← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 57

Sashe 19

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Addu'a yaseer yayi ya zurma ƙafar shi kana ya rufo musu ƙofa Kamal ya saka ma gidan ƙwado sai Jama'are.

....

Ta manta da kunya ta manta da kawaici ta manta da idanun magabata da ma ƴan baya dake wurin, ita karan kanta ta manta da lokacin da ta saka hannunta ta zagaye shi tare da cusa kanta cikin ƙirjin shi ta saki kuka lokacin da taji yawan albashin da za'a ke biyan shi. Naira na dukan Naira har dubu ɗari da goma.
Shikkenan hutu yazo, wahala ta ƙare musu in sha Allah.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

14......Gida-gida aka dinga shigowa ana yi ma Kamal Allah ya sanya alkhairi bayan wuri ya rufa kuma sun samu hutawa.

Yara ke layin rattaɓa sallama ɗauke da ƙwaryan abinci, wasu ma kansu suke lulluɓewa su kawo ko su tura ƴaƴan su ƴammata.

An saba yi musu tarba makamancin wannan amma tabbas na yau ɗin daban ne, domin kafin almuru ya gama lulluɓe gari da duhun shi gidan goggo babu masaka tsinke, sun yayyame Saudatu da kamal kaman sabbin amarya da ango, harda masu kawo ƙoƙon baran su ma ƴaƴan su d kula jikokin su dake karatu a halin yanzu, suma idan sun sami kammalawa Kamal ya saka baki a sama musu aiki.

Washe baki kawai yake yi yana binsu da kallo, ita nasara tafi daɗi idan mutane basu san gwagwarmayar da kayi kafin ka same ta ba, saidai a ga murmushin ka amma ba'a san dararen da ka share cikin ƙunci, yunwa da rashin barci ba.

Sun ci nama, sun sha madara, ga kuma kayan itatuwa da ba'a cika samun shi a cikin gari ba ko da kuɗin ka kuwa kowa ya tsinko na gidan shi an cike gaban su da shi.
Sai da aka ragu a ɗakin zuwa alwalan  sallar maghriba Kafin ya shiga mayar wa mahaifiyar shi yanda abun ya kasance, don har yanzu jin kan shi yake yi kaman a mafarki.

"Na hana idanu na barci Kamalu, kullum kana cikin addu'a ta amma bayan na je na gano halin da kuke ciki ban sake samun nutsuwa na ba sai a yau"

Da ace wayewar su ta fi haka zuwa zai yi ya rungume ta, ya gwada mata tsantsan farin cikin da yake yi kasancewar shi mai sa'ar da ya samu mahaifiya irin goggo Halime. Amma ya gode ma Allah ma tunda bata masa kunyar ɗan fari ko kaɗan.

"Komi lokaci ne goggo, abubuwa sukan zo ma bawa a lokacin da bai yi tsammani ba"

Ta jinjina kai "haka ne. ni ba ma kai nake ji ba kaman yaran nan nake ji da kuma Saudatu baiwar Allah. gidan su basu san babu ba basu saba da shi ba, rufin asirin Allah suna da shi amma ko daga wurin Inna hajjo (mahaifiyar saudat) ban taɓa samun labarin halin da kuke ciki ba."

Tabbas Saudat matar rufin asiri ne, Saudat fitila ce dake haska duhun rayuwar shi, Saudat ɓarin jikin shi ne, ɓarin zuciyar shi. Lallai zaɓin iyaye ya zamo mishi gata, kuma biyayyar da yayi musu yayi mishi rana.

Hanzartawa yayi zuwa sallan maghriba, sai kuma ya ɗan zauna wurin don gaisawa da abokan arziƙi, kafin lokacin taron matan cikin gidan su ya ragu sai ya dawo, don yaran da Saudat a can gidan su za su kwana.

....

