Sashe 48
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu Yaseer ya dunƙule ya fara kai mishi naushi ba tare da ya shirya ba, ya kuwa same shi a fuska babu ɓata lokaci jamal dake cikin maye ya zube a ƙasa.
Sai yanzu ya fara dawowa cikin hayyacin shi ya rarrafa zai bar ɗakin Yaseer ya ɗaga ƙafa zai tokare shi sai Jamal ya riƙe kafar ya tura shi baya da iya sauran ƙarfin da ya rage mishi Yaseer ya bugu da bango sannan Jamal ya mike yana tangaɗi ya bar ɗakin kafin Yaseer ya samu kan shi.
Yayi niyyar bin shi a baya ya ci gaba da dukan shi, yayi niyyar ya kama shi tsamo-tsamo ya tona mishi asiri a idon iyayen shi da kuma mahaifiyar ta, amma ba zai iya tafiya ya bar Reina a cikin wannan yanayin ba, don haka sai ya dawo ya tsuguna a gaban gadon yana girgiza ta shiru.
Fuskar ta ya shiga bubbugawa yana kiran sunan ta da ƙarfi ko zata dawo cikin hayyacin ta, ya miƙe da nufin shiga toilet ya ɗibo ruwa ya shafa mata ta farfaɗo.
Juyawar da zai yi sai yayi gamo da katar.
Alhaji Tahir tsaye a bayan shi.
*Seemahwrites ✨*
*REINA 💍*
34.....koda ace yana fuskantar ƙalubale a kasuwanci, yanzu ya samu ya haɗa kan iyalan shi zai samu sauƙi ta wani wurin.
"Likita babu matsala dai ko?" Alhaji Tahir ya tambaya ganin a yau ɗin sun ɗan riƙe shi ya daɗe. Shi bayi da lokacin zuwa general checkup ma banda matsawar Hajiya Fauziyya, tun wata biyu da suka wuce ya kamata ace ya zo.
"Eh toh, BP ɗin ka ne ya ɗan haura gaskiya, sikarin jinin ka ma ya faɗi sosai, amma idan sauran sakamakon sun fito zan kawo maka gida a duba"
"Toh shikkenan, ni zan iya tafiya kenan"
"Zaka iya tafiya, amma Alhaji ka samawa jikin ka hutu ko yaya ne idan ba so kake yi ya baka kunya ba, zuciyar ka ma haka, sannan ana samun abincin da ya kamata a kan lokaci. Muna rawa da bazar ku Alhaji muna so kuyi ƙargo" ya karashe da raha Alhaji Tahir ya ɗan yi murmushin yaƙe sannan ya miƙe a kan dugadugan sa da suka yi masa nauyi, yayi sallama wa doctor.
"Shikkenan sai nazo Alhaji, a ƙara gaida min ƴata da jiki"
Kallon rashin fahimta yayi masa. "Waye kuma babu lafiya a cikin su?"
"Ah ah, baka sani ba? Hafsatu ce har saida aka yi admitting ɗinta"
Babu ɓata lokaci ya koma ya zauna doctor ya shiga masa bayanin abinda ya samu Reina.
Kafin ya gama Alhaji Tahir ya rasa ina kan shi yake.
Shine kuma Fauziyya bata sanar dashi ba, wannan abu mai girma haka.
Miƙewa yayi a fusace zai bar ofishin, jirin da ya ɗibe shi ya saka shi ƙoƙarin faduwa, da azama doctor ya riƙo shi ya saka shi komawa ya zauna dole.
Bai samu barin asibitin ba saida ya sha ruwa laida guda shima don ya samu ƙarfin zuwa ya sauke ma Fauziyya buhun bala'i ne ya saka shi ya jure ya jira.
Daga Asibitin ya ɗauki hanyar gidan Alhaji Salisu, ba zai iya jira sai ta dawo gida ba.
Wurin karatun su Reina ya fara dubawa, bata nan haka ma malamin su, ya juya zai nufi cikin gidan lokacin da ihun ta ya shiga cikin kunnen shi.
