Sashe 28
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta san yaran ta ciki da bai, ta san gaskiyar su tana gane ƙaryar su.
Domin ta sadaukar da baki ɗaya nutsuwar ta wajen ganin ta basu kulawa yanda ya dace.
Ta koyawa kanta zama abin da suke buƙata ba tare da sun nima a wurin kowa ba balle taga ba daidai ba. Tana zama musu ƴar uwa a lokacin da suke buƙata, ta kan zame musu ƙawa, uwa, malama, majingina, abokiyar shawara, abokiyar cin mushe, wani lokaci har Matsayin uba ta kan ɗauka idan buƙatar hakan ta tashi.
Don haka bata da haufi a kan su duk da ana cewa ba'a shaidar ɗan yau, amma ba wai tabbaci take da shi a kan su ba, A'a. A kan tarbiyyar da ta ɗauki shekara da shekaru tana gina musu block bayan block take da tabbaci.
Sauƙe idanun ta tayi a cikin nashi ta maida hankalin ta kan abinda take yi tana faɗin "toh yaya aka yi ka bari suka yi faɗa a kan ka idan baka kula su?"
Ɓalle botir ɗin rigar ya shiga yi sannan ya cire ta ya juya bayan rigan ya gwada mata zanen heart ɗin nan, kana yace. "Ashe wai Time keeper ne ta rubuta wannan a jikin riga na, ni ban ma san sunan ta Yasmeen ba, shine ita kuma headgirl ta kama ta da faɗa saboda wai ashe tana yawo tana faɗa ma mutane ni saurayin ta ne, Saboda muna aikin makaranta tare sai aka yarda. Ni kuma Wallahi ba son ta nake yi ba"
"Toh me yasa baka son ta?" Ta tambaya don taji ra'ayin shi a kan soyayyar baki ɗaya sai ta san da wani irin kalamai zata yi amfani da su ta taushe shi.
"Haba Umma duka-duka shekaru na nawa? Yanzu kafin na gama karatu in samu aikin da zan iya Aure ai wannan tana da yara ma"
Ta murmusa "haka ne. Amma daga yanzu idan ka lura wata tana son ka kuma baka da ra'ayin kula ta, kayi ƙoƙari ka fahimtar da ita saboda kada ta sake yaga ma wata Hijabi" ta ƙarashe da raha, domin ta san abu mai sauƙi ne ya iya saka abun a ran shi ya dame shi.
"Toh Umma yaya za'a yi na gane idan wata tana so nan?"
Sake baki tayi don da iya gaskiyar shi yayi tambayar, lallai kamar yanda ya faɗa ne, nawa yake?. Ta kaaɗa baki tace "turƙashi, yanzu dai ku canza kaya ku ci abinci sai mu ƙarasa hirar anjima"
Miƙewa yayi da toh, ya ɗauki Sabir ya fara ɗauraye shi saboda ƙwallon da suka sha a makaranta ƙasa har kan shi, ya shirya shi ya zuba mishi abinci kafin ya shiga nashi shirin, Suhail kam yanzu ya iya kula da kan shi sosai.
......
"Sarauniyar Baban ta yau ma da ke anka zo office ɗin?" Alhaji Abdou ya miƙa ma Reina hannu su gaisa.
Hannayen ta da suka ɓaci da icing ɗin cake ta goge a gaban rigan ta Kafin Alhaji Tahir yayi yunƙurin zaro mata tissue, sannan ta riƙi hannun Alhaji Abdou tana girgizawa da iya ƙarfin ta kaman yanda taga kowa yake yi a nan ɗin, da taga bayi jijjiguwa mata ma sai ta saka hannu biyu.
"Ai kai ma naga office ɗin daddy na kazo" tace bata bar jijjiga hannun shin ba har sai da ya zare cikin dabara.
"Toh ai ni abokin shi ne" ya faɗa yana amsar file ɗin da Alhaji Tahir ɗin ya miƙo mishi don dubawa.
