Sashe 46
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗagowa Reina tayi ta kalle ta kaman zata fasa ihu amma bata ce komai ba. "Yanzu ta rage tsalle-tsalle da rawar kai ɗinnan da surutun banza har abin naso ya damu Fauziyya amma sai ta saka ma ranta zaman asibitin ne bata so.
"Hafsatu na" ɗagowa tayi tana kallon Fauziyya dake mata dariyar karfin hali, ta cigaba da cewa "kina son cake? Zan baki chocolate cake mai daɗin tsiya idan kika faɗa min waye yake taɓa ki a nan"
Tayi ƙoƙarin ɗaga skirt ɗin ta amma sai tayi saurin jan baya tana hawaye.
"Wallahi ba kowa Aunty, Allah ba kowa"
Ta gane wayo kawai take son mata, tana buɗe bakin ta shikkenan zata ɗauki wukar da ta yanka apple ɗinnan ta yanka ta.
Suna cikin haka aka kwanƙwasa kofar tare da turo shi, Saudat ta shigo ɗauke da sallama a baki.
Sauƙe ajiyar zuciya Fauziyya tayi ta aro karamin murmushi ta yafa domin ɓoye damuwar ta, kafin tayi mata iso zuwa ciki.
itama sai lokacin ta juya tace ma Yaseer ya shigo ciki.
Sallama yayi da budaɗɗiyar murya ya ƙaraso ciki.
Reina na ganin shi tsugul ta mike zaune.
"Yaya Yaseer!!" Ta kira cikin muryar farin ciki haɗe da mamaki.
Har ƙasa ya kai a gaban Hajiya Fauziyya ya kwashi gaisuwa, saida ta amsa kafin ya ƙarasa gaban gadon Reina yana mata yaya jiki.
"Yaya Yaseer kayi haƙuri gobe zan zo class ka ji?"
Idanun Fauziyya na kafe a kan su.
"Ba komai Ki bari sai kin samu lafiya"
Da toh kawai ta amsa sannan ta matsa mishi a gadon wai ya zauna.
Cigaba da tsayuwa kawai yayi yana rejecting kiran da Meesha ta dame shi da shi, saboda kawai ya dawo gida ba tare da sanin ta ba.
Wannan ko uwar da ta haife shi albarka.
"Yaya mai jikin?" Saudat ta bukata.
"Ahh jiki da sauki alhamdulillah" Fauziyya ta amsa
"Allah ya ƙara sauƙi, amma mai yake damun ta?"
Ta so ta ɓoye mata amma sai take ganin kaman Saudat ɗin zata kawo mata mafita tunda ita da Ummi duk sun gagara amma gashi tana sakewa da ɗan ta.
Bata son yin maganar a gaban ta don haka ta buƙaci su fita waje, amma bata iya barin Reina da Yaseer su kaɗai ba saida ta tura musu Aina'u.
Aina'u ta shiga ta same shi zaune a bakin gadon yana fuskantar Reina. Ga abincin da ake buga daabi da ita kafin ta ci yana ciyar da ita cikin sauƙi.
Reina ta so ta faɗa mishi abinda yake faruwa amma tsoron idon Aina'u ya hana ta kada taje ta faɗa ma aunty, haka suka ƙarasa cin abincin cikin shiru.
.......
Fitowa yayi daga wanka sanye da jallabiya yana tsane kan shi da hand towel.
"Ai na ɗauka zan samu har kinyi barci tunda jirgin mun yayi dare sosai"
Rabon da ta samu barci cikin nutsuwa da walwala tun ranar da abin nan ya faru, balle yanzu da ya dawo, tana da tabbacin ba zata iya cigaba da ɓoyewa na tsawon lokaci ba, dole zai sani amma sai ta gama bincike tukunna.
Fauziyya dake kintsa ɗan shirgin da ya dawo da su don kawai ta guje ma idanun shi ta fitar da sautin murmushi kawai.
tana tsoron ya gano abinda take boyewa a yanayin ta wanda shima a nashi ɓangaren haka ne, yana tsoron ta gane abinda yake ɓoyewa a yanayin shi, amma tashi addu'ar bata karbu ba saboda hannun ta ne ya sauka kan wata ƴar takarda na hotel dake ɗauke da sunan wani hotel a Germany.
