Sashe 12
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga yanda yake amsa mata magana a tsatstsaye yasa taji shakkar abin da zata faɗa da wani ido zai dube shi?
Da kamal ma ya gaida shi sai ɗaga mishi kai yayi kawai.
"Tahiru ƙafar ɗayan ku bai sake taka Jama'are ba tunda Allah yayi rasuwa wa mahaifin ku tsawon shekaru 15 kenan yanzu, kun manta cewa yana da cibiya bisine a can, yana da ƴan uwa yana da dangi ku kanku kawai kuka sani"
Tunda ya ganta yasan dama sai yaji irin wannan mitan, gwanda lokacin da baiyi aure ba bata sakawa da shi, duk jidalin tan a kan sauran ƴan uwan shi take sauƙewa sai su ɗan haɗa wani abu su sallameta kana aji shiru na ɗan wani lokaci kafin ta sake dawowa.
Amma shine yau zata saka shi a gaba kaman wani ɗan ta bayan shima gashi ƴar nan ya ajiye yanzu.
"Goggo yanayin aikin ne wallahi babu lokaci, wuni muke yi mu kwana muna nima, yanzu ma nima na ake yi a wasu ƙasashen amma babu halin zuwa balle ƙauye"
Ta jinjina kai "eh lallai. Kana da gaskiya, shine kuma babu waya babu aika? Ko sau ɗaya a shekara ka ɗaga waya kayi wa wannan tsohuwar gaisuwar azumi kana ganin ba zan ji daɗi bane? Da ace nima fa bani zarya a tsakanin ku da sai inyi ta ganin ku ma a talabijin in kasa gane ku, musamman ma kai tunda ka tafi ko shekaru ashirin baka cika ba."
Cikin ƙosawa da mitar tata ya miƙe yana faɗin "ton zanyi miki aika goggo in sha Allah, ku gaida gida, mun gode da ziyara Allah ya bada lada"
Sai ta samu kanta da murmusawa, wato shi mai hali bayi fasa halin sa. Daman shi haka Tahir yake ba'a taɓa cinsa a zance domin ba zai ma baka damar da zaka tofa albarkacin naka bakin ba.
"Koma ka zauna, tun da kaga nazo har cikin gidan ka na zauna na jira ka kasan da magana nazo"
Kaman ba zai zauna ɗin ba don ƙanwar uban shi ai ba uban shi bane, amma tsufar fuskar ta ya saka yaji nayin ta ya zauna ɗin yana duba agogon shi cikin matsuwa kaman wanda zaije wani Wurin.
"Tahir Idan mu kun yada mu shi ɗan uwan ku da yazo jikin ku ba zaku taimake shi ba? Ka duba niimar da Allah yayi maka fah, ka duba daular da kake rayuwa a ciki!"
Shi da Kamal suka sake bin gidan da kallo ita kuwa idanun ta yana kan shi. "Amma shine na ɗan uwan ka musulmi yake kwana cikin zafi da ƙunci, yaran shi suke zaune a gida saboda kuɗin abin buƙatar da zai tura su makaranta ya gagara"
Da sauri da Alhaji Tahir ya amshe da "Kamalu, ba kazo har cikin gidan nan ka karɓi kuɗin registration da uniform ɗin Yaseer ba?"
"Dubu ashirin ɗin?" Mamaki ya kama Goggo ganin har taƙama yake yi da hakan.
"Toh dubu ashirin ɗin ba kuɗi bane? Ba wahala aka yi aka same shi ba?"
Bismillah tayi ta miƙe Kamal ma yayi makan yanda tayi, "toh zan dawo maka da kayan ka in sha Allah. Ni bance ku bawa kamal kuɗi ba, Alfarma ɗaya na roƙa a wurin ku shine ku sama masa aiki, aiki ko wani iri ne indai zai iya, amma ba aikin da ake biyan dubu ashirin a matsayin albashi ba, a tunani na muna da gata a kasar ɗa a yanzu baka samun komai sai kana da hanya, amma ga hanyar baiyi mana rana ba.
Amma kada ku damu, Kamal zai rayu da taimakon ku da babu shi, zumunci kuma ba zamu fasa sadawa ba in sha Allah, idan kun gaji da ganin mu muka zo kada ku buɗe kofa" sannan tayi gaba Kamal ya bita a baya.
*Seemahwrites ✨*
*REINA 💍*
09......Tun daga ciki Hajiya Fauziyya ta fara jiyo muryar Alhaji Tahir amma kafin ta fito don ganin mai yake faruwa har su goggo sun ɗauki hanyar waje. Da hanzari ta bi bayan su da nufin ta tsaida Goggo amma tayi ficewar ta bata saurare ta ba, ranta ya riga ya gama ɓaci.
Shi kuwa yana zaune hankalin shi a kwance kamar bai yi komai ba, ya cigaba da danna wayar shi.
Juyowa tayi bayan sun rufe ƙofar a fuskar ta ta zuba mishi idanu yana ci gaba da danne dannen shi har saida yaji alamun idanun ta a jikin shi kafin ya ɗago suka yi ido huɗu tana ta faman cika da batsewa.
"Fauzah a..."
Fuu tayi gaba yayi saurin binta a baya, ɗakin da ta kwantar da Reina ta shige har zata rufo ƙofar yayi saurin saka hannun shi ya tare.
"Fauzah mai kuma nayi?" Ya kwaɓe fuska Tare da sassauta murya.
"Au baka ma sani ba? Yanzu idan mahaifiyar ka aka yiwa haka zaka ji dadi?"
Hade rai yayi, "yaya kuma zaki dinga hada wata mata ta mahaifiyata?"
