Sashe 10
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yaya muka iya an gama wanke shi? Barazanar zare hannun shi cikin lamarin kasuwancin mu ya fara yi, ya shiga fushi da kowa daga lokacin muka gane ba laifin shi bane."
Hajiya hauwa ta jinjina kai "Aini na sha mamaki yanda naga rana ɗaya Abban su Jamal ya amince da zancen ashe da walakin goro a miya" tana nufin mijin ta Alhaji Salisu.
"toh a lokacin ma kenan balle yanzu da an bashi ya ci, ya sha, ya shaƙa, ya taka ya yi wanka dashi. Kinga ba abun mamaki bane idan rana ɗaya ma yace ɗaukar iyalan shi zaiyi ya bar ƙasar, muda sake ganin Tahir hala saidai a darussalam."
Hajiya lubabatu tayi saurin amshewa da "Wallahi indai kuka ga Tahir ya bar Nigeria kai ko Bauchi bai isa ya bari ba saidai idan ƙasa ce ta rufe idanu na. Auren ma saboda lafiyar shi da hankalin shi yasa muka barshi ya yi ba wai don Fauziyya tafi ƙarfin mu ba, inba haka ba me aka yi aka yi dangin ta baki ɗaya da a rana ɗaya naga dama zan iya sakawa a shafe tarihin su baki ɗaya?"
"Uhmm kun dai matsa ma Masarauta iyayen Sarauniya"
saida Hajiya lubabatu ta kai wa Hajiya Farida duka kafin taji daɗi bakin ta kuwa bai mutu ba tana ta ƙara ƙular da su har suka isa Gidan Alhaji Salisu suka baje capacityn su a can, sun samu sunyi sallar maghriba haɗe da isha suka ci abinci, domin kare aji ya hana su cin na suna kafin suka ɗaura da caccakar Hajiya Fauziyya daga inda suka tsaya.
.....
Kwana biyu kenan da zuwan Goggo Halime daga jama'are tare da kishiyar ta da suke kira da Amarya, daman haka suke tun zamanin yarinta tunda anyi zaman lafiya zaman amana sai kowa a cikin su ta mayar da lamarin ƴar uwar ta ya dawo nata suna hidimar su tare har tsufa ya kama su gashi ana kan zuba jikoki.
Tuwon dawa miyar kuka suke ci daga gindin bishiyar neem dake tsakar gidan, hasken cikakken farin wata shi yake haska musu cikin farantin suna ganin wurin da suke yanka, tunda rashin wuta har ya saka raka ni kashin goggon ma ta mutu ba caji.
Daga uwar ɗaka Saudat take fifita a hankali yanda goggon ba zata ji ba don ta hana ta amma zafin da ake kamar zai hallaka mutum har jaririn ma ƙurajen zafi sun dabaibaye masa jiki.
Ga sirkin da aka ciko ƙaton kofin silver dashi yana tururi, tabbas tasha wannan kam zaifi narka ta zaiyi har hanji.
Wutar da aka kawo ya haska ɗan madaidaicin tsakar gidan da yalon haske. Suhail da yaron huwaila suka saka shewar "nepaa" kana suka fara wawan abinci don su gama da sauri suje ɗakin Saudat kallo.
Ba'a daɗe da kawo wutan ba Kamal ya shigo sannan ya tsuguna a gaban mahaifiyar shi yana miƙa mata canjin Naira 300 "gashi sun karɓi dubu uku da ɗari bakwai da ƙyar don an ɗauki lokaci ba'a biya kuɗin ba shi yasa ma suka yanke.
Hannunta ta tsame daga cikin tuwon ta suɗe shi tass sannan ta zuba idon ta cikin na Kamal, Allah ya gani bata kunyar ɗan fari da kamal domin idan bata bashi kulawa ba waye zai bashi, tunda gashi ƴan uwan da ya kamata su ɗauki nauyin shi a ko wani ɓangare na rayuwa sun banzantar dashi.