Ta ɗago tana kallon shi da takardar a hannun ta.
Shi da yace mata Abuja zai je?
"Ba abinda kike tunani bane wallahi"
"Zan so ƙarin bayani"
Ya karaso ya karbi takardan da yayi mamakin yanda aka yi bai jefar da shi tun a can ba gashi yanzu dole ya bayyana mata abinda yake faruwa don kar ta zarge shi.
Hannun ta ya riƙo suka zauna a bakin gadon suna fuskantar juna kafin ya dube ta da damuwar da ya bayyana a kan fuskar shi.
"Ina cikin babban matsala ne Fauzah, bani son ɗaga miki hankali ya saka tun da ban sanar da ke ba"
"Subhanallahi, wani irin matsala kenan wannan?"
Numfashi ya ja ya furzar kafin yace "kuɗin kamfani na ɗauka na shiga wani project da shi a yanzu kuma project ɗin yana ƙoƙarin crashing. Shine muka tafi da yaya Salisu daman shine ya gabatar min da project ɗin, ganin na shiga daga farko na ci riba ya saka ni sake komawa, kuma a tsawon sati ukun nan ba ƙaramin yawo mukayi ba Amma wallahi babu haske Fauzah "
"Amma har nawa ne kuɗin da zai ɗaga maka hankali har haka? Ba sai ka biya su ba tunda kullum dai kasuwa daɗa bunƙasa take yi alhamdulillah"
Wani irin murmushi mai ciwo yayi yace "Hmm fiye da Biliyan ɗari biyu..."
"La haula wala ƙuwwata illa billah!" Ta rufe bakin ta da hannun ta jin yanda muryar ta ya tashi saboda kaɗuwa.
"Wallahi. Yanzu kawai ki taya ni da addu'a Allah ya fitar da mu daga cikin wannan tsaka mai wuya. Amma in sha Allah Reina sai ta gaji TK kingdom don haka yanzu niman taimako zamu bazama wurin malamai ko Allah zai saka a dace"
Ambatan sunan Reina da yayi kawai sai da ya saka hanjin cikin ta kaɗawa, abin cikin ta ma sai da ya juya babu shiri, ta fitar da ɗan ƙara ya shiga mata sannu.
Zuwa Safiya ta daɗa rasa nutsuwar ta tun Alhaji Tahir na tunanin abinda ya dame shi ne ya dame ta har ya fahimci yafi hakan.
Ga sarauniyar shi tayi wani sanyi kaman ba ita ba.
"Fauzah, ke da yaran nan ina duk lafiya kuke da bana nan? Babu wani abinda ya faru ina?"
Kirjin ta ya buga dududum amma tayi yaƙin ƙaƙalo murmushi.
"A'a mai ka gani?"
"Don Allah idan akwai wani abun kada ki ɓoye min, zan saurare ki da zuciya ɗaya koma menene kaman yanda kika min uzuri nima zan yi miki.
Kaman yanda Reina tayi tunanin wayo Aunty take mata haka itama tayi tunanin Tahir ya faɗi hakan ne kawai a fatar baki.
Kaman yanda Reina taji tsoron hukuncin da zai biyo baya haka itama.
don haka sai ta girgiza masa kai.
"Wallahi babu komai!"
.......
"Yauwa Umma an sallami Reina daga asibiti ne?" Yaseer ya tambaya yana taje gashin kanshi da bayi gajiya, a rana sai dai idan ba zai saka ƙafar shi a waje ba amma sai ya taje kai ko mace albarka.
"Eh, ai tun washe garin zuwan mu aka sallame su, kuma uwan tace ta warware sosai"
"Toh Allah ya ƙara sauƙi"
"Amma Yaseer kai babu wanda ka lura yana ruɗan yarinyar nan a gidan aikin ka? Ko da wayo ko da razanarwa?"
