Sashe 15
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wani ya hana ki cin abinci a gidan ki kafin ki fito? Abinci ma sai kalar da kika zaɓa?"
"Ni da zanci girkin Ummi kuma sai inci wani abun daban? Da yunwa na nazo na musamman don nayi kewar girkin Ummi na"
"Tuwo ne dai gashi nan miyan yauƙi ummin naki tayi" ta shiga zubawa Fauziyyan saboda tana son tatsar ta kafin ta tafi.
"Ina wa'innan ƴan cika kunnen suke?" Yaran Aina take nufi, su uku ne kuma kowa da uban shi, ɗaya a cikin su mutuwa yayi amma sauran biyun rabuwa suka yi kuma ta hana iyayen maza karɓan su gwamma ita tayi ta faɗi tashin yanda za'ayi, gwamma ma yanzu da Alhaji Tahir yake tallafa musu.
Bata yi rabi da cin tuwon ba sai sallamar Alhaji Tahir ɗin suka ji a ƙofar falon Ummi. Da farko ta ɗauka kunnen ta ne don haka ta share ta ci gaba da kai loma abinta don yanzu haihuwa ta buɗa cikin.
"Ba nace kada ki kashe min waya ba?" Yace cikin ƙasa da murya yana zama a gefen ta.
Ɗagowa tayi da lomar da bata kai ga taunawa ba ƙunshe a baki ta zuba mishi ido cike da mamaki.
*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*
```The Bleeding Rose 🌹 sneak peak```
_So now aside from the constant war between the North and the west kingdom there is a constant War between me and the queen and I'm not sure if it's stopping without any of us finishing another._
_If I take you with me you will also get involved in that war._
_So I want you to decide if you're going to continue staying here with my sister or if you are coming with me to the hellish Kingdom._
_However Farah, I won't promise to give you peace, I won't promise to give you love, I don't have any of it. but I promise I'll put my life on line to protect you, as long as you will serve and protect my mother. If you want this whole world I'll make sure to get it and place it at your feet, and no matter what will happen wether you're right or wrong I promise to be by your side._
_This is a promise I will never break. This is a promise from Namir to Farah. And this is a promise from a Husband to his wife."_
_By this time Gulping is all i can do. I feel like a shrimp comparing my struggle to giant sharks in the ocean. Whichever path Master Namir decides to follow the consequences will not only be for him but the millions citizens of North._
_"So you decide by tomorrow if you still want to go with me put off that lantern by your right side. And if you don't, I'll understand and leave after 10 seconds" he stood up._
_"I leave you in peace"_
*REINA 💍*
https://chat.whatsapp.com/JjjCOoAVsdP4PZbmCDrUOh
11....... Muƙut! Fauziyya ta haɗiye lomar tuwon bakin ta ba tare da ta tauna ba, idanun ta basu bar kan Alhaji Tahir ta ba, tana son tabbatar da kasancewar shi a wurin a daidai lokacin.
"Ina Reina?" Ya tambaya tare da yatsina fuska ganin kalar miyan da yake gaban ta, wanda yake da tabbacin ko da kuɗi aka bashi ba zai ci ba.
Saida Fauziyya ta haɗiyi miyau kafin ta iya cewa "Tana hannun Ummi a ciki" ta nuna hanyar ɗaki da hannun da ta saka a cikin miyar dan ta gwagwuyi ƙashi da kyau.
Miƙewa taga yayi tayi saurin tsare shi da "ina zaka je T?"
Juyowa yayi yana kallon ta sama da ƙasa, baki ɗaya ta yamutse bubun shaddar dake jikin ta, ga stain ɗin miya da aka goge daga wuyar rigan. fuskar ta duk tayi maiƙon yawo a rana domin da yake tambayar driver yanda ziyarar tasu yake kasancewa ya shaida masa cewa idan suka je gidajen da suke makwaftaka da juna ko kuma tazarar su babu nisa sai tace mishi ya jira ta taje da ƙafa ta dawo sai su ƙara gaba.
Kawar da wannan yayi a cikin ranshi tunda na yau ne kawai, amma kuma ta azabtar mishi da ƴa.
"Karɓo ta zanyi!" Ya juya da nufin ci gaba da tafiya ta miƙe da sauri tare da saka hannu bibbiyu ta riƙo shi.
"Ka rufa min asiri dan Allah, barci tayi aka kwantar da ita"
Yayi saurin ƙwace hannun shi amma ta riga ta shafa mishi miyar dama-dama.
Ya zaro napkin daga cikin aljihun jamfar shi ya shiga gogewa amma warin yajin daddawar har tsakar kanshi yake ji. Bai iya maida napkin ɗin aljihun shi ba ya ajiye mata a wurin.
Saida ya shinshina hannun yaji warin ya ɗan ragu saboda turaren dake jikin napkin ɗin kafin yace "A wannan zafin har zata iya barci mai daɗi Fauzah?" har wani fuskar tausayi taga ya yi.
"Akwai AC a ɗakin, kada kasa muji kunya Please"
Da mamaki yace "Duba lafiyar ɗiya ta shine abin kunya? Gidan ku ba gidan mu bane?"
"Gidan ku ne Amma Ummi surukar ka ce. Kayi haƙuri in wanke hannu in ɗauko maka ita."
Yaji daɗin hakan domin ya kawo mata ƙarshen cin tuwon don haka ya samu wuri a saman kujera mai zaman mutum uku ya hakimce. Hannun shi na dama ya miƙe a saman kan kujerar sannan yayi crossing legs ɗin shi yana jijjigawa a hankali cike da ƙasaita.