"Shikkenan kayi hakuri" ta sake kokarin rufe kofar, wannan karon da ya rike sai ya dan saka karfi ya tura, bata da zabin da ya wuce ta sake mishi kofar ta koma bakin gado ta zauna yayin da shi kuma ya durkusa a gaban ta tare da daura hannun shi bisa cinyar ta yana leka fuskar ta da take kokarin kawar wa daga gare shi.
"Yanzu har goggo ta kai ta saka kiyi fushi da ni Fauzah? Nine fa! T dinki"
Da mamaki sai yaga idanun ta sun kawo ruwa, ya santa da saurin kuka amma a tunanin shi ba a kan abinda be kai ya kawo ba kaman wannan.
"Fauziyyah?! Ya kira ta cikin tausasawa da mamaki.
"T da Allah bai zabe ka ya baka ba wani zai zo har ya roke ka ne?" Tace hawayen suna samun daman bin kuncin ta.
"A kan wannan maganar kike kuka?"
"So kake Allah ya azabtar da mu a kan ya wadata mu domin mu taimaki yan uwan mu musulmai da addinin Allah mun gagara yin hakan? Dan uwan ma na jinin ka T?"
Jan numfashi yayi ya furzar, yaki jinin bacin ran ta ko yaya ne, ko a kan menene.
"Shikkenan zan yi abun da suke so kin ji? Bar kukan"
"Toh amma kanwar mahaifiyar ka har sai na saka baki T? Suma fa suna da hakki a kan ka a matsayin ka na wanda Allah ya hore wa. Kayi wa dangi na, kayi ma makwaftan mu, har kawaye na kayi musu Amma sai abokin wasan ka ya gagara?"
Tana nufin abokin wasa cousin amma sai cewa yayi "Ni ban taba wasa da shi ba. Ina ma ya ganni balle yayi wasa da ni?"
"Okay zancen Mama ya tabbata kenan"
Ya san idan yaci gaba da magana daure jijiyoyin jikin sa zaiyi da kan shi don haka yace "toh kiyi hakuri, ya samu aiki an gama in sha Allah, ba dai aiki yake so ba? Zan sama masa aiki"
"Kuma tace matar shi ta haihu, zaka siya musu ragon suna"
"An gama, sai me kuma?"
Yace da murmushi a kan fuskar shi ganin yanda take faman kumbure kumburen baki.
Share hawayen ta tayi da bayan hannu gudun kada ta ƙure iyakar ta yasa tace "shikkenan, muje ka ci abinci"
Lakatar fuskar ta yayi "sarauniya ta tasan inda ta gado kuka kuma idan tayi ace ta cika rikici."
"Hmm yau ba don goggon ba ma da ka san ba zaka zo ka same ta shiru haka ba"
A rikice yace, "Ina ba wani abun ta kawo kika karɓa kika bata ba?"
Ta girgiza kai "ko ɗaya, tsohon hannu kawai ta ji"
"Shikkenan, bari ma inga kyakkyawar fuskar ta duk na ƙagu, ba zan iya cin komai ban saka ta a idanu na ba. Amma rikicin mummyn ta ya jawo min tsaiko"
Miƙewa tayi tana faɗin "ku kuka santa" ta fice don tabbatar da an tanadar mishi da duk abin buƙata kafin ya fito."
.....
Daɗin ƙauye ba dai wadatar abinci ba, sai dai ace babu daɗi, musamman ma ƙauye irin Jama'are da Allah yayi wa niimar ruwa, sarari da ƙasa mai albarka. gari ne da ake noma na bugawa a jarida musamman ma na shinkafa, don haka mutanen da suka sauƙa yau a gidan Kamal tafe suke da buhuhunan su na abin da Allah ya huwace musu, kama daga kan shinkafa, hatsi, wake, masara harma da busashshen kifi. suna hutawa kuma suka shiga gyara da haɗe-haɗen abinda za'a dafa gobe suna, har su kayan miya an siyo, mai, maggi, sugar da su markaɗe da aka kai sisin kamal bai yi ciwon kai ba.
Toh irin wa'innan mutanen ne zaka samu ka gagara yi musu alkhairi? bayan su basu duba rashin ka matuƙar zaka sadar da zumuncin ka to nasu nasu ne kawai.
Sun haɗu tare da ƴan unguwa an bazama ana ta ayyuka domin so suke yi goben sai dai kawai ayi ta ɗaurawa ana sauƙewa, aka fara bugun ƙofar dake a buɗe.
Hakan ya saka jikar danejo fita da gudu don korar yara da tuntuni suke wasa a tsakani, tana da tabbacin su kaɗai ne marasa hankalin da zasu ga ƙofa a buɗe kuma su ƙwanƙwasa shi. Amma sai karo tayi da ƙattin maza guda biyu.
"Nan ne gidan kamal baban Yaseer?" Na farkon da yake sanye da ƙananun kaya masu kyau yana tashin ƙamshi ya tambaya. Bayan shi kuma mutumin tike ne riƙe da gabjejiyar rago. "Eh nan ne" ta bashi amsa.
"Yauwa kira mana shi"
Da toh ta amsa ta koma a guje.
A tsakar gida mahaifiyar ta ta tsare ta da masifa, "da na hana ƙannen ki guje-guje shine ke babbar banza zaki taya su?"
"Inna wasu ne suka kawo ma Abban yaya Yaseer rago, ƙatoto wallahi mai babban ƙaho"
Jin haka yasa matan dake tsakar gidan barin abinda suke yi suka leka wajen don gaskata zancen ta duk da sun ji kukan ragon amma anyi zaton na maƙwafta ne.
"Bayin Allah daga ina?" Amarya ta tambaya.
"Direban Alhaji Tahir ne ni, kuma ya aiko mu ne mu kawo ragon suna ma kamal wai"