Sashe 5
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yaya kai sai yaushe zaka koma school?" Ya tambayi Yaseer don yafi son tafiyar su a tare gaba ɗaya, yara basu iya cin zalin shi kuma shi ya sama masa abokai na kirki wande suka daidaita a matakin karatu dama mataki na rayuwa. Uwa uba idan da ƴan canji a hannun shi yana ɗan siya musu taɓa ka lashe kuma dama suhail akwai kwaɗayi.
"Satin gaba zamu tafi tare in sha Allah" ya amsa tare da komawa ya ɗauko mishi jakan bayan shi ƴar ɗinki mai ɗauke da littattafai guda 3; farin layi, jan layi da gidan dara. Sai pencil ɗinshi guda ɗaya wanda kullum Suhail sai yayi zaman fere ta tayi tsini, samm bayi barin shi ya duskure shiyasa cikin sati guda yakan ƙarar da pencil.
Sallama suka yi ma Yaseer da Saudat, suka riƙe hannun juna sannan suka wuce.
"Nima barin hanzarta kada oga ya riga ni isa shago" yace yana tattara kwanon dake gaban Saudat da wanda Suhail yayi amfani dashi ya kaisu mawanki. Bai ajiye su ba sanda ya wanke su tass harma da tukunyan da aka dafa abincin. Colandern da rabon Kamal yake ciki ne kawai ya bari sai karamin tukunyar da aka soya manja.
Ya wanke bakin sa ya sake taje gashin kansa kafin yayi sallama ma Saudat a kan zai wuce.
"Allah yayi albarka yaro na, ya kawo haske da nasara cikin rayuwar ka"
Da ameen ya amsa yana jin daɗin addu'ar ta kafin yaja silifas ɗinshi da ta fara suɗewa ya fice daga gidan.
Fitan shi bada daɗewa ba Kamal ya dawo hannun shi riƙe da baƙar leda. Rigan shi yasha kamɓorin datti da kuma ruwan kayan miya shima ya bushe.
Sannu da dawowa Saudat tayi mishi daga zaune ganin ba zata iya miƙewa ta tare shi ba.
Ajiye laidan hannun shi yayi a gaban ta. ya fara isa bakin tukunyar ƙasan su dake ɗaukar sanyi kamar fridge ya ɗebo tare da ɗauƙo kujera ƴar tsuguno ya dire shi ya zauna. Kai kofin bakin shi yayi yasha ruwan yana maida numfashi.
"Sannu da dawowa, yaya kasuwan?" Tace dashi.
"Kayayyaki suna tsada Saudatu abun saidai addu'a kawai, amma har gwarin ba sauƙi"
Jijjiga kai kawai tayi ta shiga buɗe laidan da ya shigo dashi. Bagen kayan miya ne sai ƙullin cray fish tunda tace mishi tuwo zata yi.
"Ina kuɓewan?" Ta ɗago tana tambayan shi.
"Ƙuɓewa ta ninka kuɗinta shiyasa kawai na dawo da abinda aka samu don nasan zamu fi buƙatar kuɗin."
"Amma kasan Yaseer bayi son miyan kuka"
"Yaci gaba da haƙuri wata rana za'a ci abinda yake so"
Jan numfashi Saudat tayi tace "Allah ya ƙara buɗi"
Da ameen Kamal ya amsa cikin jin daɗi ya tsoma hannu cikin aljihu sannan ya ciro tsofaffin ɗari biyar guda biyu, ƴan ɗari bibbiyu, ɗari-ɗari harma da hamsin-hamsin a ciki.
Ya gyara zaman su ya ƙirga sannan ya cire ɗari biyar-biyar ɗin ya miƙa sauran ma Saudat.
"Gashi 950 ne ki haɗa da na wurin ki a ci gaba da cefanen har muga abinda Allah zaiyi. Wannan kuma" ya miƙa mata sauran dubun hannun shi "zan ƙaro wani abu a tura ma umma, ta fara complain babu kuɗi a hannun ta ni kuma ga wata tayi tsakiya saidai a lallaɓa har a samu albashi"
Ta jinjina kai don gamsuwa da kudirin shi dukda shima kuɗin albashin an riga an cinye shi a bashi tun kafin yazo.
