← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 57

Sashe 29

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin Alhaji tahir ɗin da ake jira ya fito yana gyara hula. "Mu tafi ko?!" Yace da su ba tare da ya zauna ba don lokaci ya riga ya tafi suna zaman jiran shi bai dawo ba, yanzu ma a gaggauce ya watsa ruwan ya shirya kuma da ya ga tashin su bakin aiki zai koma duk dare.

Ko dan saboda kasancewar shi a wurin Hajiya Luba bata fasa maida wa Fauziyya martani ba "Banda abin ki yara nawa na Raina na aurar sai ƴar ƙaramar yarinya ce zata gagare ni? Kada ki ji komai, za'a kula da ita fiye da idan kina nan, kuma za ayi mata abunda bata samu a nan ma, idan kika dawo sai kin sha mamaki."

"Allah yasa" ta amsa lokacin da Alhaji Tahir yazo ya ja akwatin ta zai fita da shi. Ta sumbaci Maama hawaye na ƙwace mata don haka ta wuce ba tare da ta sake ma Reina kallo na biyu ba, haka sauran mutanen suka rufa musu baya suna musu bankwana.

Amma da Hajiya Lubabatu ta sani da bata yi kalamin tabbatarwa a kan Reina ba, domin bala'in da zata takalo mata Allah ne kaɗai zai iya magance mata don tabbas sai ta faɗa ciki tsamo-tsamo.

......

"Sai me za'a wanke kuma Umma?" Yaseer ya tambaya yana zama a kan bokitin fenti da ya gama shanya bargunan ciki wanda ya wanke, yana haki sama-sama.

A kaikaice ta kalle shi cikin gatse tace "Saura ni! Tun da ni kaɗai ne abu mai dauɗa da na rage a gidan" kana ta mayar da hankalin ta kan ƙafar Sabir da take yanke wa farce da reza.

Ɗan ciza labben shi na ƙasa yayi yana murmushi, abunda ya zamo masa ɗabi'a musamman idan yaji kunya ko ɓacin rai.

"Toh ai Umma ke ɗin ma idan kina so zan iya wankewa"

Hannu ta kawo da nufin mangaje shi yayi saurin kaucewa yana dariya, daman ya tsammaci hakan.

"Allah Umma zaman hakan ne ba daɗi, ashe ma gwanda idan mutum na zuwa makarantar" ya riƙe igiyar shanyar daga yanda yake tsaye don yana tsoron ya koma kusa da ita bata gama hucewa ba.

"Toh kaga da Abban ka bai hana ka koyan sana'a bane, da sai dai ka buƙaci lokaci amma ba dai yayi maka yawa ba"

Matse bakin shi yayi alamun bayi son tankawa a kan maganar. Ta kalle shi ta girgiza kai kafin ta ci gaba da cewa.

"Kuma ai abun yi bayi ƙarewa, ka shiga ka ɗibo mana shinkafa da yawa mu gyara shi, kaga mun rage aiki daga an ɗiba sai dafawa"

"Toh, ni dambu ne ma nake son ki koya min"

"Dambun tsaki ko na shinkafa?"

"Ko wanne, inaga yanzu shi kaɗai ne ya rage mun ban iya ba. Amma tuwo idan na tuƙe shi ko goggo albarka" ya ƙarashe da alfahari.

"Lallai fa ma Abban ka zan faɗa ma wannan zance ya sanar ma goggo"

Dawowa wurin zaman shi na ɗazu yayi yana faɗin "ki rufa min asiri Umma dan Allah, kada idan naje hutu taji daɗin girki ta hana ni dawowa"

Suka saka dariya harda Sabir kafin Saudat tace "kaga yanzu yayi wuri, sai ka bari zuwa an gama gyaran shinkafar kaje ka siyo kayan dambun, ka roƙi Danejo ta sammana zogale sai ka tsinko"

"Muma dai da shuka ta muka yi zogalen nan Umma. Tunda akwai wuri har biyu ma zamu iya dasawa"

Ɗage kafaɗa tayi "ga fili ga mai doki Yaseer, ai gidan ku ne ba namu ba"

Yanzu kam miƙewa yayi don ya wuce yin abinda ta umarce shi.

