← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 57

Sashe 51

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamal ya bari har sai da ya tabbatar da ya fara dawowa cikin hayyacin shi kafin yayi masa tambayar ya labarta musu ainihin abinda ya faru, yanda aka yi aka haihu a ragaya.

"..... Allah da bakinta ta amsa min. Jamal ne, Yaron gidan da nake zuwa in yi mishi lesson, kuma a tambayi Aunty mahaifiyar ta, na fara mata zancen mahaifiyar Jamal ɗin ta fito ta katse mu, ko ita Hafsatun ma a tambaye ta"

Kamal ya numfasa "Shikkenan, ni bari na je gidan Alhaji Tahir ɗin goggo, in same shi ko ita Hajiyar ma idan bayi gida, idan abu ya gagara kuma sai ki zo amma bamu fatan hakan"

Babu daɗewa suka sake tasa ƙeyar Yaseer zuwa ciki, kamal ya bada kuɗin magani da kuma dressing ɗin ciwon Yaseer ya dinga haɗa su da Allah su taimaka, dukkan su ƴan uwa ne kuskuren fahimta aka samu sai dai zasu warware komai nan ba da jimawa ba.

Sun dai ji shi, amma suna tafiya suka raba kuɗin a tsakanin su.

Kamal ya fara saka goggo da Saudat a napep su tafi gida kafin ya tsari mashin ya ɗauki hanyar gidan Alhaji Tahir, ya riski unguwar ma gabaki ɗaya bata shiguwa da abun hawa.

......

Da ƙyar Alhaji Abdou ya lallaɓa Alhaji Tahir ya ɗauro alwala ya fito, yana tafiya kaman zai kifa.

yana fitowa yawan mutanen da ya gani ya saka shi sake rushewa da kuka, Ciki da wajen gidan ya cika maƙil.
Dandazon mutanen da ya gani sun zo su sallace Fauziyya ya ƙara narkar da zuciya da ruhin shi, karkarwa yake yi a yayin da ake yin ƙabbara ma Ubangiji a Saboda wa'innan halittu guda biyu da ya busa musu rai a lokacin da yaso kuma ya ɗauki ɗayan ba tare da ya shaƙi iskar duniya ba ma.

A cikin ƙanƙanin lokaci har sun kasance kamar ba'a yi ba, sun dawo tarihin da idan Reina ko Maama suka shiga halin maraici za'a kalle su ace 'Allah Sarki, Allah ya jiƙar mahaifiyar ku da ta rasu yayin haihuwa'.

.....
Gidan Hajiya Hauwa Meesha taje duba Yaseer.
Tun jiya take niman layin shi a kashe baki ɗaya ta gagara samun nutsuwa, gashi tana jin kunya da kuma tsoron zuwa gidan su, kada ya ƙara fushi da ita a kan wanda yake yi yanzu.

Tana da yaƙini koma tace tabbacin zai zo yiwa Jamal lesson yau kasancewar shi lahadi. Saidai da isar ta aka sanar da ita gaba ɗaya masu gidan basu nan sun tafi gidan ƙanin mai gidan anyi rasuwa.

Tunanin ko ta kira Hajiya Hauwa ta tambaye ta Yaseer ya faɗo mata, amma ta lura itama ba son tarayyar su take yi ba tunda gashi ta fara kai gulma wurin iyayen ta.

Toh ko taje gidan rasuwar ne ta tambayi Jamal ɗalibin shi?.

"Umm mai gadi nace Yaseer fa? Ya zo yau ɗin?"

Mutane da son gurmi wanda ba shi aka tambaya ba ya riƙe baki, "wani Yaseer ɗin? Yaron da yake zuwa laluɓe ƴar masu gida? Ai tuni ƴan audu suka zo suka yi waje da shi" da safiyar yau ya ji raɗeraɗin abinda yake faruwa shine shima yake son ayi da shi.

Yatsina fuska Meesha tayi cikin rashin fahimta tace "I don't understand, come again "

Ɗayan na ɗan tattaɓa shi don ya iya bakin sa amma ya share yace.
"Hajjaju! shi dai Yaseer abokin ki da yake zuwa yi ma yara karatu..."

