bayan zaman haya a cikin ta na tsawon shekaru sai da ya ɗaga shi ya siyar, don kawai ya kuɓutar da ɗan shi.
Dabbobi da gona a ƙauye ma an haɗa an siyar saboda da gangan ake wahalar da su kuma sun riga sun fahimci a wannan ƙasar kuɗi ke magana ba baki ba, kudi ke aiki ba hannu ba, kuɗi ke bada gaskiya, kuɗi ke bada ƴanci, amma su nasu kuɗin ya kasa, ƴan canji ne a gaban wanda suke karawa da shi.

Alƙalin da aka gama cikawa aljihu da kuɗaɗe ya daga shari'ar nan da sati biyu, sannan ya buƙaci lauyoyin ko wanne bangare su kawo shaidu domin kare wanda suke wakilta.

......

Test ya kai ta makarantar kawai amma sai da tayi danasanin zuwa.

Yau har an samu masu tsayawa a gaban ta su gaya mata magana saboda Yaseer. Mutanen da a da ko cikin ido wasu basu iya kallon ta, amma dan yau kawai Allah ya ga daman jarrabar bawan sa shine ya dawo musu abun jin daɗi abun izgili?

Ko sallama bata yi ba, da shigowar ta parlon tayi wurgi da hand bag ɗinta zata wuce sama ɗakinta, mahaifiyarta ta kirawo sunan ta tare da miƙa mata waya.

"Waye ne?" Ta tambaya tana turo baki. Idan mahaifinta ne ma ba zata karɓa ba don bata jin zata iya jurewa sauraron masifan shi a yanzu.

"Bilal ne."

Har tana tuntube ta ƙaraso ta karɓi wayan ta ƙara a kunne.

"Uncle B" ta kira cikin muryar kukan dake taso mata tun kafin yayi mata magana.

"Ameesha haka zamu yi da ke?" Wata murya mai sanyi ya amsa ta ɗaya ɓangaren.

"Wallahi Uncle B he's innocent. Yaseer is not a horrible person"

"Wannan kuma court ne zata yanke wether he's innocent or not ba ke ba."

"Uncle B na san waye Yaseer, ba zai taɓa yin abinda suke zargin shi ba. Sun fi ƙarfin shi ne kawai Uncle B don Allah ka taimaka min"

"Shikkenan Meesha, amma kin san everything comes with a price right?"

"Idan ka taimaka mishi ko me kake so zanyi Uncle B."

"That's great. Then I'll get him a good lawyer amma da sharaɗin!... Babu ke babu yaron nan Ameesha, and ina nufin har abada"

Kukan ta ne ya karu "Don Allah Uncle B!. Zan iya canza course ko wani abun amma banda wannan. Ina son shi Allah."

"Shikkenan, sai ki bari idan ya gama serving time ɗin shi a jail ya fito ku cigaba da soyayya ko?"

Hakan ma shawara ne. Amma tayi ma Yaseer adalci? Koda ace ta shirya ma zaman jiran shi amma goben shi fah?.

Yana shirin katse kiran tace "naji, ka sama mishi lawyern zan rabu da shi"

"Good girl" shine Abinda yace kana ya kashe wayan daga ɓangaren shi.

......

“Wannan kotu, bayan ta saurari kwararan bayanai daga bangarorin biyu, da shaidu da rahotannin lafiya, ta tabbatar da cewa Yaseer Kamal, wanda ke ɗan uwan jini ga wanda abin ya shafa, ya aikata ƙoƙarin fyade ga yarinya ‘yar shekara tara.

Wannan kotu tana ɗaukar wannan laifi a matsayin wani abu mai matuƙar muni, wanda ya keta doka, zumunci, da kariyar da yara suke da ita a bisa doka.

Bisa la’akari da sashe na Penal Code da kuma dokar VAPP da Jihar Bauchi ta amince da ita, wannan kotu tana yanke maka hukuncin shekaru sha biyar a gidan gyaran hali, ba tare da yuwuwar beli ba.”

