← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 57

Sashe 25

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi kuskure da ya biye mata suka dinga samun saɓani da tsohon ciki a jikin ta. Amma gani yake yi komai lokaci ne kuma a hankali Reina zata girma, zata yi hankali, zata yi ilimi, kuma duk wani rashin ji zata bar shi. Duk wannan aikin lokaci ne kawai, kuma kowa da haka ya fara.

Yana gama cin abincin kuwa ta fita da kwanon ba tare da ta sake ce da shi komai ba, babu wani nasiha, darasi ko faɗakarwar da ya wuce halin da ya shiga a yanzu, idan bai canza daga wannan ba toh tayi imani babu abin da zai saka shi ya canza.

Saudat sun je gaisuwa asibitin lokacin har Fauziyya ta farka amma bata umm bata umm-umm, sai-dai ta bi mutum da idanu kawai. Amma zasu iya cewa wannan shine karo na farko da suka miƙa gaisuwa ma Alhaji Tahir ya amsa girma da arziƙi, duk yayi wani sanyi kaman ba shi ba.

Sai da jaririya tayi kwana huɗu a kwalba kafin ta fara shiga hannun mutane, Alhaji Tahir ya saka mata sunan mahaifiyar sa Zainab ana mata alkunya Da Maama kamar yanda suka riga suka tsayar da Hajiya Fauziyya.

Tun da ta farka bata buɗi baki ta ce komai ba har sai lokacin da aka saka mata Maama a hannun ta.
"Hafsatu na kin daina kuka?" Ta tambaya maganar na fitowa a hankali ɗaya bayan ɗaya, fuskar ta na bajewa a sannu murmushi na bayyana a kan fuskar ta.

Matso da Reina dake boye a bayan ta Ummi ta yi zuwa gaban gadon don tsoron yananin Fauziyyar take ji har ran ta.

"Ga Hafsatu nan" tace mata.

Sai ta ɗago ido ta kalli Reina lokaci ɗaya tana haɗe giran sama da ƙasa. "Wa ya koya miki zagi? Yau sai na zane ki a gidan nan!"

Ai kuwa ta callara ƙara ganin Fauziyyar tayi wani yunƙuri kaman zata cafko ta, ta koma bayan mahaifin ta a guje tana kuka, ita kuma zafin fama ɗinkin ta ya saka ta miƙewa a gadon tana cije baki, Ummi ta karɓe Maama a hannun ta kwalla na cika idanun ta.

Ta san hatsarin sarƙewar haƙori, ta san illar da yake wa rayuwar mutum. Yana raba mace da hankalin ta ko rayuwar ta baki ɗaya. Wata kuma daga wannan jinyar toh tayi ta fama kenan har tsufa ko mutuwa su riske ta.

....

Satin Fauziyya biyu a asibiti kafin aka sallame ta suka maida jinyar gidan su. Daga farko Alhaji Tahir ya so yayi musu tawaye a nan ne Ummi ta tsaya ta nuna mishi iyakar shi.

Kuma da yake bata son ganin Reina a kusa da ita ko kaɗan da ta ganta zata fara masifa wani lokaci tana yi tana kuka, ya saka Alhaji Tahir tafiya da ita kuma yaƙi kowa ya karɓe ta a cikin ƴan uwan shi, sai dai ya ajiye ta a wurin su idan zai je aiki da ya dawo yazo ya ɗauke ta su tafi gida.

Idan aka ce a daddafe yayi wa'innan kwana sittin an rage ma tashin hankalin shi girma.

Tun ranar da Fauziyya ta faɗi bai sake sanin abin da ake cewa nutsuwa da kwanciyar hankali ba balle wani abu wai shi farin ciki.

Gidan ya rikice, duk da Reina tana da nanny Amma a rikice take shi kam ba'a ma magana don a office ma ba gane mishi ake yi ba.

Yayi ziryan gidan su har ya gaji, sai dai a bashi Maama su ƙarata, ga yarinyar babu ruwan ta, bata iya rikici ba sai barci kawai.

Fauziyya kuma idan ta fito su gaisa minti 15 yayi yawa za'a maida ta ciki da sunan wanka, shan magani ko wani abun.

Ba zallan ramewa ba zuwa wannan lokacin har baƙi yayi.

Yau kam ya kuɗurta a ran shi idan basu bashi matar shi ba, waliyyan shi zai turo su ji ba'asi.

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)*

*REINA 💍*

*Wannan shafin tukuici ne a gare ku, Maryam gambo da ƙawata Mrs Jay Kakan Reina😅. Ina godiya 💕*

18...... A jikin motar shi ta jingina tare da goya hannun ta a saman ƙirji kaman wacce tazo hira wurin saurayi.

Tana sanye da baƙar abayar da ya ɗauki hasken fatar ta ga wani haiba da tayi wanda yake tabbatar mishi da tana cikin hutu da kwanciyar hankali bayan ta bar shi da Reina a cikin ƙunci da Rashin walwala.

"Fauzah?!" Alhaji Tahir ya kira ta cike da mamaki ganin har da taunar chewing gum take, ko Fauziyyar shekaru biyar baya ba haka take ba.

Sai da tayi ƙoyi da chewing gum ɗin ta hura shi ya kumbura ya fashe kafin ta tauna shi ya bada sautin ƙasss. Kana ta amsa da
"Na'am my T. Ina wuni"

Ya jinjina kai tare da faɗin "gaskiya ne. Fauzah kin manta da kina da ƴa a wata uwa duniyar, da aure na a kan ki amma kin dawo gida kin yi zaune abun ki, shin rashin lafiya ya tafi da tunanin ki ne ko me?"

