Sashe 36
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarasawa ciki Yaseer yayi dukda babu wanda ya amsa sallamar shi, ya ƙarasa bakin carpet ɗin dake shimfiɗe a tsakar parlourn ya zuba a kan guiwowin shi, yana jira Alhaji Salisu ya gama ne ya gaida shi.
Ɗaya bayan ɗaya yaran gidan suke fitowa daga ɗakunan su suna wuce shi zuwa wurin cin abinci, wasu kuma su ɗebi abincin su koma ɗakin dashi amma babu wanda Yaseer yayi musu da su gaida shi, ko kallo ma bai ishe su ba.
Sai can jimawa har ya fara ƙosawa kafin Alhaji Salisu ya gama amsa wayar ya juyo ya dube shi.
"Ina kwana Alhaji" Yaseer ya gaida shi ba yabo ba fallasa.
A maimakon ya amsa sai ya haɗe girar sama da na ƙasa yana tambayar "Malam daga ina?"
Ɗagowa Yaseer yayi ya kalle shi cikin idanu, babu tsoro a cikin idanun shi, fargabar da yayi fama da ita ɗazu ma ta gudu don haka sosai yayi ma Alhaji Salisu kwarjini.
Kafin ya amsa shi Hajiya Hauwa ta fito ɗauke da food flask babba zata kai shi dining. "Yaseer ne fah. Ɗan gidan Kamalun jama'are, baka gane shi bane?"
A mamakance Alhaji Salisu ya juyo yana kallon yanda ya girma. Itama dai Hajiya Hauwa ta ɓoye nata Mamakin ne don kada ta kwabar amma Ranar da yazo suka yi magana bata gane shi ba.
Sai Alhaji Salisu ya sake mayar masa da tambayar "toh me yake tafe da kai da tsakiyar watan nan yasiru?"
Hajiya Hauwa ta sake amshewa da "shine Lesson teacher da muka ɗauka ma Jamal" tana tare-tare da shi ne saboda yanzu ba da bane, yaron ya girma yayi hankali kuma duk yananin da suka tare shi da shi zai riƙe su, sannan gashi tun ba'a je ko ina ba sun fara niman alfarmar shi.
"Toh toh toh, ashe har ka gama secondary ne?"
Ƙaramin murmushi yayi kana ya amsa da "Ina shirin shiga aji uku kenan a jami'a"
Sai ya jinjina kai, "Allahu akbar, a wani makaranta kake?"
"Nan ATBU"
"Tahiru kenan ko yaya kalabu suke biya maka kuɗin makarantar? Tunda ni ban san da zancen ba?"
Wani irin kallo ya watsa masa wanda bai san ma yayi hakan ba, sai kuma ya sauƙe idanun shi ganin girman da yayi ma mahaifin shi ma ba kaɗan bane kuma ba'a mishi tarbiyyar Raina manya ba, don haka ya amsa da.
"A'a, mahaifina yana da aiki shima"
"Aikin da Alhaji Tahir ya bashi?"
Sai Yaseer ya ja numfashi a ƙoƙarin shi na kai zuciya nesa. Matsayin shi kawai ake son gwada mishi ba komai ba, kuma ya tsammaci haka daga duka ahalin gidan, sai ya amsa da.
"Wannan kam ban sani ba, saidai idan na koma gidan in tambaye shi"
Dariyar da bai kai zuci ba yayi yace "Kada ka damu kanka, jeka, ayi karatu lafiya"
Bai ƙara cewa komai ba ya miƙe, juyowar da zai yi idanun shi ya sauƙa kan fuskar ta dake ɗauke da wadataccen murmushi. "Ina kwana Yaseer"
Tana sanye da kayan barci mai santsi babban riga da dogon wando sai gyale mai kauri da ta lulluɓe kanta zuwa ƙirjin ta dashi.