Hayaniyar yara suka fara jiyowa kafin suka shigo cikin ɗakin da gudu Aina na biye da su. "Toh Fauzee ga yaran naki da kike nima da boxing ɗin su suka shigo"
Idanun ta ne suka sauƙa a kan Alhaji Tahir bayan ƙamshin shi da ya cika ɗakin ya fara shiga cikin hancin ta. Shan jinin jikinta ta fara yi kafin ta kame kanta tsamm ta ƙarasa wurin da yake zaune ta zuba a ƙasa tana ɗiban gaisuwa.
"Lafiya Auntyn mu" ya amsa idanun shi na kan yaran da suka shigo da uniform ɗin boko suka zube a jikin Fauzar shi. Shikkenan za'a ƙarasa ɓata mata kayan! Yace a ranshi. Ita kuwa tana ta faman murmushi don tayi kewar su harda hayaniyar sun ma sosai.
"Toh kuje ku sauya kaya sai kuzo ku karɓi tsaraba" tace, da gudu kuwa suka miƙe suna rige-rige suka yi ciki.
Ganin Fauziyya na shirin miƙewa tare da tray ɗin abincin yasa Aina saurin tashi daga gaban Alhaji Tahir ta tare ta. "Haba dai mai jego, ki bari a fitar miki da kwanukan kaman yanda aka shigo miki da su mana" tace tana satar kallon Alhaji Tahir ɗin don taga yanayin shi.
Murmushi Fauziyya tayi son ƴar uwar tata na daɗa shiga ranta. Tabbas suna yawan rikici a baya duk da akwai Yayan ta namiji da Yaya Zeenat a tsakanin su, kuma yawanci Ainar ce take janyo wa Saboda bata kama girman ta gata da shiga abinda bai shafe ta ba. Sai kuma adawa da Fauziyya take yi da ita a kan yawon gidajen aure, wanda kusan kowanne ita ke jawo mutuwar su.
Amma tunda tayi aure komai ya sauya, daman ance idan ƴan uwan da suke da ƴar tsama a tsakanin su suka yi nesa da juna shaƙuwa takan shige su sosai.
Babu musu ta mika mata tray ɗin tare da faɗin "toh muje sai in wanke hannu na"
"hannun ma bari a kawo miki ruwa da Rubber ki wanke, kisha zaman ki kawai ƴar ƙanwata"
Saida ta dara tace "A'a barshi kawai muje, zan ɗauko Reina a bata magani ne kada mu ɓata mishi lokaci" tayi ƙarya don danne ko wani irin tunani da zai iya ziyartar zuciyoyin su a kan dalilin zuwan Alhaji Tahir din a wannan lokaci.
Suna fita Ummi na fitowa daga ciki.
"A'a Tahir, sannu da zuwa" tace murmushi shimfiɗe a saman fuskar ta.
Sauƙe hannu da ƙafar shi yayi tare da ɗan zamewa ya gaidata, don baki ɗaya cika masa idanu take yi.
"Ka biyo sawun mai sunar ne ko?" Tace tana son harbo jirgin shi.
Sosa ƙeya yayi a kunyace tare da faɗin "A'a Wallahi, daman Asibiti zamu kaita toh daa nace a bari sai gobe saboda ina da baƙi a office amma mun kammala meeting ɗin da wuri ma"
Jinjina kai Ummi tayi don babu wanda zai ji wannan dogon sharhi ya ƙaryata, duk da ita Fauziyyar bata faɗa mata wani magana makamancin haka ba.
"Gaskiya ne, kuma zuwa a kan lokacin shi yafi. Toh bari ta zo ku tafi amma kafin nan ka tsaya kaci tuwo mana"
Da sauri ya shiga girgiza kai tare da hannu. "A'a wallahi Ummi a ƙoshe nake alhamdulillahi"
"Ko dai baka cin tuwo Tahir?"
Dariyar ƙarfin yake ya saka yana faɗin "A'a wallahi Ummi cikakken bahaushe ne ni fah! ina ci, na ƙoshi ne kawai sai wani jiƙon in sha Allah" yana cin tuwo don tuwo, kalar miyan ne dai bayi ci.
Ita kuwa ummi murmushi kawai tayi tana tuna Alhaji Tahir ɗin a wani lokaci da ya shuɗe, a lokacin da yake da buri guda ɗaya kacal, tana da tabbacin a wannan lokacin koda kwatar ƙofar gidan su aka ce ya sha idan zai samu cikar wannan burin to tabbas zai sha, amma yau taga ƙyanƙyamin abincin su a kan fuskar shi.
Kafin Fauziyyar ma ta dawo taje ta ɗauko mishi Reina da kanta kuma babu kunya ya saka hannu ya karɓe ta.
Ta shigo tana tsantsame hannu sai karo tayi dashi yana jijjiga Reina da ta tashi yanzu a tsakar ɗaki ga Ummi a zaune ta zuba musu idanu. Kunya ne ta kama Fauziyya kamar mene duk da tasan Ummi bata da matsala samm amma zaƙewar na Tahir yayi yawa.
Saurin ƙarasawa tayi ta karɓe ta cikin ƙasa da murya yanda shi kaɗai zai ji tace "tunda ka ganta dan Allah kaje zamu dawo anjima"
"Toh asibitin fah?" Yace cikin buɗaɗiyar murya yanda Ummi zata ji ta saka baki.
Kallon shi tayi don ita bata san da zancen wani zuwa asibiti ba, kenan ɗaurawa yayi a kan ƙaryar da ta fara? Itama maganin ta.
"Toh ai baba bai dawo mun gaisa ba, baiga jaririyar ba ma" tace tana rau-rau da idanu.