Ya ƙanƙance idanun shi yayin da ya ɗaga kai zuwa ga kwallon Ranar da ta haske Safiyar Litinin, gajimare masu haske da masu duhun launi mai kyau suka yi mata ado abin burgewa. Bata da zafi kasancewar yanayi na sanyi da ya fara shigowa, Amma hasken ta ya wadaci ko ina, ta haske ƙwaƙwalar mai niman ilimi, ta haske zuciyan mai niman dukiya.

Miƙa yayi tare da lumshe idanu ya fitar da ɗan karamin gurnani, sai yanzu ya fahimci ashe durƙeshen da yayi ya saka bayan shi yayi tsami.

"Yauwa Umma dan Allah in je kwallo da yamma?"
Bata cika son zuwan shi kwallon ba dan haka har a zuciyar shi ya raya idan ta hana shi ba zai je ba. Shi ba kaman Suhail bane mai satar hanya.

"Allah ya kaimu yammacin"

......

Kwana biyu, kwana biyu kacal Amma Hajiya Luba ta gama gajiya da tsirface-tsirfacen Reina.

Ga iyayi gashi bata iya zama wuri guda, gidan kuma ba ƙananun yara suke da shi da yawa ba sai yaran kishiyar ta da ko ɓangaren ta basu takowa amma har shashin uwar su Reina ke zuwa ta nemo magana, idan an taɓa ta kaɗan kuma tazo wa mutane da ihu da kuka tana zage-zage.

"Ba zaki ci indomie ɗin ba?" Hajiya labatatu ta tambaya takaicin ta na daɗa kama ta.

Girgiza kai tayi tare da zumɓuro baki ta tura mata bowl ɗin.

"Toh kici ko ƙoyin dan Allah"

Ta sake maƙe kafaɗa "o'o bani sho"

"To me kike so ki ci?"

"Froot Loopsh" tace tunowa da aunty tayi mata kashedi a kan cake amma da cake ɗin zata ce.

"Menene Froot Loopsh kuma ni Luba?"

Yarinyar ta dake gefen ta na hagu ne tace "wani cereal ne, amma wallahi sai ki zagaye garin bauchi kaff ba zaki samu ba, ba ma a ƙasar nan ake yin shi ba. Bari ki gani"

Tayi minimizing ta fita daga abinda take yi sannan tayi mata browsing ɗin sunan Froot loops ɗin sai ga hotunan shi sun fito.
"Kin gan shi"

Ta gwada mata abun masu kala-kala, zobe-zobe.

Hajiya luba ta riƙe baki tana sallallami. "Toh a ina kenan ake siyarwa in saka a samo mata"

Ta kalle ta da mamaki "taɓɓ, Hala Abuja ko kano za'a samu. Amma Wallahi mummy kada ki ɓata lokacin ki a kan wannan abun, ki bata abin da kike da shi idan bata ci ba cikin ta."

Murguɗa baki uwar gayyar tayi tace "Ni ba wannan abun bane shunana Hafshatu Reina Tahir Tk Kingdom"

Tsaki tayi "Shegiya da dogon baki kamar aku"

"Ni ba shegiya bane, sai dai in ke!"

A zafafe ta miƙe zata kai mata bugu Hajiya Lubabatu tayi saurin tare ta "Rufa min asiri don Allah da Tahir, ban shirya tafka babban asara ba"

Nuna ta tayi da yatsa tayi ƙwafa kafin ta ɗauki wayarta ta wuce.
Sauran yaran basu ce komai ba don yanzu Uwar zata gwale su amma baki ɗaya haushin Reina suke ji Saboda shegen rashin kunya, idan kaga bata yi da kai ba toh baka shiga shirgin ta ba, shima sai dai idan taga alamun baka ɗaukan raini.

.......