Sauƙe numfashi yayi, ya nufi hanyar waje ba tare da yace da ita komai ba, ba zai iya magana da ita a gaban su ba.
bata yi ƙasa a guiwa ba ta biyo shi.
"Meesha a nan kika kwana?" Yace da ita bayan sun fito waje.
Saurinta ta ƙara domin ta jera da shi tana faɗin "I wanted to surprise you, na san kuma you are functual zaka iso a kan lokaci , ni kuma ban gama barcin hutun gama exams ba I can't wake up before 9, shiyasa kawai nazo tun jiya na kwana a nan"
"So daga barin ki hostel da yammacin jiya a nan kika sauƙa baki je gida ba"
"Yep" ta washe fararen haƙwaran ta tana mishi murmushi.
Girgiza kai kawai yayi domin idan ka ganta a school ba zaka ce ta taɓa dariya ba.
Ƙarƙashin wani rumfar bunu dake cikin ɗan ƙaramin garden ɗin gidan suka ƙarasa, ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake wurin yana jiran fitowar Jamal tunda iyayen shi sun riga sun san da zuwan sa.
Itama jawo wani kujerar tayi ta saka shi yana fuskantar tashi ta zauna, kana tace
"You're not a gentleman Yaseer, tunda baka san ka jama mace kujera ba"
"Ba gashi dai kin zauna ba?!" Ya mayar mata.
Sai ta ɗan harare shi. "Why are you treating me like your sister? Ko dan ina sake maka da yawa?"
"Toh wa yasan miki yanzu kuma" ya ciro wayar shi tare da duba lokaci. 9 ne da minti 28. Kuma duk Alhaji Salisu ne ya ɓata mishi lokaci tunda ya shigo gidan ma taran bata cika ba.
Turo baki tayi tace "Allah da gaske nake, You should be taking me seriously, cos wa ya sani? Maybe mu zamo wani abu a nan gaba"
Ciza laɓɓen bakin shi yayi yana ƙarewa fuskar ta kallo. Ita kuma a duk lokacin da yayi hakan sai tana ƙara jin wani abu na fisgan ta a kan shi.
"In kai wannan kyan naki ina Meesha?"
Kuncin ta da yayi ɗumi tare da jaa a lokaci ɗaya saboda kalamin shi ta dafe tare da yin farr da idanu tana murmushin jin daɗi kafin ta gyara zama tayi ɗan gyaran murya tace "waye yace maka kaima ba kyakkyawa bane?"
"Toh shikkenan, naji. Shekarun ki nawa?"
"20" ta amsa a takaice.
"Shekara ɗaya na baki toh"
"Toh meye a ciki? Banda abu irin na Nigeria ma, a ƙasashen waje auren Sa'a da Sa'a suke yi"
"Haka ne, kije ki shirya ki tafi gidan ku." Ya gwada mata hanya a ƙoƙarin shi na kawar da zancen.
"Yauwa, ashe wai Uncle Salis ɗan uwan ku ne?"
Kaman bayi so ya gyaɗa mata kai kawai.
"Why didn't you tell me then?"
"Amfanin me zai yi miki idan na faɗa mikin?"
"Yana nufin mu ƴan uwa ne kenan"
"Taɓɓ, kalen dangi"
Haɗe rai tayi tace "waye mai Kalen dangin? Ni ko kai?"
"Ni mana! Cousins fa suke da uba na, me ya haɗa ni da su toh?"
"Ban gane me ya haɗa ka da su ba? Suma iyayen ka ne a al'adance. Ko akwai wani abu mara daɗi a tsakanin familyn ku ne?"
Ba zai iya da wannan tuhumar ba don haka ya riƙe hanci yace "don Allah kije kiyi wanka, tsami kike yi, ga kwantsa a cikin idanun ki"
Da sauri ta miƙe tana shinshina jikin ta, ta kunna cameran wayan ta a selfie tana duba fuskar ta. "Saida nayi wanka fa kafin na kwanta"
"Toh ni dai ina jin tsami"
"I know you're just pulling my leg, amma muje mu karya toh sai in sake yin wankan"
Taɓe baki yayi "ance miki gidan mu babu abinci ne da zan kai tara ban karya ba?"
