← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 57

Sashe 47

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ƙarasa shiga tana tura ciki, yayi saurin jawo mata kujera ya riƙe shi da kyau har saida ta zauna tana sakin ƙaramin nishi kafin ya sake.
ya dawo gabanta ya rusuna irin wanda Reina tayi a gaban shi da zata gaida shi kana shima ya gaida ta.

Ba zallan shekaru ya ƙara da tsayin ƙafa ba, harda kyawawan dabi'u da nagarta, shin tayi masa adalci idan ta zarge shi?.

Amma shi mugu bayi da kama.

Kawar da dubanta tayi daga kallon da take mishi, gashi ya koma gefe ya tsaya sai fara'a yake yi ko zama ya gagara.
ta maida hankalin ta tana duba tsaruwan wurin domin Alhaji Tahir ba ƙaramin shirya musu yayi ba, an saka musu kayan karatun yara sosai a wurin, ga calenders da aka maƙala na multiplication table, phonetics da sauran su, an maida shi kaman wani classroom.

Ganin shirun yayi yawa ya umarce su da su fara bitan AlQur'ani, Reina ta miƙe ta ɗauko ɗaya daga cikin wa'inda ke ajiye sannan suka fara ƙira'a cikin kananun muryoyin su masu daɗi, Hajiya Fauziyya ta ka kasa kunne tana sauraro.

"Aunty bari na kawo miki ruwa" yace da nufin shiga cikin gidan ya karɓo mata.

Saurin girgiza hannu tayi duk daɗi ya cika ta jin yanda muryar Reina har yafi na kowa tashi "A'a barshi, yanzu zan shiga cikin kawai nace bari na tsaya duba ku ne"

Sai ya ƙara murmushi Aunty akwai sanin ya kamata.
"Allah sarki"

"Toh yaya karatun? bata wani rashin jin dai ko?"

Yayi saurin girgiza kai "A'a wallahi, da sauƙi" gaba ɗaya ma ya rasa a ina zai saka kan shi, kwarjinin da Hajiya Fauziyya take mishi ko ita bata san tana da shi ba.

"Toh alhamdulillah, idan tana wani abun ma don Allah kada ka ɓoye min, zan hukunta ta yanda ya kamata"

Yayi tunanin barin abinda yake zargi a zuciyar shi har sai ya tabbatar amma sai yake ga kaman hakan bai dace ba, gwara ko ita ya faɗa mata tun da duk yanda ya damu da Reina yana da tabbacin mahaiyarta ta fishi damuwa da ita, idan ma binciken ne zata fishi tsaurarawa gashi bayi da cikakken iko a gidan.

Ɗan matsowa kusa da ita yayi yace "Aunty daman ina son mu ɗan yi wata magana idan babu damuwa"

Sosai ta bashi hankalin ta tare da gyaɗa masa kai "go ahead, ina sauraron ka" fatan ta ya kasance abinda take son ji shi yake son faɗa.

"Idan babu damuwa mu ɗan fita daga waje"

Wannan karon bata yi nauyin jiki ba ta miƙe ta fara gaba yana biye da ita a baya.

Gefe kaɗan suka koma tace "uhmm hmm, ina sauraron ka"

Sai yanzu kuma yaji maganar yayi mishi nauyi, ya haɗiyi miyau tare da ɗan ciza bakin shi.

"Kada kaji komai, koma menene idan ka faɗa min taimako na kayi. A kan Hafsatu ne ko?"

Ya gyaɗa kai a hankali sai ga ƙwalla sun fara taruwa a idanun ta, tana da tabbacin duk abinda zai fito daga bakin shi a yanzu sai ya tarwatsa zuciyar ta.

Saida ya sake haɗiyan miyau kafin ya fara magana "Zargi ne kawai, amma ina ganin kaman...."

"Ah ah, Fauziyya barka da zuwa. Shine kuma kika tsaya a waje?"

