← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 57

Sashe 43

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga ɗaya bangaren ya rintse idanu yana sauraron kukan nata, Fauziyya ta azabtar da su duka, Allah kaɗai ya san yanda aka yi ya iya jurewa har zuwa wannan lokacin ba tare da ya ji muryar ta ba. Da ita yake kwanciya yake tashi idan ma ya samu barcin kenan tunda yanzu abubuwa sun haɗe masa goma da ashirin ga yanda baki ɗaya rayuwar take ƙara rikice masa idan bata tare da shi.

"likita yana zuwa duba ki ina? Kuma kin fara zuwa asibiti?" Ya tambaya don tabbatarwa duk da yana bin diddigin halin da take ciki.

Gyaɗa kai tayi kaman yana ganin ta kafin tace "T ina yara na? Ina ka kai Maama?"

"Ba zaki tambayi Reina ba ko? Ita kullum sai ta tambaye ki"

Hannu ta saka ta share hawayen fuskar ta tace "Na san kulawar da Reina zata samu ko a bayan idanu na yana da yawa, amma Zainab baiwar Allah T, bata ma iya buɗe baki ta faɗi abinda take so balle wanda bata so, sai ni kawai da na san buƙatun ta zan iya kula da ita"

Dariyar da bata haɗe da nishaɗi ya sake, dama ya san saƙon da ta turo mishi trick ne saboda ta samu ya kula ta. "Fauzah wato ba zaki taɓa sauya zani ba ko? Ashe baki ɗauki darasi a abun da ya faru ba? Hmm. Tunda haka ne ba matsala zan cigaba da kula da yarana duka, kowa zan yi mata abinda take so babu bambanci. Kuma ki sani Idan kin haihu kin yaye abinda kika haifa zan karɓi abuna in nima musu wata uwar da zata fiki son su"

Zamowa tayi daga kujerar ta samu wuri a ƙasa ta zauna daɓas, cikin muryar kaɗuwa tace "Mai kake nufi T??"

"Ina nufin aure zan ƙara kwanan nan, ba zamu ƙare ni da yara a tsakanin gidaje ba kullum a tagayyare ba. And for your information Maama tana Nijar, na bada ita ma Alaji Abdou"

Ya san shikkenan ya ƙare mata tanadi don haka ya datse kiran ba tare da ya saurari kururuwar da ta fara kaman zautacciya ba, kuma yana da tabbacin zancen kishiyar da yayi mata bai kiɗima ta kaman zancen kasancewar Maama a Nijar ba.

Abinda bata sani ba kuwa Rabon shi da Alaji Abdou tun fara rikicewar lamarin nan, gashi yanzu ya fara shiga tsaka mai wuya babu abokin shawara balle mai taimako, yana daga cikin dalilin da ya saka bai nemi sasantawa da Fauziyya ba don bayi son sai ta dawo kuma ya saka mata wani damuwar ga ciki.

Bai gama tunani ba aka yi knocking sau biyu tare da turo ƙofar a lokaci guda.

Hajiya Jummai ne ta shigo sai Maama biye da ita, da ɗan gudunta ta ƙaraso ta faɗa a jikin mahaifinta.
Shima rungumar ta yayi yana shafa bayan ta a hankali "gimbiya ta makarantar ne?"

Cigaba da riƙe shi tayi bata ɗago ba sai ya saka hannu ya tallafo fuskar ta da yanzu ya jiƙe sharƙaf da hawaye.

"Yaya Jummai don Allah jira mu a waje" yace don ya san ba zata iya ce komai a gabanta ba.

Lokaci ɗaya ta fara rantse-rantse domin ta san babu abinda zai hana Maama faɗa mishi abinda yake faruwa a yau dukda lallashin ta da ta gama yi, ta kawo ta wurin mahaifinta kaman yanda ta buƙata da sharaɗin ba zata yi masa kuka ba.

