← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 57

Sashe 49

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Fauziyya har dare ya raba suna abu ɗaya, ga jinin ta yayi mummunan hawa, tsoron buɗe ta likitoci suke ji domin za'a iya ɗaya babu idan ba duka biyu ba.

Karshe sai da suka gayyato wani babban likita yazo daga Abuja kafin suka shiga da ita tiyata.

......

Kasancewar a weekends kafin maghriba ko bayan ta Yaseer yake dawowa gida ya saka hankalin Saudat tashi matuƙa.
Gashi bai kira ya faɗi uzurin shi ba don haka ta fara niman shi a waya sai dai kalma ɗaya matar cikin na'urar take maimaita mata, 'the number you have dialled is switched off.'

Gashi Kamal ya tafi mata sari Jama'are da ganin gida sai yammacin Lahadi zai dawo.

Kiran shi tayi ta sanar dashi fa Yaseer bai dawo gida ba har yanzu kuma wayar shi a kashe. Yace ta kwantar da hankalin ta wataƙil ya bi wani wurin ne kuma wayan ba caji, amma zuwa tara idan bai dawo ba ta sanar da shi zai kira abokinsa ya tambaya.

Haka lokaci ya dinga tafiyar saiɓi bata kuma fasa kiran wayan Yaseer ba, tun takwas da rabi ta sake kiran Kamal domin hankalin ta sam ya gagara kwanciya tunda bai taɓa irin hakan ba.

Kamal ya kira Muhammad ya tabbatar masa rabon shi da Yaseer tun safiyar juma'a kuma shikam ma yana hostel amma zai binkica sauran course mates ɗin shi yaji.

Har goma da rabi ta wuce babu wani labari lokacin hankalin kowa a gidan ya gama tashi har na Kamal da bayi nan. Kuma azancin kiran gidan Alhaji Salisu bai zo mishi ba sai daga baya.

Ƙarfe sha ɗaya da minti talatin da shida Saudat ta sake danƙara ma Kamal kira a karo na babu adadi.
Bai ɗauka ba har saida ya kusan tsinkewa saboda bai san me zai faɗa mata ba.

Masu gadin gidan Alhaji Salisu basu ɓoye mishi ba suka sanar dashi Yaseer yana police station Alhaji Tahir ya saka an rufe shi a cell, amma ko suma basu san me yayi ba.

Ɗaukan kiran Saudat ɗin yayi kafin ya tsinke, ya daidaita muryar shi yace "Saudatu mun yi magana dashi yana lafiya, wai assignment ɗin su ne a makarantar za'a karɓa da gaggawa shine ya tafi can don ya samu ya ƙarasa nashi kuma wayan shi ba caji. Yanzu kiyi hakuri ki kwanta ki huta nima gobe da sassafe ina hanya"

Ta yarda da abinda yace don haka ta samu nutsuwa tayi barci. Su kuwa a cikin daren goggo ta saka aka ɗago wani maƙwafcin su direba suka kamo hanya.

.....

