Sashe 56
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Please To be clear document sai an kammala haɗa labarin kafin a same shi, wanda basu samu a lokacin da ake posting bane idan an haɗa document kuɗin shi daban. Amma mai son sai an gama zai iya biya ya jira.
Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.
Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 300fcfa posting, document kuma 600fcfa.
*Seemahwrites ✨*
*REINA 💍*
Book 1
Saliha A. Na'ibi (seemahwrites)
_Women of words writers association_
40(End)...... Kaman ta san abinda ke zuciyar kamalu kenan, kuma yana da niyyar tunkarar Halime da zancen amma ya rasa ta inda zai fara don haka shi hanya tayi mishi.
"Ta bani gadon ta kaman yaya? Ni ban kare mata dukiyar ta ba sai in karɓe?" Ya kintime fuska yana watsa ma Talatu harara, Halime sai faman murmushi take kawai.
"Au, wai na san hali ne shiyasa."
"Ni bani son haɗa wuri, haka zaku ganni ku barni da ƙanwata, idan tayi niyyar ara min dukiyar ta don in nima na kaina laifi ne?" Shanya baki kawai talatu tayi tana kallon shi, na sakwan guda ta ɗauka Kamalu sauya hali yayi.
Sai ya juyo ya dubi Halime "Ko bari na zaki yi in yi ta fama bayan jarabawar da ya faɗa min Halime na?" Ɗago idanun ta tayi ta zuba mishi, tun kafin ya isa wurin da yake son zuwa ta harbo jirgin shi, amma kaman buƙatar tashi tayi wa sikelin kyautatawar ta nauyi.
Sai ya saka fuskar tausayi ƙwalla na taruwa a idanun shi, ya riƙo hannun ta biyu cikin nashi ya ɗan matse su yanda zai yi saurin narka mata zuciya.
Talatu dai tana zaune tana kallon ikon Allah, ƙarshen sakarcin Halime take son gani a yau, idan har zata iya saka rayuwar ta a kwale-kwale saboda son zuciyar Kamalu.
Ya ci gaba da cewa "Ga mata da yara ko sana'ar riƙe su bani da shi, ki taimake ni ƴar ƙanwa ta kin ji? nayi alƙawarin zan dawo miki da abinda na karɓa harda riba a kai wallahi, kuma ba zan yi miki wasa da gado ba, wannan da ya faru ma tsautsayi ne."
"Toh zan faɗawa Inna" ba ƙaramin tausayi ya bata ba .
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Talatu ta tafa hannuwa cike da al'ajabin jin yanda ta amsa kai tsaye.
"Halime! Hankali wala ko?"
Murmushi mai sauti tayi tace "toh Addah meye amfanin kana da shi idan ɗan uwan ka na cikin wahala? Ko rayuwata yaya ya buƙata zan bashi bare abin duniya mai ƙarewa"
Ta jinjina kai. "Allah ya kyauta" kana ta zaro kuɗi bandir ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ta zare guda biyu ta miƙa ma Halime, ta karɓa tana nanata godiya.
sannan ta zari wani biyun ta miƙawa Kamalu.
"Haba ke kuwa talatuwa na? Yi haƙuri ki ƙaro wasu biyun ko ki bani aron ko dubu biyar ne, Allah zan maida miki cikin ƙanƙanin lokaci" ya yunƙuro kaman zai fisgi sauran daga hannun ta.
Tusa kuɗin ta tayi cikin jaka ta maƙale shi a hammata domin idan bata yi da gaske ba bazata fita da su daga ɗakin nan Lafiya ba tunda Kamalu ya gani.
"Ka gani kuɗin hayan gona ne aka biya ni bana ban samu damar yin noma ba shiyasa ba wasu kuɗaɗe bane a wuri na. ka samu ma tunda kai duk shekara ko abin naira 50 baka iya yiwa kowa a cikin mu" ta harare shi.
"Allah ɗawainiya ne yayi min yawa abinda nake samu ko nima bayi isa na, amma na samu mai yawa kema kin san duk zaku ji daɗi"
Haka yayi ta mata magiya bata bar ɗakin ba sai da ta samu kanta da ƙara masa wani dubun.
Ta miƙe tana yatsina fuska "Sai kace wani ne ya ɗaura maka! Ka san ba zaka iya ba ka auro su?"
Bai ce da ita komai ba tunda dai ta bayar, tayi masa sallama da Allah ya ƙara sauƙi ta bar ɗakin sannan ya koma lallaɓa Halime, a ƙarshe dai bata bar ɗakin ba sai da ya karɓe dubun wurin ta kafin nan.
Ta ji nauyi sosai kafin ta tunkari Inna da buƙatar Kamalu, bata ƙi tata ba tunda yace aro ne kuma juyawa zai yi amma tace ta bari ta shawarci ƴan uwanta tukunna.
Ko da wasa basu amince da zancen ba, yarinya marainiyar Allah gashi a ko wani lokaci Allah ya kawo mata miji zata yi aure shine zasu ɗauki sauran abinda ya rage mata su bawa wani gardin banza?.
Halime ta samu Kamalu ta faɗa mishi yanda aka yi, Bai tsammaci hakan ba domin har kasafin yanda zai yi da kuɗin yayi, har ya samu masu siyan dabbobin Halime da ɓangaren su da take kiwon ma.
Kamalu ya shiga tashin hankali sosai, ya dinga jigila ma Inna da Halime har wurin yayun innan sai da yaje suka fatattake shi amma bai haƙura ba.
Sai gashi da wasu mutane wanda ya samu zasu dinga sarin shinkafa a hannun shi suna fitarwa kudu ga uban riban da zasu samu saboda kayan abinci ya fi tsada ta can.