Sauƙe comb din yayi ya juyo yana dubanta "bannn gane ba."
Bayanin abinda Hajiya Fauziyya ta sanar da ita tayi mishi sai kawai ya tsaya yana kallon ta kaman mutum mutumi, zuciyar shi ke bugawa a cikin kunnuwan shi, ya kasa gaskata abinda yake ji daga bakin wanda ya san ba zata masa karya ba.
Haka har ya ƙarasa shiri ya tafi gidan Alhaji Salisu jiki babu ƙwari.
Sai ya tsaya a filin gidan yana karewa masu hada-hada a cikin ta kallo. Toh waye? A ina? Tun yaushe?.
Juyowa yayi idanun shi suka shiga cikin na Jamal dake fitowa riƙe da littafi idanun shi sun ƙanƙance alamun yanzu ya farka daga barci yana tafe yana tsaki.
Wuce Yaseer din yayi yana jan wani dogon tsakin don har yanzu bai fasa mishi ɗanyen kai ba, shi kuma Yaseer yabi bayan shi da kallo ƙwaƙwalwar shi tana taryo mishi kusancin Jamal da Reina, alaƙar su da kuma kusanci na musamman da ya lura akwai a tsakanin su a dan zuwan shi gidan.
Ya ga abubuwa da yawa da a da yayi ƙoƙarin kawar da su daga cikin ran shi da tunanin sharrin zuciya ne kawai yake son raya mishi wani abun. Ga irin sunan da yake mata amfani da shi da kuma wasu maganganu marasa ma'ana da wani lokacin idan ya faɗa mata sai Yaseer ya dago ya dube shi sai ya fara kame-kame da bayanin da shi bai tambaye shi ba.
Yana da yakinin Jamal ne, abun da ya rage a yanzu shine tabbatarwa.
Ƙoƙarin jan ƙafar shi yayi ya ƙarasa suka yi karatun sama-sama, Jamal dai duk a tsarge yake da kallon da Yaseer din ya ƙure shi da shi.
Har lokacin na su Reina yayi sauran yaran suka fito ita bata zo ba.
Yau kam ya damu, har ya fara tunanin ko dai ya koma zuwa nasu gidan ne yana mata a can tunda a nan ɗin cutar da ita ake yi?
Bai ida tunani ba hancin motar gidan su ya danno kai cikin gidan.
Tsayawa yayi yana kallo ta fito daga cikin shi ta nufo su a ɗan hanzarce, sai ɗaya ɓangaren shima ya buɗe Hajiya Fauziyya ta fito....
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
33......Sauran yaran ma suka miƙe ta karaso suka rungume juna suna tambayar ta mai yake hana ta zuwa, domin suma sunyi kewar ta.
Duk cikin su babu wanda ya san tayi rashin lafiya don ko iyayen su ma basu sani ba, maganar na shiga kunnen su toh ya shiga kunnen Alhaji Tahir.
Rusunawa tayi har ƙasa ta gaida Yaseer, ya amsa idanun shi yana kan aunty dake takowa wurin a hankali nata idanun a kan Reina, al'ajabi sosai yake kama ta na yanda Reina take behaving sosai a gaban Yaseer, abinda ko iyayen ta basu sami darajar hakan ba.
Toh ko tsoron shi da take yi yana alaƙa da abinda ya faru da ita?.
Ta zurfafa cikin tunani sai ganin Yaseer tayi durƙushe a gaban ta a lokacin da zata taka matakala na ƙarshe da zai sada ta da cikin wurin.
Takalman shi da na yaran ya matsar mata a hanya sannan ya miƙe da wadataccen murmushi a kan fuskar shi yana mata iso.
"Bismillah Aunty, sannu da zuwa" sai kuma ta samu kanta da maida masa murmushin.
A yau bata shafa kan shi ba, Saboda wannan karon ba ƙaramin yaro ɗan shekara 12 bane a gaban ta, wannan Yaseer ɗin har ya fita tsayi sosai.