Da ba'a yayi mata zancen amma sai taji babu daɗi tace "ba nufi na ba kenan amma kayi haƙuri"
Ya dai samu ya kora ta kafin ta sake ɓaro wani hirar, sannan yaci gaba da zaman jiran Jamal amma har goma da rabi shiru. Sai dai masu aikin gidan sun kawo mishi sabon white board da kuma kwalin marker da duster, sai kuma text books na subjects ɗin da Jamal zai rubuta Jamb ɗin a kansu.
Har Meesha ta karya ta sake wanka Jamal bai fito ba.
fitowa tayi cikin dogon rigan material da hula a kanta ta sauƙo da dogon gashin ta a baya, sai ta saka hair band ta daure shi hawa uku.
tana ɗauke da tray mai goran juice, ruwa da cup guda ɗaya, plate ɗin meat pie da kuma cookies. ta ƙaraso wurin Yaseer sai baza ƙamshi take yi.
"Da nace miki kina tsami, bance ki dulmuyar damu a cikin zunubi ba, don Allah kije ki saka hijab ko ki rufe kan ki yanda ya kamata" ya sake toshe hancin shi a karo na biyu idanun shi na kallon wani wurin.
A maimakon ta amsa shi sai ta ajiye tray ɗin a gaban shi ta riƙe ƙugu.
"Kambu! Yaron nan barin ka yayi kana jiran shi?" Ta juya fuuu ta koma cikin gidan.
Kusan minti 10 a tsakani ta fito riƙe da kunnen Jamal wanda ke sanye da guntun wando da tank top, yana ihu da ƙoƙarin ƙwace kunnen amma ta sha muurr.
Saidai ga mamakin shi ta saka hijab ɗin da yace.
"You're very stupid! Kasan yanda aka yi na samu nayi convincing ɗinshi ya yarda zai koyar da soko irin ka?" Ta talle ƙeyan shi ya saki ƙara 'Ahh!.'
Tsaki Jamal yayi sai ta ɗaga hannu zata make bakin Yaseer ya dakatar da ita. "It's okay Ameesha zaki iya tafiya"
Gwada shi da yatsar da take kaɗawa tayi tace "don Allah kada ka mayar da hankali tunda zaman gida bai ishe ka ba". Da haka ta wuce tana sababi shima bai fasa ƙunƙuni ba, sai Yaseer ya maido da hankalin shi gareshi.
"Sannu ko Jamal"
Tun daga kan ɗan iskan askin dake kan shi yabi da kallo, zuwa sarkar chain dake wuyar shi, da wasu abun hannu da ya saka irin na gayu da faracun shi zaƙo-zaƙo kaman mai cin kare.
A yatsine ya kalle shi "Malam kayi abinda ya dame ka"
"Ta ina kuwa zan yi abinda ya dame ni bayan bani son yin wannan aikin na shekaru biyu?"
Ya miƙe tare da ɗaukan jan marker ya buɗe ya rubuta cikakken sunan shi a kan allo.
Sai Jamal ya kalli sunan sannan ya juyo ya kalle shi ya sake kallon sunan. "Yaseer Kamal Jama'are da na sani?!"
"Eh shi ɗin dai, ɗan kauyen da kuke kora shine zai koya maka karatu a yanzu idan ka mayar da hankali"
"Bantan uba!" Ya miƙe baya a kan kujerar yana mishi dariyar rainin hankali.
Yaseer ya ƙara tamke fuska, "koma na waye ne dai haka zamu yi, domin kaman yanda dole ne ya zaunar da kai a nan nima haka ne, don haka idan zaka bani haɗin kai muyi abinda ya dace da yafi."