"Saudatu ko dai na kuskure a hanya?" Tun da ya samo ƙarin bayani a kan farashin makaranta da kuma ɓangaren karatun da Yaseer ya cika ya shiga cikin damuwa. Ko dambun tsakin da aka ajiye a gaban shi ya gagara ci.

Tsura mishi idanu tayi, yanda yake ɗaga hankalin shi a kan lamarin Yaseer, ya ɗaura duk wasu mafarkayya da burikan sa a kan shi sai yake bata tausayi, amma tana tsoron kada kuma su ɗaurawa yaron nauyin da ya fi ƙarfin ƙirjin shi ya ɗauka.
"Sai mu ɗauki darasi mu gyara ta tun kafin ayi nisa. Faɗa min menene damuwan?"

Numfasawa yayi kafin yace "Wallahi da aka faɗa min kuɗin registration kawai na jami'ar da yaron nan ya cika sai da ciki na ya tsure, kuɗi samama Saudatu, ina zamu same shi?" Ya ƙarashe kaman zai yi ihu.

"Toh ai da sauran lokaci ko? Naga sukan yi watanni a gida kafin sakamakon jarabawar su ma ya fito tukunna azo zancen ɗiban sabbin ɗalibai. Sai mu tara a hankali, amma ya kai nawa haka kuɗin?"

"Hmm, duk da mutumin yace min bayi da tabbaci amma yana da yaƙinin kuɗin ya doshi dubu ɗari uku. Dubu ɗari uku Saudatu, ko tarawan muka ce zamu yi sai munyi watanni uku bamu ci ba bamu sha ba kafin mu tara dubu ɗari uku!"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un." Suka ƙarashe addu'ar a tare.

"Daman ka san makarantu a kudu sun fi arewan mu tsada, toh yanzu meye abun yi?"

"Wallahi ban sani ba, lissafi na ya cushe, bani da dubu ɗari uku bani da dalilin shi."

"Toh a haƙura da makarantar mana mu saka shi a wanda zamu iya, koda irin wanda kayi ne"

Yana cikin yanayin damuwa amma ba shi ya hana shi ɓata ran shi lokaci guda ba. "Allah na tuba ko babu na yafi haka sai in bar shi yayi poly?"

"Amma naga mutane ne suma wanda suke yin ko? Kuma ma ga makarantu muna da su a kusa menene sai an ɗauki yaro an kai shi cikin arna? Gaskiya ka canza shawara"

.......

Yau ta kama sallar layya, masu zuwa Masallaci sun je, sauran sun yi kwalliya sun ɗau hotuna sannan suka koma suka bi lafiyar gado.

Da gudu Reina ta fito ta ƙofar bayan dake kitchen, yanda zai sada ka da babban filin da ma'aikatan ke sarrafawa iyayen gidan su naman Sallah.

"Bibalo ki duba min kaskon nan, idan ya soyu ki kwashe ki zuba wani daga cikin wancan tukunyar" cewar Inna larai, tana cire dogon matsamin daga ciki kana ta jingina shi daga jikin kaskon.

Da toh bibalo ta amsa ta ci gaba da tuƙa tukunyar dambun ta, da niyyar sai an ɗauki mintuna kafin ta duba suyar.

Ita da ubangijin ta kawai suka san me take gujewa, sai kuma wanda tayi wa laifin. Tana gudu tana waiwaye taci wawan tuntunɓe da matsamin, wanda yayi sanadiyar tankwaro da kaskon daga kan murhu mai da naman ciki ya wantsalo sai a kafafuwan Ta.

Seemahwrites ✨

*REINA 💍*

*BookNest, Wattpad and arewabooks @ Seemahwrites*

21..... Idan azaba ta wuce fata, ta ratsa jijiyoyi, ta shiga cikin nama, ƙashi, da kuma ɓargon mutum, toh a cikin zuciya da ƙwaƙwalwa ake jin ta, gashi yarinta da hauka basu hana kuruwa cikin azaba.
Chapter 29 · 0% Book details