Hajiya Hauwa ta tunkaro su tana washe haƙwaran dole ganin hajiya Fauziyya a gidan su da sammako haka, ko lura da fitowar ta ma basu yi ba.

Sakwan biyar kawai, ji suka yi inama ace ta kara sakwan biyar kafin ta fito?!.

jinkirin sakwan biyar ya isheta taji komai ta yanke hukunci.

Jikirin sakwan biyar ya isa ya sauya rubutacciyar ƙaddara.

Jinkirin sakwan biyar ya isa ya tseratar da rayuka guda biyar.

"Zan jira idan kin fito" yace tare da juyawa ya koma wurin yaran tabi bayan shi da kallo.

Yanzu da anjima duk abu ɗaya ne. Ta ayyana a ranta sannan tayi ƙoƙarin sanya murmushin dole itama ma Hajiya Hauwa suka wuce ciki a tare.

Zama yayi ya fara musu ƙari, suka koma gefe suka ci gaba da bita. zai yi amfani da wannan daman ya tabbatar da zargin shi yanda zai faɗa ma Aunty abinda yake da tabbaci a kai.

Kiran Reina yayi ta ƙaraso gaban shi.
Hankalin shi a kan text book ɗin da yake koya musu saboda kada kallon cikin idanun shi ya sanya ta tsorata ta gagara fayyace mishi komai.

"Yaya jikin ki? Yayi sauƙi?" Ya tambaye ta.

"Eh, yanzu bani jin ciwo sosai"

"Masha Allah. Ƙurajen fa? Suma sun warke?" Yayi mata tambayar yanda zata fahimci ya riga da yasan komai ta saki jiki ta sanar dashi abinda yake son sani.

Da "Eh" kawai ta amsa lokaci ɗaya jikin ta na yin sanyi.

"Amma me ya saka miki ƙurajen?"

Yatsan ta takai baki ta saka farce a baki tana ci, alamun rashin gaskiya sun gama bayyana a tattare da ita. "Haka kawai fa ya fito"

"A'a Reina, ƙuraje basu fitowa mutum haka kawai har su kwantar dashi a asibiti, Ko wasan da kuke yi da Jamal ne ya saka miki?"

Suman tsaye tayi a wurin, ga idanun ta da suka firfito saboda tsoro kaman kace kyat ta zura a guje. Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta, suka yi ido huɗu, kuma bai taɓa ganin tashin hankali zunzurutun shi a cikin idanun ta ba kaman na yau.

Daman ya sani! Jamal ne!.

Ba ƙaramin yaƙi da zuciyar shi yayi ba ya sanya murmushi a kan fuskar shi domin tayi tunanin abun ba komai bane ya samu ya sha cikin ta.

Yaci gaba da cewa "ai ina ji wataran yana ce miki zaku yi wasa, shine ko?"

Sai kawai ta fashe da kuka tare da haɗe hannuwan ta cikin sigar roƙo.
"Don Allah yaya Yaseer kada ka faɗawa Aunty, wallahi yanka ni zata yi"

Lokaci ɗaya tafasan da zuciyar shi yake yi ya saka zufa fara yanko mishi duk da iska mai sanyi da yake kaɗawa.  Yana jin yanda tuƙuƙin baƙin ciki ya maƙure shi a wuya. Ji yake yi kaman ya shiga cikin gidan ya fito da ɗan akuyan yayi masa dukan shan gishiri.

Ganin su Zaheera suna wurin gashi ta rikice yasa yace "shikkenan, je kici gaba da karatun ki, ba zan faɗa mata ba"

Bata yarda ba tace "kayi alƙawari?"

Irin wannan alƙawarin bayi da tasiri don haka yace "nayi alƙawari"

"Toh kace wallahi"

Sai a yanzu ya bari ɓacin ran shi yazo cikin idanun shi ya watsa mata mugun kallon da ya sanya ta saurin juyawa ta koma ta zauna amma gabaki ɗaya ta rasa nutsuwar ta ko zama mai kyau ta gagara.

