Sashe 45
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
T ɗin da ta kira shi ya goge sauran kalmar don haka ya miƙe, yace "toh bari na tafi, ki kula da kan ki da kuma yaran , in dawo inga canji a yanayin ki don Allah"
Ta gyaɗa masa kai tana leƙen fuskar damuwar shi ta ƙasan ido sai kuma ta ɗan ji daɗi a ranta har ta fara jin kaman komai zai iya wucewa a yanzu.
"Ko zaki min rakiya ne?"
"T bani jin daɗi fa" tace cikin muryar shagwaɓa.
Murya a tausashe yace "Kiyi haƙuri don Allah, ban sani bane ko idan na tafi ba zan dawo ba, kinsan haali na tafiya"
Sai ta saki kan sannan yayi gaba ta bishi a baya tana jan cikin da yayi girma yanzu, har zuwa jikin motocin shi.
Kayan taɓe-taɓe irin wanda yaran shi suke ci kuma ya san ba za'a samu a nan ba shine aka zube ɗazun na Reina da Maama.
Sai kuma aka fito mata da akwatunan kayan su daga booth.
A wurin ya saka mata kuɗi masu yawa na bukatun ta dama yaran kafin suka yi sallama ta bishi da addu'a ya tafi.
.....
"Reina lafiya?" Hajiya Fauziyya ta riƙo kafaɗun ta don jin damuwar ta.
Rawan banjo take mata a wurin tana matse cinyoyi "Aunty fitsari nake ji"
Haɗe fuska tayi duk wani yunƙuri da zata yi na sauraron yarinyar nan sai ta bata haushi.
"A bakina ne zaki yi fitsarin? Ko sai na zo na kai ki?"
Fashewa tayi da kuka tace "yaƙi fitowa ne"
"Yaƙi fitowa kuma?"
Rage tsayin ta tayi ta ɗaga rigan da ya kai ma Reina zuwa cinya tare da saɓule pink ɗin leggings ɗin tare da pant ɗinta har ƙasa sannan ta leƙa wurin, lokaci ɗaya kirjin ta ya fara bugu fat-fat!
Wurin yayi jaa ga ƙuraje sun feso mata sosai.
Ɗagowa Fauziyya tayi, tayi mata irin kallon da ta daɗe rabon ta da mata irin shi. "Reina akwai abinda kike sakawa a private part ɗin ki ne?"
Da sauri ta girgiza kai.
"Toh zaki faɗa min waye yake taɓa miki wurin?"
"Wallahi tallahi babu" tsoro ma har ya saka ta bar rawar matsuwar.
Ƙwafa Fauziyya tayi ta ja hannun ta zuwa ɗakin su tace ma mai aikin da take gyaran ɗakin taje ta kira mata Aina'u kuma kada ta dawo sai ta nime ta.
Daman Aina'un tana kusa don haka babu ɓata lokaci ta ƙaraso ta samu Reina mai rawan fitsari da Fauziyya da ta kasa zaune ta kasa tsaye.
"Gani Aunty"
"Yauwa saka ta tayi fitsari don Allah " tace da ita tare da ficewa daga ɗakin.
Bata wuce ko ina ba sai kitchen ta zaro sharbeɓiyar wuƙan yanka nama sannan ta dawo lokacin sai yunƙuri Reina take yi na fitsarin amma sai kaɗan-kaɗan yake fitowa kuma da tsananin zafi.
Shiga banɗakin tayi ta nufi Reina dake zaune a kan toilet seat gadan-gadan da wuƙar sannan ta cukumo wuyar riganta ta kawo wuƙar kusa da fuskar ta tana zare idanun ta da sun kaɗa sun sauya kala.
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Aunty lafiya? Mai yake faruwa?" Aina'u tayi kokarin riƙo Fauziyya amma sai ta fisge.
"Zaki faɗa min wanda yake taɓa ki a wurin ko sai na yanka ki?!!"
A razane ta saki ihu "wayyo Allah Aunty! kiyi haƙuri! na shiga uku!"