Dare ya kusa rabawa, Suhail da Yaseer harma da jariri sun samu barci, sai Saudat dake linke kayan Sabir tana shiryawa a jakar da suka zo da shi. Domin gobe sammakon komawa Bauchi zasu yi, duk da ta yi kewan gida amma bata jin su biyun za su iya haƙurin ci gaba da zama a nan sanin abinda yake jiran su a can ɗin.

Kowa ya watse sai makwafciyar su innayi da ta tasa Saudat da inna hajjo a gaba tana zuba kaman ƴaƴan kurna ko barci bata ji.

Sai da ta bari Inna hajjo ta bar ɗakin kafin ta matso kusa da Saudat cikin ƙasa da murya, ba kamar ɗazu da take da tabbacin sauran maƙwafta suna jin duk abinda take cewa ba tace.
"Saudatu a baki yarinyar da zata na taya ki da wasu ayyukan mana tun da ga iyalai sun fara miki yawa yanzu?"

Dagowa Saudat tayi daga abinda take yi tana kallon ta sheƙeƙe cikin hasken jan ƙoyin da ya ƙara ma bakin Innayi kala bayan rinin da goro ya gama yi mata.

Bata ba ta damar tankawa ba ta ɗora da "ga zulaiha nan ƴar wurin harira ta ƙare karatun ta na sakandare wannan shekara , kuma mahaifin ta bayi da Ra'ayin barinta ta cigaba, ga shi har yanzu babu wani tsayyayye, to kinga zata taimaka miki ƙwarai koda Allah zaiyi ta samu mashinshini ta can kinga sai tayi auren ta a sake baki wata, don ƴammata kam masha Allah akwai su kaman Jamfa a Jos".

Murmusawa Saudat tayi, wato ko wani matakin rayuwa da mutum yake kai kalan kalubalen shi daban?!. "Innayi ni kuwa ina zan ajiye Zulaiha gida duk samari?"

"Ah-ah to ke ba mace bane? A inda kike wurin zaki ajiye ta. Ni amfanin da zata yi miki nake gani, kinga har ɗawainyar jaririn nan ma kina kwance zata yi miki komai wallahi"
Inda take na nufin ɗakin Kamal kenan?!, bata san da nufi Innayi ta faɗi hakan ba ko kuwa zuciyar ta ɗaya ne, amma koma yaya ne Rashin hankalin ta bai kai ta ɗauki kishiyarta da hannunta ta kaita har gida ba.

"Toh yanzu idan auren ya kusa naji ba zan iya rabuwa da ita ba fah? Ko ita zaman gidan ya yi mata daɗi? Kinga ai sai a samu matsala. Kuma Kina ganin tsayin ƙafar nan na Yaseer ba a banza ba, babu abinda bayi min sai dai abinda yafi ƙarfin shi."

Taɓe baki tayi ta miƙe tare da kakkaɓe jiki domin abin da ya kawo ta kenan daman. Har ta saka Zulaihan haɗa kayan ta tayi sallama da maƙwafta gobe sai tafiya amma haka Saudat ta sace mata guiwa. Ba zata bari ma Inna hajjo ta ji wannan zancen ba don wulaƙancin da zata yi mata sai ya fi wannan.

...

Kuɗin da tazo dashi da niyyan saran wani abun shi kamal ya karɓa yayi alkhairi ma iyayen su. duk wanda ya shigo musu murna ma saida aka sammusu wani abu da masu ɗari biyar da masu ɗari biyu, ƙananun yara kuma aka bisu da minti mai tsinke. Kafin su bar Jama'are dubu Arba'in katt ya tafi, amma fatan shi addu'an da zai samu daga gare su zai yi musu sanadin samun albarka ninkin ba ninkin ɗin abinda ya ɗauka ya bayar.

An haɗa musu sha tara na arziki kafin suka tattaro suka dawo da safiyar. Da suka sauƙa ma yawan ƴan unguwa da suka shigo yi musu Allah ya sanya alkhairi ba kaɗan ba.
Sai can yamma suka samu kan su, aka fito da kayan da suka taho da shi ana karkasawa.