"Uhm hmm?"

"Toh ashe zagawa yake yi yana laluɓe Hafsatu Rayina ƴar gidan Alhaji Tahir. Shine dubun shi ya cika Allah ya kama shi uban ya kama shi da idon shi"

"Reina dai?!" Meesha ta maimaita da mamaki ganin to ko iskanci Yaseer yaso yi me zai yi da wata Reina jaririyar da ko ƙirgen dangi da sauran ta?.

Amma shi sai ya ɗauka sunan da bai faɗa daidai bane take gyara mishi.

Yace "Ita dai" kana ya ɗaura da "ai ina faɗa miki Hajjaju mutane kina ganin su nan maha'inta ne ƴan kutumar kaza. Ki ɗauko mutum a bushe ana bashi maiƙo har ya fara tada komaɗa yana tafiya da dogon wuya zoƙai-zoƙai kaman jalbe amma shine duk cikin yaran duniya ya rasa wa zai taɓa sai ƴar alhajin Alhazawa..."

Zai ci gaba da magana Meesha ta gwada shi da yatsa "in sha Allah duk ranar da na dawo cikin gidan nan ka bar aiki. Wani station aka kai shi?"

A tsorace ya durƙusa yana ɗaga mata hannu kaman mai bara "dan girman Allah hajjaju a yafe ni, Wallahi suɓul da baka ne, bakin ne ba'a farsa shi ba tun haihuwa"

Reverse tayi zata bar ƙofar gidan ɗaya mai gadin ya faɗa mata address ɗin wurin gudun kada idan tazo tattarawa shima ta saka a haɗa da shi.

.....

Meesha bata yi musu kama da wanda zasu hana ta ganin Yaseer ba duk da suna tsoron Alhaji Tahir kuwa.

Yana fitowa yaga ita ce ya juya zai koma, bai san kuma wata jarabar zata ƙara mishi ba yanzu, ta bar shi ya ji da abu ɗaya.

Da gudu ta ƙarasa ta riƙo hannun shi amma saboda raunin shi ya saki ɗan ƙara sai a lokacin ta matsa baya ta ƙare masa kallo da kyau.

"Yanzu shi Alhaji Tahir ɗin ne yayi maka haka? Wallahi ko duk duniya zasu taru a kai na ba zan taɓa yarda da sharrin da suke son ƙulla maka ba, kai ba mutumin banza bane"

Wasa-wasa kukan da Meesha tayi sai da ya kusa zarce na mahaifiyar shi ma. Aka dawo shine mai rarrashi da bada baki su kuma suka fita siyo mata ruwan gora mai sanyi saboda sun ganta da mota, gashi kana kallon ta kaga rich kid.

Da ƙyar ta bar station ɗin zuwa tunkarar Hajiya Hauwa a gidan mutuwa. Ita ta ɗauke shi aiki don haka ita ya kamata ta tsaya mishi tun da su suke morar shi.

.....