Ya miƙe kan ƙafafun shi tare da sauƙe dogon numfashi "Toh barin fara watsa ruwa kafin in karya in wuce wurin aiki"
......
Reina ce ta tashi Fauziyya daga baccin da ta samu ta mayar da safe bayan daren jiya ta hana su rintsawa, Mutane 3 a kanta amma kuka ta kwana yi kaman ta ari baki.
Ƙarfe 8 da rabi ne na safiyar Alhamis amma ma'aikatan gidan sun gama tsaftace ko wani lungu da saƙo da yake gidan duk girman shi kuwa. ƙamshin airwick da turaren wuta haɗe da sanyin Ac wanda an rage ƙarfin shi saboda masu jego amma duk wanda ya shigo gidan a cikin irin wannan yanayi na zafi ba zaiso ya fita ba.
Bai jira an wanke su ba Alhaji Tahir ya faɗo ɗakin, lokacin hajiya Fauziyya na ƙoƙarin shayar da Reina ko zata rufa musu baki.
"Good morning Habeebty" yace da ita yana ƙoƙarin zama ba tare da wani damuwa ba.
Ganin haka yasa mutanen ɗakin kowa ta kama gaban ta.
*Seemahwrites ✨*
*REINA 💍*
BookNest, Wattpad and arewabooks @seemahwrites
https://chat.whatsapp.com/JjjCOoAVsdP4PZbmCDrUOh
04...."My T. Ina kwana" ta maida masa da gaisuwar. Tana ƙarawa da "kaga ƴar rigimar ka ta hana mu barci ko?"
Ya murmusa, kwana 5 kenan amma har yanzu wani ɓangare na jikin shi ya kasa gaskata cewa wanzuwar Reina cikin rayuwar su gaskiya ne ba mafarki ba.
"Duk wata Sarauniya ai da rigima aka santa Fauzah ta"
"Oh haka ma kace? To gobe wurin ka zan kawo ta ku kwana"
Saida ya dara kana yace "Da kuwa kinga yanda ake raino mai kyau ba Irin naku na ƴan koyo ba."
Zancen shi ya saka ta darawa itama "ai ko? To kuwa kada daga baya kazo kace ba haka ba"
"Ki gwada ni mana ki gani" yace yana miƙa hannu ya karɓi babyn Ganin ta cire bakin ta daga jikin Fauziyya.
"Zo nan ƴar albarka, baiwar Allah, Fauzah tana so tayi miki sharri ko?" Yace yana lakatar fuskar Reina ita kuwa ta shiga murmusawa.
"Masha Allah tabarakallah, Fauzah kaman kakin yarinyar nan kika yi"
Leƙa fuskar Reina Hajiya Fauziyya tayi tace "ni kuwa banga kaman da ake ta cewan ba T. Haka hanci na yake a nane?"
"Toh ta girma ne kika ga bai tsiro ba?" ya amshe cikin salon karɓa ma ƴarshi faɗa.
"Oh ashe hancin ma shuka ne da zai tsiro"
Ciza laɓɓan shi yayi ya ɗan jijjiga kai. "Idanma bai fito ba zamu yanke naki ne mu dasa mata"
"Lala-lala, Sarauniyar babanta ne ba nawa ba, kuje can ku ƙarata da munin ku" tace tana taɓe baki.
"Munji mun gode kuma zaki maimaita" ya sumbaci kumatun Reina sannan ya maida ta ma Fauziyya yana faɗin "toh mun fita sai ayi mana addu'a"
"Allah ya kiyaye, ya tsare kuma yasa a samu abinda aka je nima"
Da ameen ya amsa yana juyawa baby ta callara ƙara. "Iyee, to ai sai kazo ku tafi tare, kaga tun yanzu an fara nuna min fifiko"
Juyowa yayi ya dawo yana faɗin "Don kada ki wuni kuka ne amma da taren zamu tafi" ya sake manna ma Reina sumba kafin ya juya ya fice yana jin kukan ta a cikin zuciyar shi.