Ta jinjina kai, Tahir dai ba zai canza ba. Wahala da daɗi ba za su saka shi ya daina son kan shi ba. Shi kan shi kawai ya sani, a kan son zuciyar shi kawai yake jajircewa ba tare da damuwa da yana cutar da wanda yake tare da su ba.

"Wata ƴa wai? Ga yarinya ta nan Maama, ai Reina kam taka ce, na bar maka ita halak malak".

Ya gyara tsayuwa, yana son yayi mata uzuri amma ya kasa. Ciwo ba hauka bane.

"Mu shiga mota mu yi magana" ya riga ya yanke shawarar da ta shiga locking motar zai yi ya gudu da ita, in yaso daga baya su biyo ta da Maama, amma wannan rainin hankalin ya gama isar shi.

Kaman ta karanci zuciyar shi, ko dan halin shi ta karanta ne?. Sai kawai ta saki murmushi mai sauti kafin tace "A'a nan ma ya Isa T. A cikin gida muke, me kuma zamu sirrinta a cikin mota da ranar Allah. Bari dai in ɗauko mana kujera mu zauna" ta juya zata tafi ya riƙo hannun ta.

"Fauzah ko wani abu kika fara sha ne?"

Da mamaki ta kalle shi amma murmushin dake ƙara tunzura shi bai bar kan laɓɓenta ba tace "me kuwa zan sha da bani sha a gidan ka? Garau nake"

"Naji, koma meye ki yi, amma yau ba zan bar ƙofar gidan nan ba tare ke ba"

"Tohhh, gashi kuwa Ummi bata min izinin tafiya ba"

"Da ni da Ummi wa yafi wani iko a kan ki?" Taku biyu, sai gani tayi ya cika mata idanu. Anya zata iya isar da wannan saƙon nata? Ba salon da ta saba da shi ba kenan, tafi ganewa yin magiya da kuka ya mata abin da take so. Amma tunda sun rage yin aiki a kan shi dole ta bi shawarar Ummi ta dake don tseratar da hankalin ta da rayuwar ta.

Sai da ta hadiyi miyau kafin cikin ƙarfin halin da ta ƙi bari ya gwada raunin ta a fuskarta tace "kaine mana, amma iyaye na a yanzu sun goya min baya, ko me ya faru tsakani na da kai zasu bani mafaka. Don haka banyi niyyar komawa a yanzu ba sai ka ƙara min lokaci" da ƙyar ta kai kalmar ƙarshe don gani take yi yanda yake huci kamar zai ɗaura mata mari.

"Ni kike faɗa ma wannan maganar Fauziyya? Baki da hankali ne?"

_A'a tarbiyya ne bani da shi, ba'a nutsu an bani ita yanda ya dace ba. Duk da ni ba ƴar kowa bace da irin riƙon da kake wa taka ƴar iyaye na suka yi min da yanda rayuwa ta da kai zai kasance kenan. Sai abin da na so, a lokacin da naso, sannan babu kunya da fargaba a cikin lamari na. Ba zan juri ladabi da biyayya ba domin ban saba da yin shi ma na gaba da ni ba tun a gida. Kalaman kan harshe na babu daɗi saboda ban iya tace su a rariyar sanin ya kamata ba, duk kaifin abin da yazo kan ta haka zan watsa shi ma duk wanda ke tare da ni ba tare da damuwa da girman shi ko matsayin shi ba._

Wannan sune abubuwan da take son faɗa mishi a wannan gaɓar, Sai dai idan ta faɗa din da harshe ba lallai ya ɗauke su ba balle yayi amfani da shi, kamar yanda suka saba yi a baya.

Don haka mai hankali shi ke gane karatun kurma, gwanda ta nuna mishi hakan a aikace ya ji dafin illar shi a jikin sa.

"Ka san ance rashin lafiyar da nayi yakan taɓa ƙwaƙwalwa, toh hala shine"

"Ai naga alama kam. Bari in tafi kafin ki shafa min ko kuma in yi miki abun da banyi niyya ba" yace tare da danna key ɗin motar shi yayi ƙaran buɗuwa. Yau ko driver bai ɗauko ba saboda da niyyar kidnapping ya zo, amma banda ɓacin rai babu abin da ya samu.

Ya shiga ya kunna motar yayi reverse, ta kwala kiran yara daga ciki su zo su buɗe masa gate. Sannan ta shiga ɗaga masa hannu tana bye bye da faffaɗan murmushi a kan fuskar ta, har da hura masa kiss ɗin da ya ƙara kawo shi har wuya, ya zugi motar da ɗan iskan gudu yana jin kaman zai tashi da wuta idan bai yi ya bar unguwar ba.

Yana fita ta zuba a kan guiwowin ta hannun ta a kan zuciyar ta dake bugawa a tamanin-tamanin tana maida numfashi, bata taɓa tsorata da yanayin shi ba kamar na yau, Amma tun da an ƙare lafiya falillahil hamdu, yanzu fata ɗaya ya rage shine Allah yasa yayi amfani.

.....

Gidan Hajiya Jummai ya wuce ɗaukan Reina daga wurin, hala idan ya ganta zai ji sanyi a ran shi.

Ta tanadar mishi da abinci na musamman tunda daman ta san da kan shi zai zo ya ɗauke ta.
Chapter 25 · 0% Book details