"Haba! Maman ku ne friends ko school ɗin ku ɗaya?" Ta daɗa matsowa gaban shi a kan makeken table ɗin da take har tana ture wasu takardu da kafar ta.
Bai samu daman amsa ta ba saboda abinda yake karantawa ya ɗauki hankalin shi.
"Tahir minana wannan?" Ya tambaya yana ɗan yamutsa fuska cikin ruɗu.
Murmushin kan fuskar shi Alhaji Tahir ya ƙara faɗaɗawa, abin dai da kake gani shine. Deal ne mai mugun kyau nake faɗa maka, riba za'a samu ba ɗan kaɗan ba"
"Riba? Da aka siyar da mene?" Ya ɗago yanzu yana duban sa.
"That's the best part. Baya buƙatar wani wahala da ɓata lokaci, funding kawai suke buƙata su yi projects ɗin da kake gani a wurin, kuma cikin wata uku za'a mayar mana da ninki ukun abunda muka bayar. Ko yaya ka gani? kawai kuɗi zamu zuba musu muma mu samu kuɗi"
Ya ajiye file ɗin a saman table ɗin sannan yayi baya ya jingina da kujeran da yake kai tare da jan dogon numfashi yana bin Alhaji Tahir ɗin da kallo.
"Yaya kake abu kaman ba ɗan kasuwa ba Tahir? Kaman yau ka fara kasuwanci? Kaman baka san rules na kuɗi ba? Babu wahalar da baka yi ba don ka tara abun da kake da shi a yanzu, kuma ko wani ma'aikaci a ƙarƙashin ko wani sassa na Tk Kingdom, albashin da ake biyan sa daidai aikin sa ne. Sai kai ne baka yi komai ba zaka yi tsammanin wasu daga sama su ɗauki zunzurutun kuɗi su baka haka siddan? Gaskiya idan barci kake yi kama farka"
Daman yayi tsammanin sai sun kai ruwa rana da shi kafin ya amince don haka bai damu ba ya jira shi saida ya dasa aya kafin yace "Abdou Hamissou ka gama?"
"Eh na gama Tahir Kamal Jama'are"
Tahir ya ɗan saki dariya kaɗan ganin har ya shaƙa.
Sai da ya ciro wayan shi ya shiga ma Reina kallo a YouTube Saboda ta fara damun shi, kafin ya matso ya ɗaura hannun shi saman teburin ya harɗe su guri guda tare da tattaro dukkan nutsuwar shi yace.
"Yau muka fara funding projects muna ribantuwa ne? Ko a tunanin ka bani zurfin bincike a kan abu ne da idan anso cuta na ba zan gane ba? Wallahi ba dan amanar dake tsakani na da kai ba da ko labarin anyi ma ba zaka ji ba. Shi yasa na jawo ka ciki don kai ma ka mori arziƙi."
"Zai iya zama funzy ne, ko kuma paper company, har wa'inda suka fika arziƙi da bunƙasa ma ana cutan su Tahir, ka bi a sannu kawai"
Sunkuyawa yayi ba buɗe drawer ya ciro wasu takardu ya ajiye ma Alhaji Abdou a gaban shi. "Gashi na tura har babban branch ɗin su dake China an duba min. Kuma ana kan bincika min manyan branches ɗin su dake Germany da Mexico. Kuma a nan Africa suke so su yi rabin project ɗin, kaga riba biyu kenan"
Ya ɗaga takardun ya duba su da kyau kafin ya ajiye "shikkenan, ka bari zan yi tunani kafin mu san abun yi"
Ya murmusa, "haka nake son ji. Hidima na samu ba wasa tunda shi muka fito yi"
Ya miƙe yana faɗin, "toh ni ina da wasu ayyukan a gaba na, zan ƙoƙarta in gama komai a cikin satin nan saboda Malika bata jin daɗi Wallahi"
"Allah sarki, jikin ne?" Ya tambaya cikin kulawa.