Ba'a ɗauki awa guda ba mai jego ta fito cikin rantsatstsiyar leshi da jaririyarta cikin shawul. Ƴan barka har sun fara sintiri, da wanda zuwan su na farko kenan da kuma wanda so da girmama abin duniya ya saka su dawowa a karo na barkatai.
A cikin baby basket aka saka Reina duk mai son kallon ta saidai yaje ya leƙa don kada a saka mata tsamin jiki a garin passing-passing.
Aka fara shigo da abin kari ma ƴan gaisuwa nan suka zauna suka baje shi tsaff, kafin a ɗaura abincin Rana shima suyi mishi illa.
Hira ta zauna suka sha da baƙin ta dama wanda bata wayi fuskokin su ba har zuwa jimawa da aka samu Reina ta maida barci sai ta nemi iznin ta koma ciki don basu samu isasshen barci ba daren jiya.
Bata sake fitowa ba saida aka yi azahar nan tazo ta samu yawan mutane sun ninka na ɗazu kaman ma yaune suna, haka ta zauna aka sake sabon gaisuwa.
.....
"Yanzu sake komawa zaka yi?" Tace tana jingine da jikin wardrobe ɗinsu da ƙofofin sun ɓaɓɓalle amma gyara ya gagara saboda damuwowin su na yau da kullum yafi ƙarfin wannan.
"Inada zaɓin da ya wuce wannan ne Saudah? Kina gani dai sati ya kusan ƙarewa yaron nan yana zaune a gida, gashi kema EDDn ki ya kusa, ba zanso har ki haihu Yaseer bai koma makaranta ba" Kamal ya sanya rigan da ta ciro mishi ya shiga haɗa botir.
"Kema da kin shirya ne muka je kika yi musu barka, Hajiya Fauziyya ba zata ji daɗi ba idan baki je ba bayan ta roƙe ki ki dawo."
Taɓe baki Saudat tayi tace "tana zagaye da jama'a ina har zata wani lura da rashin zuwa na?"
"Kiyi haƙuri mu dai je ɗin"
Ta turo baki. "Nifa ba daɗi nake ji ba abban Yaseer."
Sauƙe murya yayi cikin lallashi yace "kiyi haƙuri."
Tana zunkuɗe-zunkuɗen baki ta shiga shiryawa. Shi da kanshi ya fita waje kiran Suhail a wurin wasa kasancewar yau Alhamis babu Islamiyya, shi kuwa sai murna yake ganin za'a je anguwa. Cikin zumuɗi ya shirya
Har sun fito ta jawo musu ƙofa Yaseer ya shigo da uniform ɗin hadda.
"Ina wuni Ummah, ina wuni Abba, fita zaku yi ne?"
"Gidan Alhaji Tahir zamu je yin barkan sabuwar jinjira" cewar Kamal.
"Toh sai kun dawo, Allah ya kiyaye" yace yana nufar hanyar ɗakin su da nufin ya ajiye jakar shi don ya ɗibo yunwa.
"Ai yanzu kam shiryawa zaka yi muje ka taya ni da wannan sarkin rikicin" Saudat ta nuna Suhail da ya washe ma Yaseer ɗin haƙwara baki ɗaya murna ya cika shi.
Sosa kai yayi "Umma zan shigar da hadda ne"
"Babu jimawa ai zamu dawo, sai mu siyo sabon batir ɗin toci ka shigar da haddan da daddare"
Da toh ya amsa sannan ya shiga ɗaki ya sako T-shirt ɗin gwanjo navy blue da baƙin wando ya fito ya ɗauki buta sannan ya ƙarasa bakin rariya ya ɗauraye ƙuran ƙafar shi ya koma ya shafa mai a ƙafar da fuskan shi sai ƙyalli suke, bai manta da taje kanshi ba.
kafin lokacin da ya gama Saudat ta gaji da tsayuwa ta samu kujera ta zauna amma kuma bata ƙosa da jiran nashi ba dukda ma bayi da sanyin jiki ko kaɗan.
"Muje umma" yace da ita yana kama hannun suhail, kamal ya riga da ya wuce nima musu napep, itama ta miƙe suka fita.
.