Ta jijjigata "ba zaki faɗa min ba sai yau kin mutu?!"
"Wallahi babu kowa Aunty!. Wallahi, tallahi, billahillazi la ila...,"
"Ba rantsuwa nace kiyi min ba, ki faɗa min ko in yanka wuyan ki da wukan nan!"
Idan ta ɓoye aunty ne kaɗai zata hukunta ta. Amma idan ta bayyana...
Idan ta bayyana aunty zata hukunta ta, daddyn ta ma hala yayi mata horo mai tsanani. Jamal zai ƙona ta, yace mummyn shi ma idan taji zata yanka ta, sannan idan ta shiga kabari ma Allah zai yi mata azaba da su macizai da wuta, haka Yaseer yace.
"Aunty don Allah abi komai a sannu." Aina'u ta shiga roƙon ta amma Fauziyya ta kurmance ta makance.
Ta sake wuyan rigan Reina ta ɗauke ta da zazzafan mari kafin ta sake mata ɗamƙar da yafi na da, amma sai kawai ta biyo hannun ta yuuu kafin ta ankara ta zube a ƙasan bandakin sumammiya.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
32......RANAR WANKA
Zaune suke a harabar asibitin ita da Aina'u domin Fauziyya ji take yi duk iskan dake ciki ya kasa ma huhun ta.
Ta rasa wani irin tunani zata yi, ta rasa mai yake mata ɗaɗi, idanun ta a bushe sai zuciyar ta dake zafi kawai.
Motar yayan su ne yayi parking Ummi tayi saurin fitowa ta tunkaro su, "lafiya dai Fauziyya? Ina Hafsatun? Mai ya same ta?" Ta tambaya cikin kaguwa saboda Aina'u ne tayi azancin kiran su ta sanar da su an kwantar da Reina a asibiti, amma dalilin hakan yayi mata nauyi ta sanar da su don haka ta bari idan sun zo suji daga bakin ɗiyar su.
Matsawa Aina'u tayi Ummi ta maye gurbin ta, yayan su ma ya zauna ta ɗaya ɓangaren yana bubbuga kafaɗan ta cikin sigar lallashi, amma har yanzu idanun ta suna kafe a gaba kaman bata san da zuwan su ba.
Ummi ta riƙo hannun ta na dama cikin nata duka biyu tana murzawa a hankali.
"Fauzeen Ummi, faɗa min abinda ya faru kinji? Cuta ba mutuwa bace Allah zai ɗaga kafaɗun Hafsah"
Sai ta juyo a hankali tana duban ta. "Ummi, na shiga uku!" Daga nan hawaye ya ɓalle mata kaman saukan ruwan sama, ta damƙo hijabin Ummin sannan ta cusa kanta a cikin jikin ta tana kukan da ya jawo musu hankalin sauran majinyata.
Babu wanda bai kawo cewa mutuwa aka yi mata ba.
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" shine abinda Ummi ta shiga nanata mata.
Da ƙyar ta samu ta kama maimaitawa cikin muryar kuka har muryar ta na shaƙewa.
"Kai danna min kiran Abban ku ya bar abinda yake yi yazo wannan lamarin babba ne" Ummi tace da yayan su.
Ciro waya yayi daga aljihu zai kira shi Fauziyya tayi saurin miƙewa ta riƙe wayan "A'a, kada ka kira shi don Allah. Yana sani zai faɗa ma Tahir kuma ban san da wani ido zan dube shi ba wallahi, Tahir zai iya raba ni da yara na har abada ku rufa min asiri"
"Shikkenan ba za'a kira shi ba" ya sake mata wayar ganin yanda ta kiɗime.
"Ummi muje ciki sai in faɗa miki" ta fara ƙoƙarin tsayar da hawayen da bai ma san tana yi ba, zuba yake kan yi abin shi.
Babu musu Ummin ta miƙe, itama ta ja hannun ta ciki, fauziyya ta gwada mata ɗakin da aka kwantar da Reina suka shiga.