"Ka san da sanyi ya fara zuwa sai ciwon sun yayi ta tashi"
"Allah ya sawaƙe, amma ka gama tunani mu yanke shawara a kan wannan deal ɗin kafin ka tafin"
"In cha Allah " yace tare da miƙewa da niyyar tafiya. "Amma kaman nawa ne daman kake na niyyar zubawa?"
"200 million..."
Alaji Abdou ya gyaɗa kai alamun gamsuwa.
"...In Dollars!" Ya ƙarasa
"Mene?! Tahir Are you mad??!" Ya tambaya a kiɗime.
~~~~~~~
*Ayi maneji da wannan gobe zamu sake mai tsayi sosai in Allah ya yarda*
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
20.......Alhazai sun gama shiri saura tafiya, daga gidan Alhaji Tahir zasu wuce don haka masu tafiyan wanda suka haɗa da Hajiya Hauwa, Hajiya Jummai da yaran ta biyu, sai Kuma ita Hajiya Fauziyyar. Bayan su akwai Alhaji kalabu da matan shi duka uku sai kuma iyayen Hajiya Fauziyya da yayun ta dukkan su Alhaji Tahir ya biya musu, zasu haɗe a airport.
Shafa fuskar Maama dake hannun Hajiya Farida tayi ƙwalla na taruwa a idanun ta, bata ji irin abin da take ji a ranta yanzu ba lokacin da ta tafi ta bar Reina tana kamar ta. Sai take ji kaman bata yi wa yarinyar adalci ba, haƙurinta yayi yawa.
Sannan lokacin da ta bar Reina a wurin Ummi ta barta, tana da tabbacin zata samu cikakkiyar kulawa. duk da lokacin da ƙyar da suɗin goshi Alhaji Tahir ya yarda, shi dai sai dai a barwa ƴan uwan shi ita, sai da ta gwada mishi idan bai amince ba ta fasa tafiyan kuma a tare zasu je a lokacin kafin ya amince.
Hijabin jikin ta Reina ta ja, ta sauƙar da ganin ta zuwa kan yarinyar da tayi kamar zata fasa ihu.
"Aunty zan bi ki" tayi maganar cikin nuryar kuka.
Wani ɓangare na zuciyar ta na so yaji tausayin ta amma ta san yanzu sai ta yi mata ɓaci, don haka ta haɗe rai "Kin san Allah idan aka kira ni da complain ɗaya a kan ki Reina tun daga can zan sayi bulalar da zan shiga jikin ki da ita. Don haka ki nutsu, kina fitowa da assignment ɗin ki daga kin dawo daga school a taya ki ba sai da safe idan driver na jiran ki ba. Ki nutsu ki ci abinci kuma banda yawan kallo ko a TV ko a tab. Kuma in ji labarin kin roƙi wani cake kiga yanda zan yi da ke" ta ƙarashe muryar ta na sarƙewa don kuka ne yake so yazo mata.
Waye zai iya haƙuri da halin Reina ba tare da ta cika mishi ciki ba, kuma tana tsoron kada su mayar mata da agogon ƙoƙarin da ta fara yi a kanta baya, shi yasa da ace Alhaji Tahir wani ne toh da ma ƙanwar Ummi zata bada ita.
Hajiya lubabatu ne ta ƙaraso ta janyo Reina daga Jikin Hajiya Fauziyya.
"Ai da kunne na kika zo kika kama kike zuba min wannan kashedin Fauziyya, sai in daɗa ɗaukar su da muhimmanci don wannan maganar masu hankali ne ba na ƙaramar yarinya ba"
Ta shiga girgiza kai "A'a Wallahi Addah, yarinyar ne bata jin magana wallahi, ga shegen taurin kan tsiya, ina tsoron kada kisha wahala da ita."