"Ga kifin Alhaji Tahir ɗin nan. Ai yayi ko?"
Ta tura mishi gasasshen kifin a cikin ƙaramin kwalin indomie ya duba.

"Yayi in sha Allah, kuma za su ji daɗin ajiyar shi don gashin yayi kyau sosai."

Ta gyaɗa kai sannan ta jawo kwalin don ta rufe shi da kyau.
"Kuma da an fara biyan na albashi zan biya ki kuɗin ki in Allah ya yarda"

Murmushi tayi, "Haba babu komai, ka bar shi kawai, daman na tafi da shi ne zan sari wani abun daga can in fara siyarwa, amma akwai sauran Rabin da na bawa Huwaila ajiya, zan karɓa in tura ma Inna ta"

Shiru yayi da zancen amma ya saka ma ran shi zai biya ta ɗin koda ba a dunƙule ba.

.....

Yau kam Su Saudat sun sha zaman jiran Hajiya Fauziyya don ma Aina'u tayi tunanin kunna musu tv bayan ta kawo musu ruwa da abin mitsa bakin da wajibi ne gabatar da shi ma kowani baƙo. decodern yana kan channel ɗin Nat geo wild; da ake program ɗin tsuntsaye sai kuwa ya ɗauke hankalin su duka.

Bayan kaman minti talatin Hajiya Fauziyyar ta fito ɗauke da ƙaramin hand towel tana tsane hannun ta.

"Afuwan Umman Yaseer na barku kuna ta jira". Tace tana zama a ɗan gefen su kaɗan.

Washe baki tayi tana ƙare mata kallo yanda ta cika idanu ta ƙara kyau "Babu komai wallahi Aunty, mun same ku lafiya? Yaya mai sunan ƴan gayu?" Da gaske sunan ya gagare ta tunawa.

Dariya sosai Fauziyya tayi tace "Hafsatu fa sunan ta, sunan Ummi na aka mayar mata shi yasa ake mata inkiya da Reina ɗin"

Dariyar yaƙe Saudat tayi tace "Allah sarki"

Hajiya Fauziyya ta ɗaura da "yanzu na gama wanke ta ma, don kun shigo na riga na rage kayan jikin ta ne kada sanyi ya shige ta shiyasa. Amma za su fito da ita idan aka gama shiryata"

"Ayyah" tace tana zunkuɗa yaron bayan ta.

"Muga Jaririn mana an ƙulle shi a baya" tace tana miƙa hannu.

Miƙewa Saudat tayi ta warware goyon sannan ta taka ta miƙa shi ma Fauziyya wacce ta karɓe shi da Bismillah.
"Masha Allah, yanzu kam kunyi arba'in ai, don tsakanin mu ma babu nisa"

"Satin mu takwas da kwana biyu"

"Ahh masha Allah" ta saka hannu a kan goshin shi da kurajen da suka mutu sun bar tabo ga wasu ma sun fito an mulke su da farin powder, jikin shi a yamushe kaman ba na jariri ba duk da babu yunwa a jikin shi"

"Umman Yaseer kun kai shi asibiti kuwa aka duba masa kurajen nan?" Ta tambaya da damuwa shimfiɗe a kan fuskar ta.

"Wallahi zafi ne kawai Aunty, don ma tafiyan mu Jama'are sun ɗan mummutu don yanayin wurin yafi cikin gari Iska.

"Amma to kina mishi amfani da lotion da sabulun da na tura miki? yana da kyau sosai kwanan nan zaki ga duk sun baje tabon ma ya ɓace kuma jikin shi zai yi kyau sosai"

Ɗaga kanta tayi kaɗan kaman mai tunani tace "wani sabulu kenan Aunty?. Kaman cikin kayan da aka kai mana babu sabulu gaskiya"

Shiru Hajiya Fauziyya tayi
Saudat ma tayi shiru

Lokaci ɗaya suka fahimci abinda yake faruwa, Rijiya ne ta bayar da ruwa guga kuma ya hana.
Chapter 19 · 0% Book details