Shekarun shi huɗu kenan da dawowa cikin garin Bauchi da iyalan shi a kan cewa Alhaji Kalabu zai sama mishi aiki amma bata san irin rayuwar da yake yi ba kenan, har ita ma idan damuwar ta ya tashi take turo mishi ƙorafin kuɗi kuma yayi ƙoƙarin mata ba tare da ƙorafi ba saidai a samu jinkiri, ashe ita ma ta fishi samu tunda ba aikin arziƙi aka sama mishi ba.
Gadin makaranta ce ta firamare ana bashi dubu ashirin a wata, a wannan zamani na tsadar rayuwa ga mata da ƴaƴa guda biyu yanzu sun zamo uku, ga mahaifiya da ƴan uwa masu bani-bani a ƙauye.
Hannun ta miƙa da nufin karɓan kuɗin tace "kace ma da kaje wurin Alhaji Tahir nawa ya baka?"
"Dubu ashirin" ya bata amsa.
"Babu komai zanje in same shi"
Ta sake mishi kuɗin sannan ta miƙe da nufin wanke hannun ta.
Duban shi ya mayar ga Amarya da bata rabuwa da murmushi a ɗan yamutsattsen fuskar ta, halin su ɗaya da goggo shi yasa tasu tazo ɗaya, don haka ganin ɓacin rai a fuskar ta yau ya ɗaga hankalin shi matuƙa.
"Amarya ki bata hakuri kada taje ta tayar musu da hankali don Allah"
Murmusawa tayi kaman damuwar shin ba komai bane tace "kada ka damu zuwa gobe zata huce, yanzu ka ƙaro wa mai jego sikari da canjin hannun ka".
Da toh ya amsa sannan ya miƙe, ya shiga ɗakin kwanan su duba Saudat kafin goggo ta dawo daga ban ɗaki.
Tana fifita ya riske ta ga gumi nata karyo mata don haka ya jefa mata tambayar, "yaya baku kunna fanka ba"
Ƙasa da murya tayi yanda na waje ba zai jisu ba tace "goggo tace sanyi zai kama yaro"
Jin sunan goggo yasa bai tanka zancen ba saima sauya akalar zancen da yayi. "Saudatu wani suna kika ga ya dace mu saka mishi?"
"Duk sunan da kake so ka saka bani da haufi a kan zaɓin ka"
Ɗan shiru yayi yana sosa ƙeya kafin yace "dama ni naso wai ko mu saka mishi Tahir ne tunda naga kaman shi bayi da takwara"
Nan da nan annurin fuskar Saudat yayi saurin ɗaukewa ta kuwa tamke shi tamau. "Wani irin Tahir kuma? Mu ke da alhakin mishi takwara saboda Allah?"
"Ai shiyasa na tambayi ra'ayin ki."
Ta san ba lallai zaɓin ta ya faranta ran kowa ba domin tafi son sunayen zamani ita, kaman na Suhail da aka bata zaɓi, toh yanzu ma in ta sake zaɓa surakanan ta zasu ga taso kanta don haka tace "toh a tambayi Goggo"
"Idan itama tace a saka Tahir ɗin kuma fa? Koma kalabu? Kinga ba zamu iya ja da ita ba gwanda ki zaɓa sai ince mata ra'ayi na ne."
Shiru tayi tana nazari kafin tace "toh a saka mishi Sabir."
"Shikkenan an gama amma zan shawarce ta a kan sunan kafin mu saka" gyaɗa kai tayi, ya saka hannu yana share ma yaron gumin da ya jiƙa farin powdern goshin shi. Yace "ɗan albarka baka da rikici"
Saudat ta karɓe da "gaskiya kam, saidai idan yaji yunwa ko barci amma ko zafin bayi damun shi sosai. akwai haƙuri kam yaci sunan shi haka muka yi da Yaseer ma, baba na ne mai rikici dai har yanzu."