"Wallahi Tahir ban sani ba! Amma yanzu ma na ɗauki mataki na hukunta su sosai kuma duk saida suka bata haƙuri. Faɗa ne kawai irin na yara, ka san su da rashin hankali wai suna rama abinda Reina tayi musu a kanta" ta fallasa kanta da kanta domin ta san itama yau ta ƙare mata kaman dai Hajiya lubabatu wanda ko ga maciji yanzu bayi haɗa ta da Tahir.

Bayi son ya rikice a office yayi mata abinda zata sha mamaki, idanun shi a kan gefen collar farar rigar Maama da fatar wurin ya tara jini yace "A shigo min da school bag ɗinta kawai ki wuce gida, na gode da riƙon amana"

Zata ƙara magana ya ɗaga mata hannu "don Allah ki tafi"

Haka ta mayar da bakin ta rufe sannan ta juya cikin tashin hankali ta bar office ɗin.

Tana rufo ƙofar ya shiga ɓalle botiran rigan Maama sannan ya cire yana kallon jikin ta harda tabon cizo a damtsen ta. "Tun yaushe suke miki haka?"

Shiru tayi daga farko kaman ba zata amsa ba sai kuma tace "Idan.... idan muka je school ne sai su duke ni su saka friends ɗin su duka na wai ai Reina tana dukan yayun su suma. Ko kuma idan tayi musu wani abu sai su rama a kai na, har lunch ɗina suke ƙwacewa kuma ko a gida sai su kai abinci na ma kare idan Hajiya bata kusa"

"Kin faɗa ma teacher ɗin ku?" Ya tambaya cike da tausayin ta.

Ta gyaɗa kai "na faɗa mata ta saka su kneel down da picking amma basu daina ba"

"Ita Hajiyan fa? Kin faɗa mata?"

Sai ta girgiza gai wasu sabbin hawayen na zubo mata "Ina tsoro"

Ya sake kallon yanda ta ƙara ramewa ta lalace daman ita ba mai jiki bane kaman sarauniyar shi.

"Zan ɗauki tsatstsaurar mataki my princess, kada ki damu"

A ranar su biyu suka kwana a ɓangaren shi, daɗin ta ma Aina'u tana nan don haka ita ta shirya masa ita ta bata abinci da kan shi ya kaita makarantar zuwa ofishin principal, yaje ya sauƙe musu buhun bala'i.

Har ƙasa saida principal ɗin ya kai yana bashi hakuri domin cewa yayi zai cire Maama da Reina a makarantar. Gwanda ma Maama da take zuwan baya amma Reina da kuɗin makarantar ta aka kammala ginin makarantar, saboda lokacin ɗoki ya saka Alhaji Tahir biyan school fees ɗinta baki ɗaya tun daga farko har ta gama secondary.

Kuɗin uniform, abinci da litattafai duk ya biya a dunƙule saboda zumuɗi domin tsarin makarantar yayi mishi, kaman na ƙasashen waje.

Da ƙyar manyan makarantar suka taru suka taushe shi, har mai makarantar sai da ya zo ya saka baki. Kafin suka daidaita a kan bawa sauran yaran suspension na sati biyu sannan idan zasu dawo sai sunzo da iyayen su dukda shi korar su yaso ayi harda yaran ƴan uwan shi duka, daga ƙarshe dai ya cire Maama a makarantar ya bar musu Reinan tunda ita kam da bakin ta.

Haka dai ya tafi ya bar su da Mamakin shi nashi ƴar tana jibgar yaran jama'a ta kwana lafiya, a haɗu a rufe maganar, amma an taɓa ƴar uwar ta ya ɗaga musu hankali.

......

Yau Yaseer ya samu kuɗin da yake jira daga wurin iyayen Jamal don haka ya biya kuɗin hostel ɗin da an riga an kama mishi, sannan ya fara shirin tarewa a can sai dai dole zai dinga dawowa ko wani weekend don zuwa koyar da Jamal da su Reina.