"Alhamdulillah" shine kawai kalmar da bakin shi ya samu daman furtawa. Idanun shi a rintse har Yan sanda suka ɗauke shi daga gaban kotu, cikin sanyin jiki yake bin su. Ihu da kuka daga bangaren iyayen shi da ƴan Jama'are da suka zo mara masa baya ya kankama, har suka wuce da shi idanun shi na kallon ƙasa, ba zai iya haɗa idanu da ɗaya daga cikin iyayen shi ba.

......

"Daddy... Daddy Wallahi ba yaya Yaseer bane, ƙarya nayi daddy....."

......

"Wannan expulsion letter ne, sun kori Yaseer daga makarantar.
~~~~~~~~~~

Hmm... Sannun mu.

Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

39..... WAIWAYE.

"Ah ah, Halime ta Kamalu, yanzu ɗaukar ɗanwaken kika yi kika ba shi?" Dattijuwar da ta shigo ɗauke da kunu mai zafi a cikin kwanon sha ta tambaya, kana ta dire shi a gaban Halimen dake kishingiɗe a kan shinfiɗin da aka yi mata saman tabarma hannun ta na ɗama a daure.

Kariya ce ta samu a sanadin ƙwatar Kalabu da taje yi a hannun kamalu lokacin da ya ɗauko tabarya zai rotsa ma yaron saboda yanzu kuntalancin sa har ya kai yana saka hannu cikin aljihun uban shi yana masa laluɓe.
Shine aka rasa mai shiga ukun da zata shiga tsakani sai ita dai Halime tsugudidi kaman yanda suka laƙaba mata a gidan, don ita komai da ruwan ta.

ta kuwa yi Sa'a ya sauƙe mata taɓaryar a hannu, a take ya raba mata ƙashin wurin gida biyu. Sannan yanzu a tare suke jinyar, ba wai raba zafi ko taya ta ɗawainiya yake yi ba A'a, duk abinda ta samu ne dai nasu ne su biyun, duk abinda aka kawo mata na taɓawa tare zasu ci.
Koda ace bayi kusa ta samu abin daɗi zata rage masa, a dalilin haka bayi fashi kullum sai ya zo dubata a ƙalla sau biyu zuwa uku a rana, ita kuma a tunanin ta ƙauna da yan'uwantaka ne hakan, har yake barin iyalan shi da kasuwan shi ya zo ya kasance tare da ita saboda danasanin abinda ya faru da ita da ya kasa barin shi.

Da wuya ka taɓa jin Halime ta ƙyalƙyala maka da dariya. Ko tatsuniyoyin nishaɗi ake yi haka zata yi ɗan dariya kaman nishaɗin bai kai zuciyar ta ba, tayuyu tafi kowa jin daɗin ta kuwa saboda ita mutum ne mai son ko yaushe ta kasance cikin nishaɗi bata son taga wani yana ƙunci a kusa da ita balle ita da kanta. Amma kunya, kawaici da sanyin hali su suka yi mata ƙawanya, har aiki idan kana son kaga saurin shi toh gwanda kayi kayan ka da ka haɗa Halime da shi, duk da cewa bata da ƙyuya kuwa.

A yanzun ma murmusawa tayi irin nata ita kaɗai, "Inna wai bayi son ɗumame ne yau ɗin, ya gaji da cin ta kullum"

Kuma shine ya haɗa iyalan shi da ɗumamen? Yazo yana cinye wa mai jinya abinci?.

Amma dake duk jirgi ɗaya ya ɗibo Halime da mahaifiyarta sai cewa tayi "Allah sarki, to ga wannan kunun ki sha da ɗumin sa, zai riƙe miki ciki"

A lokacin Salisu yayi Sallama da ƙullin sugar a hannun shi ya miƙa ma Innan Halime.
Kallon ƙullin sikarin Naira ashirin tayi, tana mamakin ko har ya sake tashi ne haka? Wannan tsadan rayuwa dai Allah yayi mana maganin shi.

Karɓan sikarin tayi lokacin da idanun ta ya sauƙa a kan Naira biyar ɗin dake gaban aljihun rigan Salisu da ya sha mandaƙo.
Chapter 54 · 0% Book details