"Allah ya raya mana shi da imani, ya kuma basu ingantaccen rayuwa baki ɗayan su" da ameen Saudat ta amsa sai ya ƙara da "baki buƙatar wani abu?"
"goggo ta sayi komai ni har kunya ma ta kama ni wallahi"
"Babu komai, haka iyaye suke koda mun hana su idan suna da halin yi sai sunyi mana, Allah dai ya bamu ikon kyautata mata muma" ta ƙara amsawa da ameen sannan ya miƙe.
Suhail na ganin zai fita ya maƙale dole ya fita dasu biyun zuwa shagon dake can bakin titi.
.....
Har yanzu goggo bata bar Mamakin yanda Yaseer ya iya komai a cikin gidan ba, yanda bayi barin su su ɗauki ko tsintsiya Idan dai yana nan.
Shi zaiyi shara, wanke-wanke, wanke ban ɗaki, ɗebo ruwa, wanki, yabi ya wanke yara harda na makwafta idan sun shigo bayi barin su su fita da dauɗa kuma ya shirya ya tafi makaranta da ya dawo yaci abinci ya wuce hadda ranar da babu ya tafi shagon ɗinki.
"Saudatu so kuke yi ku kar yaron nan ko?" Goggo ta shiga rikici bayan Yaseer yayi musu sallama ya fice, daman ita bata yiwa iyaye faɗa a gaban yaro don hakan ba a ko wani lokaci yake daidai ba.
Shiru Saudat tayi don bata da ta cewa, goggo ta ci gaba da zuba zance"kunyi mishi horo mai tsanani yaro bai san ya huta ba ko kaɗan? Ko mace kuke son maida shi ne iye?!"
Saudat dai tana shiru sai huwaila dake aza ice a ƙasan tunkyar wankan mai jego ne tace "wallahi Goggo ko kince ya bari bayi bari, haka nan yake da zafin nama jikin shi bayi son zaman banza, ga fannin karatu ma ba baya ba ance har monita ake bashi a boko a hadda kuwa idan baizo na ɗaya ba bayi wuce na biyu."
Goggo da Saudat suka saki murmushi a tare duk da ba kallon juna suke ba. Amarya dake daga uwar ɗaka tana wanke jaririn tace.
"Huwaila bar Halime kishi kawai take kada mijin yace yana son sabuwar amarya kwanan nan tunda girma da hankali sun zo"
Da haka suka ci gaba da hira cikin nishaɗi Saudat na saka musu baki jifa-jifa idan buƙatar hakan ta taso, yara kuwa duk an wuce boko Kamal ya tafi wurin aiki.
.....
"Baba kiyi haƙuri Alhajin bayi gida nace miki" mai gadin nan ne na gidan Alhaji Tahir.
Yanzu haka daga gidan Alhaji Salisu suke shima an hana su shiga wai Hajiya da Alhaji duk sun tafi aiki shine suka gangaro nan don fushi take da Alhaji Kalabu.
"Toh matar gidan fah? Ko itama bata gida?"
"Eh bata nan" ya amsa kai tsaye yana daɗa haɗe giran sama da na ƙasa.
"Mai jegon ne bata gida?" Sai yanzu kamal ya sako musu baki cikin zancen su. "Ko yau ma zaka ce baka gane ni bane?" Ya ƙara matsowa kusa dashi da confidence yau gashi da shaidar shi a tare da shi. "Wannan da kake ganin ta ƙanwar Uban mai gidan ne, don haka kafin yazo ka rasa aikin ka bata hanya ta wuce"
Ƙaramin tsaki yaja sannan ya bada izini aka buɗe musu ƙofar suka shige Kamal har wani boƙarewa yake kan shi yana mishi faɗi suka shige direct har parlourn Hajiya Fauziyya wanda Wannan shine shigan shi cikin gidan a karo na farko, duk cikin sauran ƴan iwan ma idan yaje gidajen su toh saidai ya jira a waje.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Mrs Imran ✨)*
*REINA 💍*