Tsoro ya kama shi, kada ace yau ma Fauziyya ƙoƙarin kashe masa ita take yi.
Jamal da ya fito a guje, ganin su Hajiya Fauziyya da mahaifiyar shi suna fitowa ya shige ɗaki mafi kusa dashi ya rufo ƙofa.
Zarah dake kwance a gadon ta tana kallon series ta miƙe a firgice zata yi magana yayi saurin ƙarasawa ya rufe mata baki ga idon shi ɗaya zuwa kumatun shi da ya tara jini.
A hanya Hajiya Fauziyya suka yi kiciɓus da Alhaji Tahir amma dake ba ita bace damuwar shi a lokacin ya tunkari ƙofar da bai gama rufuwa ba sanadin kiran sunan Reina da yaji ana yi a ɗakin.
Ya ƙarasa ya wangale ƙofar, a nan yayi mummunan ganin da ya daskarar dashi a wurin ya gagara motsa koda ɗan yatsan shi.
Ƴar shi ce kwance magashiyyan rigan jikin ta ya ɗage zuwa ƙirji sannan babu wando a jikin ta sai kuma wanda ya gani a wurin yana taɓa ta.
Maganar da likita ya faɗa mishi ya shiga mishi yawo a kunne lokacin da Yaseer ya miƙe da niyyar guduwa ko ɓuya yana da yaƙinin ɗayan biyun su tunda ya hallaka mishi yarinya.
cikin rashin Sa'a suka yi ido huɗu.
Daman wannan la'anannen yaron cutarwar da yake mishi kenan? Yana yi kuma yana biyan shi?.
Tsoro zahirin shi ya bayyana a cikin idanun Yaseer kaman ba shi bane ranar da yazo yana roƙon shi alfarma a darajar Hafsatun yake masa kallon banza, ashe kashe masa ita zai yi.
Yaseer sai ya rasa da wani irin kalma ma zaiyi amfani ya kare kan shi.
Ya taka sawun ɓarawo, Allah kaɗai zai iya fidda shi.
Gwada Reina yayi yace "bata numfashi ne...." kamata yayi ya damu da kan shi ya nemi hanyar tsira.
"Ku taimaka mata Alhaji"
Su Hajiya Fauziyya da sauran mutanen gidan sun ƙaraso don ganin mai yake faruwa. Dukan su turus suka yi a bayan Alhaji Tahir banda Hajiya Fauziyya da ta fashe da kuka haɗe da salati, ta bankaɗe Alhaji Tahir a kan hanya tayi kan reina ta shiga jijjigawa.
Sai Yaseer ma ya juya zai shiga taya ta lokaci ɗaya yaji an finciko shi, bai sake ganin komai ba bayan koriyar wutar da ta ɗauke ganin shi baki ɗaya sai duka kawai da ya shiga samun shi ta ko ina, hannun shi kawai ya ɗaura a ka yana tare na wurin tare da yin baya-baya yana ƙoƙarin faɗawa a gadon shima, Alhaji Tahir ya fisgo shi ya watsa shi a wajen ɗakin kaman kayan wanki sannan ya rufa mishi baya, yana ƙwala kiran masu gadi.
Suna isowa babu tambayan ba'asi suka rufu a kan Yaseer da duka tun yana daurewa har ya fara ihu da ƙoƙarin tserewa amma sun fi ƙarfin shi.
Da cikin jikin ta haka Hajiya Fauziyya ta cicciɓo Reina bayan ta suturta mata jikin ta tayi hanyar waje da ita, bata lura da hajiya Hauwa bata nan ba a lokacin, hakama Alhaji Tahir ko lura da su bai yi ba burin sa su kashe Yaseer kawai.
Sai da ta ƙarasa wurin mota drivern Alhaji Tahir ya ƙaraso da nufin karɓa mata ita tayi saurin ja da baya.
"Kada ka taɓa min ita! Kada ka kuskura ka taɓa min ita!!"
Komawa yayi ya buɗe mata bayan motan suka shiga suka bar gidan zuwa asibiti.