Yau ne gobe ne kamal zai dawo shiru. Har rana ya fara sanyi yana zaune cikin ƴan karɓar gaisuwa. Da goggo taji shirun yayi yawa ta kira shi don jin ba'asi ya sanar da ita ai Hajiya Fauziyya ce ta rasu sai ta ƙarfafa masa guiwar ya jinkirta da maganar suma gasu a hanya, don bata jin zata taɓa mantawa da kirki da kuma halaccin Fauziyya ɗiyar albarka.

~~~~~~~~~~~~

Idan Allah ya bamu aron rai, littafi na biyu zai zo paid ne. 500 posting document kuma 1000, Zaku iya fara payment yanzu ko zuwa lokacin da muka kammala littafi na ɗaya.
8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay
Sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

https://chat.whatsapp.com/Dn6MNAK5vgX3kRbwKwAPCv

37......A bakin hanya Meesha ta samu tayi parking, ganin yawan mutanen da ke sintiri a gidan ya saka ta ɗauki sunglasses ta ƙwama saboda idanun ta da suka kumbura a dalilin kuka.

Da ƙyar ta samu wucewa cikin parlourn dake cike maƙil da mutane, bata fasa kiran Hajiya Hauwa a waya ba ita kuma ta ƙi ɗauka.
Glasses ɗin ta cire ta fara baza idanu ko zata ga wanda ta sani ta tambaye su inda take yanzu su wuce police station ɗin, don tana ji kaman idan Yaseer ya ƙara awa guda a cell zata iya haukacewa.

Can ta hango Zahra ta maƙale a wata ƴar kwana tana danne-danne a cikin wayar ta. Babu ɓata lokaci ta ƙarasa wurin tare da ɗan shurin ta da ƙafa ta ɗago.

"Ke ina maman ki?" Ta tambaya.

Sai Zahra ta fara dube-dube, ita kaman ma tun kafin karyawan safe rabon ta da ita.
"Ban san inda take ba" ta bata amsa.

"Oya tashi kije ki dubo min ita, and ki hanzarta"

"Ni Wallahi ban san a ina zan same ta cikin wannan taron ba. Kije ki duba ta da kan ki"

A masife Meesha da ta manta a gidan mutuwa take tace "zaki je ki kira ta ne ko sai ɓaɓɓallaki mara kunyar banza?"

Nan hankalin mutane ya dawo kan ta.

"Lafiya dai Meesha?" Hajiya Farida ta tambaya.

Juyawar da zata yi taga duk idanun mutanen parlourn ya dawo kan ta.

"Aunty Hauwa nake nima, ko kin san yanda take?"

"Gani. Mai zaki bani kike nima na?"

"Aunty Hauwa kin ci amana Wallahi " ta juya tana kallon Umman Jamal da yanzu shigowar ta gidan sun raka Jamal airport kuma basu bar airport ba sai da suka ga tashin jirgin su.

hawaye na sake taruwa a idanun Meesha ta cigaba da cewa. "Kin ɗauko ɗan mutane zai taimaka muku shine zaki bari ayi masa wannan wulaƙancin? Yaseer ɗin da ko kallo ban ishe shi ba mai zai yi da wata Reina don Allah?"

Lokaci ɗaya hankalin Hajiya Hauwa ya ƙara tashi, kada Meesha ta since mata zani a gidan mutuwa. Mutane kuwa an zuba kunnuwa aji gulma har masu jan tasbaha suna lazimi ma dakatawa suka yi su ji rikicin duniya tukunna. Sai wata wata mai tunani ne aka samu ta tunasar da su cewa a gidan mutuwa suke.

Meesha bata da niyyar fasa magana don haka ta karasa kusa da Hajiya Hauwa ta riƙo hannun ta tare da sauƙe murya iya tsakanin su "Aunty Hauwa, don Allah ki taimaka ki yi magana a fito da shi. Wallahi yana shan wahala sosai, kuma na tabbata ba shi bane, sharri aka yi mishi"

Hajiya Hauwa ta buɗe baki zata mayar da raddi suka jiyo hayaniya a waje. Alhaji Tahir da bayi iya buɗe baki ya amsa gaisuwa amma muryar shi har cikin gidan yana hayagaga ma wasu.

Yanda kasan yara sun ji ana sadaka haka matan cikin parlon nan suka rige-rigen fita su ga abinda ke faruwa.

......

Mutuwa ce, mutuwar ma na mace kamar Hajiya Fauziyya, matar kirki gaba da bai wanda babu fatan da zasu yi mata da yayi ƙasa da Allah yayi mata rahama, ya kai haske makwancin ta.
Amma zuciyar uwa, Saudat ji take yi da wata ce ba zata je ba bayan Abinda suka yi ma gudan jinin ta.

Muhammad abokin Yaseer ya kira Kamal lokacin su goggo suna hanya ya bashi haƙurin sammakon zuwa lectures yayi shiyasa bai kira ba tuntuni, sannan ya tambaye shi an ga Yaseer ɗin? Tunda ya san ba halin shi bane fashin makaranta. department ɗin su ba ɗaya ba amma ɗakin su ɗaya kuma bai ga ya dawo ba.
Chapter 51 · 0% Book details