Babu yanda Inna da Halime suka iya haka Kamalu ya danne su suna gani aka fice da dabbobin Halime ko ƴar kaza ba'a bari ba. Wurin da aka yi kiwon ma ya je aka yi mishi takarda ya zo ya tursasa su suka saka hannu wani sabon ango ya bashi kuɗin sannan ya shiga kwaskwarima ma amaryar shi.
Ya dawo babu Abinda suka tsira da shi bayan ɗakin da suke kwana a cikin ta, ga hanyar samu lokaci ɗaya ya tsaya musu, don ma ƴan uwan Inna masu ƙoƙari ne, su suke ciyar da su shiyasa Halime ke tsammanin nata ƴan uwan ma zasu kasance haka.
Kamalu aka shiga business ɗin shinkafa fakafaka kuma da gaske ana samu ɗin. Domin ba zallan nashi mutanen suke karɓa ba, tireloli suke cikawa suna kaiwa kamfani a gyare su a siyar a farashi mai kyau.
A hankali ya dinga taro musu mutane ana bashi kwamisho, kusan duk manoman shinkafa a Jama'are dama masu zuwa garin su hayi gona suyi shuka duk suka koma bawa kamalu amfanin gonan su saboda lokaci ɗaya za'a biya ka kuɗi a dunƙule kuma suna kamanta siya da daraja, kan kace mene farashin abinci ya fara hauhawa a Jama'are saboda kowa ma siyarwa yake yi wa masu kuɗi, don haka suka bunƙasa kasuwar su zuwa sauran ƙauyuka da suke makwaftaka suma ana saye nasu.
Da suka fara aminta da shi sai ya buƙaci yana bin su, da alƙawarin zai yi musu hanyar bandan kifi shima.
Allah mai azurta wanda yaso ba tare da hisabi ba, sai ya saka ma niman Kamalu albarka wanda ya fara shi da dukiyar marainiya da niyyar zalunci, domin har a cikin zuciyar shi bai ji cewa zai biya Halime kwanan nan ba, hala sai ya zamo wani hamshaƙin mai kuɗin tukunna.
Halime na cika shekara 15 wani ɗan makwafcin su ya turo tambaya. Basu bada rana ba sai da suka tambayi Kamalu da yanzu zaman Jama'are ya fara gagaran shi. Ya faɗa musu a saka babu matsala zai yi ma Halime duk wani abun buƙata, shi da kan shi ma ya bada lokaci aka saka tunda a yanzu shine waliyyin ta, sannan bayan kwana biyu ya ƙada bujen shi yayi garin plateu, domin wani sabon kasuwancin ma'adanai ma ya buɗe musu ta can.
Lokacin biki ya ƙarato, samun Kamalu a waya yayi wuya ma Inna, ko da ta tuntuɓi iyalan shi ma suma shaida mata suka yi rabon su da shi tun tafiyar shi sai dai ta samu Maman ɗahiru hala.
Haka ta ci gaba da haƙurin jira har sai da biki ya kasance sauran sati guda Halime ko buta ba'a siya mata ba kafin Inna tayi ƙarfin halin tunkarar Amaryar shi ƴar cikin ta, ta roƙe ta da ta kira mata Kamalu, cikin Sa'a kuwa ta same shi saboda da ya canza layi ma ita kaɗai ya bada lamba, harƙan tonan kuza ya shiga sosai a jos kuma yana gane mishi don haka shi ko ranar dawowa gida ma bayi da shi.
Ya dinga rantse-rantse ma Inna da ta tuhume shi da alƙawarin shi da kan shi zai ɗauki halime suje shagon kayan ɗaki a Kano ta zaɓi wanda take so tunda akwai kuɗi yanzu ba sai an yi wahalar jiran kafintoci ba.
Inna ta yarda da shi, cike da jin daɗi taje ta sanar ma ƴan uwan ta suma suka yarda har da taya ta murnan za'a yi ma Halime kayan ƴan gata. Itama Halime ba ƙaramin daɗi taji ba sai ta sami kanta da taɗa ma ƙawaye don haka kowa ya zuba idanun gulma a kan bikin ta.
Sai dai har an fara shagulgula babu Kyallin Kamalu ko wani aika daga gare shi. Har kiran maman ɗahiru ya daina ɗauka, ya ce dai ta faɗa ma Inna ko a ranar bikin ne dai zo musu da komai ayyuka ne suka yi mishi yawa a yanzu.
Sun fara sarewa don haka aka haɗa abinda ya samu daga gudumawan ƴan uwa aka siya ma halime abinda ya samu da fatan Kamalu zai cika alƙawari.
Ƙarshe dai ƙanin shi mai bin shi ne ya bada auren Halime kuma har yamma basu fidda tsammanin ganin Kamalu ba har saida aka zo tafiya da ita ɗakin ta.
Ƴan gulma sunyi har sun gaji, Halime da mahaifiyar ta sun yi kuka har sun gode ma Allah. Haka aka kai ta ɗakin miji daga katifa sai laidar tsakar ɗaki da ƴan robobin aiki.
Tukwanen girki ma ba'a iya siya mata saiti ba saboda gudumawar ƴan uwan inna da shi aka ciyar da ƴan biki.
Wannan ya wuce, Kamalu da ya tashi dawowa bayan shekara guda bai zo ma halime dake ɗauke da cikin wata tara da komai ba bayan kalmar haƙuri a kan harshen shi, sai kuma alƙawuran da ya rubuta su a kan ruwa, bai sani ba dai ko Halime tayi ma ruwan kallon tawada ne don ya gani a cikin idanunta ta yarda da shi.