Ya karɓo sabbin ɗinkunan shi, Umma ta taya shi haɗa kayan yanzu gobe daga yayi wanka ya karya zai wuce.

A sauran kuɗin ya cire har dubu ashirin pocket money sannan ya ɗauki ragowar ya damƙa ma umman shi da take ta kalen inhaler alamun ya ƙare.

"Umma gashi a sake siyan numfashi" ya saka mata kuɗin a cikin tafin hannu.

Ɗayan hannun ta a kan ƙirji tana ƙoƙarin daidaita numfashin ta da tarin da tayi Saboda ƙuran waken da take gyara mishi ya saka shi hawa, ta ɗago hannun tayi mishi danƙwale kafin ta mayar da shi kan ƙirjin.

Murya a shaƙe tace "ka ajiye kayan ka, ina da kuɗin siyan wani"

"Nima akwai kuɗi a wuri na, kawai ki riƙe" ya ajiye mata kuɗin a kan cinyar ta.

"Ba zaka yi ma kanka tanadi bane? Sai kashe kuɗi kawai Yaseer? Kaga bamu san mai gobe zata haifar ba, ya kamata ace kana da wani shiri idan wanda kake da shi a yanzu bai ɓulle ba. Idan kana ajiye wani abu duk wata zaka tara jari mai yawa zuwa ka gama karatun ka kaga sai ka kama sana'a mai gwaɓi"

"Umma Alhaji Tahir fa yayi min alƙawarin aiki idan na gama" yace don yaji bakin ta tare da karɓan tray ɗin daga hannun ta yaci gaba da gyaran yana ɓoye dariyar shi.

"Kaci gidan ku! Alƙawarin Alhaji Tahir alƙawarin Allah ne? Ko baka ga abinda ya faru da mahaifin ka bane? Ashe baka ɗaukan darasin rayuwa daga kuskuren wasu?"

Dariya kawai ya sake yi saboda daman tsokana ce, ya sauya hirar da "Umma yanzu ace da wata rana zan yi kuɗi mai kike so inyi miki?"

Sauƙe numfashi tayi tace "ni idan ka kaini ɗakin Allah ka gama min komai Yaseer, ya Allah ka kira mu"

Da "ameen" ya amsa kana ya ɗaura da "in Sha Allah toh Umma Hajji duk shekara Umrah duk sati idan nayi kuɗi"

Darawa tayi tace "toh Idan haka ne ai sai ka nima min gida a can kawai in tare"

"Shawara mai kyau, hakan ma kawai za'a yi. Idan baki son Abbah ma yana damun ki sai shi in bar shi a nan in gina mishi makeken gida in bar shi yana hutawa kawai ya dawo Alhajin parlor har sai kin buƙati ganin shi"

Shi karan kan shi saida ya dara jin abinda ya faɗa tace "kana magana Kaman Irfan wallahi, shi yace ma wai jirgi baki ɗaya zai siya mu koma rayuwa a sararin samaniya"

"Tashin hankali, ashe namu burin kaɗan ne"

Sai da suka tsagaita dariya yace "amma da gaske Umma da ace Allah zai wadata ni ya bani dama kinga matasa masu zaman hakan nan?! Sai na tattare mana su duka a Nigeria an dawo babu mai zaman banza. amma bari kiga ma ba sai an je da nisa ba yaran da suke zube a unguwar nan kaman kiyashi, babu boko islamiyya sai ɗaɗɗai ɗin nan kwanan nan duk zan biya musu PTA in ɗinka musu uniform in kai ƴan ƙaniya makaranta, suna nan sai aikin cika mana kunne da zubar wa mutum aji a unguwa"

"Allah ya taimaka ya ida nufi"

Ya amsa da "ameen" suka ci gaba da hira har aka kira sallan maghriba sannan ya tattari ƙannen shi suka wuce karatun dare da suke ɗauka a masallacin unguwa.

...
Chapter 43 · 0% Book details