Shima kan shi ya rike yana jin yanda yake tsananin sara masa. Jamal yayi illa ma rayuwar Reina amma yana tsoron sanin girman shi, tun yaushe yake ta cutar ta babu wanda ya sani?. Yana taraddadin yanda mahaifiyar ta zata ɗauki abun.

"Yaya Yaseer"

Ya ɗago rinannun idanun shi ya zuba mata, "don Allah kayi haƙuri"

"Idan na haƙura zaki faɗa min abinda yake miki?" Da kyar ya samu muryar shi yake fitowa.

"Ba zaka duke ni ba ina?"

"Kin san kinyi ba daidai ba kenan"

"Wallahi ba zan sake ba, kaji na rantse. Idan na sake Allah ya ƙona ni a..."

Yayi saurin saka yatsa ya ɗane mata baki.

"Shikkenan, ba zan dake ki ba, labari kawai zamu yi.

"Toh I want to ease myself"

Shi a yanzu ko cikin gidan ma bayi son ta shiga, shima daga yau ba zai sake taka kafar shi a nan ba ko miliyan nawa za'a bashi, amma ganin a matse take tana haɗe cinyoyi yace "okay, na baki 5 minutes ki dawo"

Da sauri ta bar wurin yayi mata rakiyan idanu.

Babban parlour babu kowa don haka ta wuce toilet ɗin ɗakin baƙi kasancewar shi mafi kusa. 

Minti biyar, goma, har sha biyar Reina bata dawo ba.

Miƙewa yayi kai tsaye ya shiga gidan, hankalin shi bai kwanta ba duk da mahaifiyar ta tana cikin gidan, ko da ɗinma ai masu gidan suna nan amma ake cutar da ita.

Har yanzu parlorn babu kowa, sai ya rasa a ina zai fara duba ta ɗaya. Ƙofar ɗakin Jamal yaje yana kwanƙwasa shiru. ya tura ƙofar ya buɗe shi amma babu kowa, sai wani wari da yake fitowa daga ɗakin ga tarkace a saman gadon shi, kayan shi kuma barbaje a ƙasa.

Har zai fita ya hango kwalba daga gefen gadon shi don haka ya ƙarasa ciki yaje ya ɗauki kwalban, bai kai ga karanta abinda ke jiki ba warin abinda aka sha a cikin kwalban ya daki hancin shi. Yayi saurin ajiyewa yana riƙe hanci cikin kaɗuwa, bai taɓa ganin giya zahiril ayni ba amma yana da tabbacin wannan shine, Jamal har giya yake sha kuma a cikin gidan uban shi.

Ba zai iya ƙara second ɗaya cikin ɗakin ba don haka ya fito tare da rufo ƙofan. Ko babu komai yanzu hankalin shi ya ɗan kwanta ya san cewa Reina bata tare da Jamal.

Neman wuri yayi ya zauna yana jiran yaga giftawar wanda zai tambaye su inda ta shiga.
Ko kuma ya kira umman shi ta kira Hajiya Fauziyya ne ta tambaye ta idan suna tare? Domin ya gagara samun nutsuwa har yanzu.

Ciro wayan yayi daga aljihu zai danna kiran Saudat. Razanannen ƙaran da Reina ta sake ya karaɗe ilahirin gidan.

Miƙewa yayi tare da sakin wayan a ƙasa ya ɗiba a guje zuwa direction ɗin da ya jiyo sautin.

Ya bankaɗe ƙofar ɗakin da yake da yaƙinin daga wurin saurin ya fito, idanun shi basu sauƙa a kan kowa ba sai Reina dake zube a kan gadon ɗakin idanun ta a rufe bata motsi, sai kuma Jamal dake tsaye da saɓulallen wando yana ƙoƙarin gyarawa cikin tashin hankali.

"Wallahi ban mata komai ba! Duba ka gani ma"
Chapter 47 · 0% Book details