Su Alhaji Tahir ma sai da suka tabbatar sunyi ma Yaseer jina-jina bayi ko ƙwaƙƙwaran motsi kafin suka miƙa shi ma folisawan dake jira a waje hankalin su a kwance, sun san ko gawar shi aka kawo musu za'a biya su kuɗin da zasu binne shi babu wani matsala.
Haka suka tasa ƙeyar shi babu tausayi babu imani suka kai shi station suka rufe shi a cell.
Likitoci suka rufu a kan Reina, zuwa lokacin da Alhaji Tahir ya isa har ta farfaɗo anyi mata allurar bacci, Amma sai da suka saka mata oxygen don ko da ta farka numfashin ta bai daidaita ba.
Saidai kuma naƙuda ne ya taso ma Hajiya Fauziyya gadan-gadan, ko da ta iso ita ta shigo da Reina har emergency, taƙi yarda kowa ya karbe ta, tana ajiye ta ta zube itama aka rufu ceto rayuwar ta.
Zafi ya haɗu ma Alhaji Tahir goma da ashirin sai can jimawa Kafin Alhaji Salisu da Hajiya Hauwa suka ƙaraso.
Abinda ya faru kuwa shine, Hajiya Hauwa da ta ga giftawar Jamal zuwa ɗakin Zahra da suka fito, sai ta bari har sai da hankalin kowa ya karkata kan Yaseer da Reina kafin ta saɓule jiki taje ta buga musu ƙofa.
Zahra dake a tsorace tayi yunƙurin buɗe kofar Jamal ya hana ta, har saida Hajiya Hauwa tayi magana ta umarce su su buɗe kafin ya barta.
Itama tana shiga ta turo zahran waje kana ta sake sakawa ƙofar key ta tunkari Jamal da shima ya miƙe ya nufo ta jikin shi na kyarma.
"Wallahi Umma ban yi mata komai ba Allah" ɗauke shi da gigitaccen mari tayi, zai kai ƙasa ta riƙo shi ta sake kai masa wani.
"Kai bunsuru ne?! Ba nace ka fita a harƙan yarinyar nan ba?! Sai ka jawo mana bala'i ko?!"
"Wallahi Umma ban yi mata komai ba." Kuka yake yi wiwi.
Yaci gaba da cewa
"Tsorata ta kawai nake son yi saboda ta fara fallasa ni ma wancan jakin yaron, na gwada mata zanyi mata mai zafin shine kawai ta sume min shi kuma sai gashi ya shigo"
Wani ɓari na hankalin ta taji ya kwanta, tana da tabbacin Hajiya Fauziyya bata san da zancen ba har yanzu balle Alhaji Tahir, kiran Alhaji Salisu ta fara yi yazo su san na yi kana ta umarce jamal da ya zauna a ɗakin kada ya fito har sai ita ta dawo ta fito dashi da kanta, daga ƙarshe ma kawai sai ta cire key ɗin ta rufe shi ta waje, hankalin ta zai fi kwanciya.
Lokacin kowa ya watse sai yara da suka haɗa kai suna kuka a parlour da kuma jinin Yaseer da ya ɓata tiles inda suka buge shi.
Babu daɗewa Alhaji Salisu ya ƙaraso, bata bar shi ya fito daga mota ba ta shiga suka nufi asibiti a hanya tayi mishi bayanin komai kuma hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba saboda shi bayi da masaniya kwata-kwata, yayi alƙawari Hajiya Hauwa ta kuskura ita da ɗan ta suka jawo masa matsala a business ɗin shi da Tahir itama ba zata tsira ba, sai yaga bayan ta da duk dangin ta.
Likitoci sun tabbatar da Jamal bai yi nasarar cutar da Reina ba, yayi ƙoƙarin shigar ta da ƙarfi amma suman da tayi shi ya ceceta, amma labarin da ya samu na Abinda ya faru ya saka shi ya ɗau alwashin ko duniya zata tashi sai ya rufe Yaseer, Alhaji Salisu na daga gefe yana daɗa masa famfo domin daga an rufe shi shikkenan asirin su ya rufu.