Tana kwance tana barci ga drip ɗin da aka ɗaura mata, sai bakin ta dake fashe da gefen fuskar ta da yayi jaa wurin da Fauziyya ta mare ta.
"Mai ya same ta?" Ummi ta sake tambaya.
Sai da ta riƙi gadon duka biyu ta sauƙe duban ta ƙasa kafin tace "Ummi wani mugun ne yake son ƙarar da rayuwar yarinyar nan tun bata fara shi ba. I think she's being molested"
"Ya rabbal alameen! Wa kenan? A ina? Yaushe?"
Ta ɗago tana girgiza kai don gani take yi kaman ummin ma ganin laifin ta take yi "wallahi ban sani ba Ummi, ta ƙi faɗa firr, ni kuma bani zargin kowa."
Ganin kukan ta ya dawo sabo Ummi ta sake jawo ta waje don kada su tada Reina.
"Yanzu mai likitan yace"
"Ta kamu ne da UTI, infection ɗin mafitsara, sai kuma rashes da suka feso mata a wurin. Ummi shekarar ta tara kacal fah!"
Salati Ummi ta sake yi, ba don itace ƙarfin guiwar Fauziyya ba da itama kukan zata yi.
Sun daɗe zaune a wurin kowa na saƙa da warwara a tashi zuciyar kafin Ummi tace "toh yanzu yaushe zaki sanar da mahaifin ta? Don ya kamata ya shigo cikin lamarin nan a bincika"
Girgiza kai ta shiga yi "na san waye Tahir wallahi Ummi, musamman ma a kan Reina, kafin ya bincika sai ya ɗauki matakin da dukkan mu ba zai yi mana daɗi ba, zai ɗaura min laifin abinda bani da masaniya a kai daga baya ya zo yayi nadamar da bashi da amfani. Gwamma ni in bincika in kamo koma waye kafin nan"
Tunanin ta lokacin da take gida abin ya fara, don haka Ummi bata tuhumi Fauziyya ba da tace bata da masaniya a kai.
Haka suka yi ta jinyar Reina har na sati guda, sa'ar ta ɗaya Alhaji Tahir ya ɗaga dawowar shi kuma kaman bayi cikin mutsuwar da zai fahimci komai ba lafiya ba, don idan ya buƙaci zantawa da yaran kullum da uzurin da Fauziyya take bashi, Maama ma yanzu tana wurin Ummi, tsakanin Reina da Fauziyya kuma sai kallo don har yanzu da take bin ta da lalama ta ƙi faɗa mata, gashi likita ya gargaɗe ta sosai a kan tsorata ta idan ba so suke yi su suka mata panic attack ba domin tsoron shi yake saka ta suma.
A rana na shida Yaseer ya kawo Saudat asibitin a mashin ɗin abban shi, don haka suka shigo tare.
A sanadin shi ma Saudat ta san Reina bata da lafiya domin ta kwana biyu bata zuwa lesson kuma ya ji a bakin sauran yaran wai ai Auntyn ta ne ta dawo. shine ya matsa mata ta kira Hajiya Fauziyyan ta tambaya domin bayi son shi da kanshi ya tambayi Alhaji Tahir balle Hajiya Hauwa, Alhaji Salisu kuma tare suka yi tafiya Abuja.
Bayan sun gaisa da Saudat tana tambayar ta Reina ko lafiya Yaseer yace bata zuwa lesson. Mamaki ya kamata jin wai ana yi musu lesson ashe, Alhaji Tahir bai faɗa mata ba, kuma itama Reina bata fada ba duk da ranar zuwa lesson ɗin bai zago ba wannan abin ya faru.
A nan ne take faɗa mata ai an kwantar da Ita ne a asibiti shine a yammacin ranar suka zo duba ta.
Tana zaune da kwanon abincin da take ta juyawa tana kallon shi, shikkenan Aunty kuma ta dawo za'a ci gaba da bata abinda bata so.
"Kici abincin mana" Fauziyya ta ajiye plate ɗin apple da ta fere ta yanka mata a gefe.