Tun kafin a fara ma Hajiya Fauziyya tiyata suka tabbatar da babu rai a jikin abun cikin ta daman bakwaini ne kuma babu lafiya don haka babu yaƙini, amma duk yanda suka yi ƙoƙarin su ceto nata rayuwar abu ya gagara.

~~~~~~~~~

Ga rayuka huɗu a cikin garari, wanne ne cikon na biyar?

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

35......da ace a halin yanzu za'a samu wanda zai yi gigin yiwa Alhaji tambayar tsakanin Fauziyya da Reina wa yafi so, to wannan mutumin ba zai bar ƙofar ɗakin tiyatar nan da ƙafafuwar sa ba.

Zama mai kyau ya gagare shi, yayi gaba yayi baya sai kuma ya sake gyara zama. Hannayen sa da ya dunƙule a saman cinyoyin shi sai karkarwa suke, yana jin kaman ya ƙalubalanci ƙaddara; me yasa idan zata zo ma ɗan adam sai ta taro muƙarraban ta? Ita kaɗai ma ai ta wadata ta danne mutum har sai ya ji kaman numfashin sa zai ɗauke.

Idon shi ya ɗaga ya kalli mahaifiyar ta dake zaune da tasbhaha a hannu, bata fasa goge hawayen da ya ɗauki awanni yana sintiri a kan fuskar ta da ɗan hankici ba. Wai itama kenan mai wasu yaran da yawa kuma ga mahaifin su a tare da ita bai gaji da lallashi ba amma shi fa? Babu wani wuri da zai dafa ya ji sanyi a halin yanzu.

"Tahir"

A hankali ya ɗago rinannun idanun shi ya zuba su ma Hajiya Hauwa.

Taci gaba da cewa "Bari naje na duba Reina ko ta farka"

Jinjina kai kawai yayi saboda shima yana so ya ji halin da take ciki. Ita kuwa a nata bangaren tsoron Reina ta farka ta faɗa ma wani ainihin abinda ya faru take yi, idan hakan ya faru komai ya lalace.

Gwanda taje ta gargaɗe ta, domin a halin yanzu ƙoƙarin nima wa Jamal visa aka shiga yi faka-faka, koda ace ba na ƙasar da suka so ya tafi ɗin ba idan an samu student visa ko na Sudan ne sai ya tafi tunda shi ya jawo ma kan shi.

Murɗa ƙofar VIP room ɗin tayi ta shiga.
Reina na kwance har yanzu da oxygen mask a kan fuskar ta. Hajiya hauwa ba zata iya jira sai ta farka da kanta ba don haka ta karasa gaban gadon ta jawo kujera ta zauna ta shiga bubbugata ta tashi.

Da ƙyar ta iya buɗe nannauyan idanun ta, tabi ta lumshe su. cikin muryar kukar da ta suma da shi tace "yaya Jamal... ka yi haƙuri bana so.."

Zata cigaba da kukan Hajiya Hauwa ta miƙe tsaye ta miƙar da ita ta zaunar, tare da cire mata oxygen mask. lokaci ɗaya Reina ta watstsake ganin yanda ta zaro mata idanu kaman zata ɗauki ran ta.

"Umman Jamal, kinga shine yake cire min wand..."

Bata san lokacin da ta shaƙo wuyar ta ba, tare da ɗaura yatsar ta a saman baki alamun tayi shiru.

"Ba yace idan kika faɗa zaki mutu ba? Kin ɗauka ƙarya ne?"

Idanun Reina zuru-zuru ta shiga girgiza kai da ƙyar tana ƙaƙari, ganin haka Hajiya Hauwa ta sake ta.

"Duk wanda kika faɗa mishi abinda yake miki shima sai ya mutu. Kinga kin faɗa ma Yaseer shima gashi can zai mutu, shima ya faɗa ma Auntyn ki itama mutuwa zata yi kema kuma zaki mutu"

Cikin hargitsi ta fashe da kuka tana riƙo hannun Hajiya Hauwa.
"Don Allah umman Jamal ki yi haƙuri kada su mutu, wallahi ba zan sake faɗawa kowa ba na rantse, idan na sake faɗa Allah ya tsine m..."

Kukan ta ne yake ƙaruwa muryar ta na tashi don haka Hajiya Hauwa ta saka tafin hannunta ta rufe mata baki gudun tonon asiri.

"Shikkenan na ji. Amma idan baki so su mutu sai kin faɗa ma kowa Yaseer ne yake miki kin ji?"

"Toh shi yaya Yaseer ɗin ba zai mutu ba idan na faɗa haka?"

"Eh, yanzu haka ma ya kusan mutuwa har da ciwon mutuwa a jikin shi amma idan kika ce haka ba zai mutu ba"

"Toh zan faɗa"

Ta murmusa tare da sauƙe ajiyan zuciya sannan ta mayar mata da oxygen mask ɗin ta, ta kwantar da ita. "Yauwa ƴar albarka, yanzu daddyn ki zai ci gaba da son ki, amma duk ranar da kika ce ma wani Jamal na yi miki wani abu toh har daddyn ki da kowa sai ya mutu."

Sai ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata, hajiya Hauwa ta saka ƙasan gyalenta ta share mata sosai.
"Ai yanzu babu wanda zai mutu har sai kin faɗa. Ki daina kuka kin ji Sarauniyar baban ta"

Ta shiga shafa kanta, Reina da bata son ganin fuskar ta sai ta rufe idanu a haka har barci ya sake awon gaba da ita bayan tsawon lokaci don nurse sau biyu tana shigowa tana fita suna a haka har Hajiya Hauwa tayi mata kyautar kuɗi saboda toshe ɓaraka sai zuba godiya take yi.

......

Dare ta raba, idanun masu ƙarancin damuwa ya fara nauyi amma akwai wa'inda duk halin sata irin na barci bai isa ya tunkaro su ba.

Yana dafe da kansa idanun shi a kan ƙafar shi duk da zuciyar shi ba su yake kallo ba. Ɗauko mishi hoton fuskar Fauziyya yake yi, da wasu moments a cikin tarayyar su da ba zai taɓa mantawa ba har duniya ta naɗe, lokacin da idan ya zo ƙofar gidan su ta leƙo taga shi ne sai ta ɗiba da ɗan iskan gudu ta koma.

Murmushi mai sauti ne ya kuɓuce masa duk suka juyo suka dube shi amma bai san ma yayi ba. yana tuna lokacin da ya ɗauki burin samun ta da kuma lokacin da ya same ta ɗin.

Lokacin da ta zamo kwanciyar hankali da nutsuwar shi, murmushin ta, kukan ta, sautin dariyar ta da rabon da ya ji shi har ya manta, sai yanzu abun yake zuwa kan shi cewa tun da Fauziyya ta haifi Hafsah yawan dariyar ta ya ragu, yawan kukan ta ya ƙaru, sai yanzu da lokaci yake niman ƙure masa ya fahimci hakan.

Da buɗewar ƙofar da miƙewar shi a kan ƙafar shi bai san wanne ya riga wani ba.
Yanayin da ya gani a kan fuskar likitar kawai ya saka shi fara sarewa.

Ya dai yi juriyar buɗe baki yace "doctor anyi Nasara?"

Sai da ya ja dogon numfashi kana yace "ku yi haƙuri ɗan cikin ta bai zo da rai ba"

Namijin ne, namijin da yake buri, namijin da ya ƙwallafa rai, ya rasa shi, amma a yanzu shine ainihin ƙarami daga cikin jerin gwanon damuwowin shi.

"Ita Fauzar fa? Tana lafiya ina?"

"Ku yi haƙuri..... Allah ya karɓi abun shi!"

Bai san cewa ya kai ƙasa ba sai da yaga Alhaji kalabu da Alhaji salisu a kan shi suna ƙoƙarin ɗago shi, haka ma dangin Hajiya Fauziyya suka yi kan mahaifiyarta da duk yanda tayi domin ta jurewa tayi tawakkali sautin kukan ta sai da ya suɓuce daga bakin ta.

Ƴan uwan ta ma kukan suke yi amma burinsu su tsayar da na mahaifiyar su.
A hankali aka gunguro musu gadon da aka rufe ta da bed sheet har kayi.

Sai aka rasa wanda zai buɗe a cikin su saboda tsoron ganin ita ɗin ce ya kama su, kaman idan basu buɗe ɗin ba za'a ce musu wannan wani gawa ne daban, Fauziyyar su har yanzu tana numfashi.
Chapter 49 · 0% Book details