← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 57

Sashe 35

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh ba zan faɗa mata ba. Amma ka siya min harda cake toh" tace muryar ta na karyewa zuwa na kuka. taƙi ta bada muhimmanci ne ma abinda take ji yana tokarinta ta ƙasa amma kanta duk ya ɗaure da wannan yanayin.

Rungumo ta yayi jikin shi yace "shikkenan amma kada ki faɗa ma kowa irin wasan mu ko daddyn ki ko ƙawayen ki, duk wanda ya sani zai saka Auntyn ki ko Umma na su zane ki."

Ta gyaɗa kai da sauri, sai ya sauƙe ta ya buɗe mata ƙofa ta fito ɗauke da chocolate ɗinta ganin yanda ta gama firgita, yafi so ya bita a hankali ta saba da shi kada tazo ta tona mishi asiri.

Haka ta ƙare wunin gidan sukuku har Alhaji Tahir yazo bayan Isha ya ɗauke su.

.......

"Wallahi baka da hankali Tahir" ji yake yi inama da akwai halin ya kama shi ya naɗa mishi na jaki ko zai huta da takaici.

Dariyar da ya ƙara ƙular dashi Alhaji Tahir yayi kafin yace "Nine bani da hankali angon Mariama?"

Dogon tsaki yaja ya miƙe zai bar masa office ɗin kafin ya bashi mamaki.

"Tsaya kaji mana amini na"
Juyowa yayi a karo na ƙarshe ko akwai sauran notin kan shi da bai gama kuncewa ba yace.

"Tahir da kanka kake tona ramin mutuwar ka da hannun ka! Ka san Naira biliyan ɗari nawa ka zuba su a cikin wuta domin su ƙone? Da biliyoyin kuɗi ka sake shiga Ponzi Tahir? Kana hauka ne?"

Wasu takardu ya miƙa masa yana faɗin "karɓa ka gani"

Tsayawa yayi yana kallon shi yana harsaso masa irin matsalar da zai iya shiga a gaba.

Alhaji Tahir ya sake cewa,
"Karɓa ka gani sai ka yanke hukunci idan ina kan daidai ko akasin haka"

Ƙarasowa yayi ya karɓa yana dubawa. "Takardun meye wannan?"

"Riban da na samu ne a wancan karon, rabona ne ni kaɗai ba tare da kowa ba Abdou. Ka kalli yawan kadarorin da ya mallaka min"

"Toh sai anka yi yaya?"

"Tunda kai baka da niyyar amfanunwa da garaɓasa sai ka zama min wakili kuma mai riƙon wannan kadarori, ka bunƙasa min su in biya ka"

Watsa masa takardun yayi a kan fuskar sa tare da buga mahogany table dake tsakanin su yace "Tahir! Duk wani bala'in da zaka saka kanka ka kuskura ka nemi Abdou Hamissou wallahi sai na wulaƙanta ka yanda baka tsammani. Ni bani hidima da mutanen da basu da nazari da tunani, so as from today, Idan ba Abinda ya shafi kasuwancin dole ba kada ka sake nima na kafin nima ka ɗaura ni a hanyar da bata ɓullewa."

Alhaji Tahir ya san zai dawo, ya san zai yi nadama, ta yuyu shi ya fara tun yanzu shine yake naɗe tabarmar kunya da hauka, amma har malamai ya saka anyi mishi istikhara kafin ya shiga abun nan kuma an tabbatar masa da nasara don haka zaman jiran sakamako kawai zai yi.
.......

Zuwa yanzu bashi ya fara yiwa Kamal da Saudat katutu Saboda karatun Yaseer, saboda kullum cikin fidda fice ake yi buƙatar kuɗin yau daban na gobe daban, ga campus life sai a hankali.

Ga karatun Suhail, Sabir da Ajmal suma, ga kuma ɗan kuɗin da yake turawa ma Goggo a ƙauye, kuma ba'a fasa ci da sha da sanya sutura ba.

Rayuwa ta ƙara tsada, farashin kayan abinci kullum daɗa hauhawa yake yi, ga ƙarin albashin da suka samu a tsawon shekarun bai kai ya kawo ba. Sannan Saudat tun baya haihuwar Ajmal ta kamu da cutar Asthma.

Zauna suke a kujerun can ƙarshe na NLT yana gwada mata Physics 126 da ta samu carry over ɗin shi na aji ɗaya, amma wai sai yanzu da zata shiga jarabawar gyara shi gobe da safe zata zo ta dame shi ya koya mata, wanda shima gudowa yayi yazo nan ɗin yanda babu haske ya samu yayi karatun nashi exams ɗin.

"Kinga idan kika gama buɗe wannan, a nan sai ki ɗauko wancan formula ɗin kiyi applying ki ƙarasa solving"

"Umm" tace hankalin ta na kan zakarar wuyar shi dake lugude da duk kalmar da zazzaƙar muryar shi ta furta, zuwa kan kyakkyawar fuskar shi, a maimakon ta maida shi kan takardar ta.

"Toh solva mu gani" ya tura mata takarda da biron gaban ta amma sai ta ƙara matsowa daff da shi jikin su na gogan na juna.

Haɗe fuska yayi, yace "Meesha! Matsa"

Sai ta ɗago ta kalle shi. Suka yi ido huɗu, kaman ranar da ta fara ganin shi a makarantar, amma wannan karon sai ta sake mishi murmushi a maimakon harara. babu musu kuma ta matsa ɗin domin wannan hali nashi shi yasa yake ƙara burgeta kuma yasa ya shiga ranta.

Tana son namiji tsayayye, kaifi ɗaya, ba kawai namamajo wanda kowa nashi bane, kuma bata damu da talaucin Yaseer ba wanda yakan gwada a suturar shi da dabi'un shi, dukiyar mahaifin ta ya ishe su. Sannan ma ai yana da bright future a gaba, tana yin nasarar kama tashi zuciyar shikkenan daga ya gama karatu daddynta sai ya sama mishi aiki mai kyau suyi auren su.

"Uhmm... Yaseer!" Ta kira shi cikin siriryar muryar ta mai daɗi.

"Yaya aka yi?" Ya tambaya hankalin shi yana kan wayar shi da yake duba alert ɗin naira dubu biyu da ya shigo yanzu daga Abban shi.
pocket money ne ya ƙare mishi gashi an fara jarabawa don haka bayi da yanda ya iya dole ya tambayi Kamal kuɗi shine ya turo masa abinda ya samu. Baki ɗaya naira ɗari biyu da saba'in da biyar ya rage a account ɗin sai yanzu da wannan ya shigo.

Hankalin ta na kan wayar nashi don screen ɗin ba privacy bane tace "dama wata aunty na ce take neman lesson teacher ma yaron ta."

Ɗagowa yayi ya kalle ta "ni kuma sai aka ce miki charity foundation ne ni"

Dariyar ta mai kyau tayi tace "zasu biya fah, da kyau ma. Yaron ne dolo ne wallahi sau biyu yana rubuta jamb tun yana ss2 ya gagara ci, waec da neco ma rubuta mishi aka yi. Shine suke niman wani guru ya saka ka shi a layi ni kuma kai na sani."

"Okay, for how long suke buƙata?" Tambayar da ya mata daban amsar da yake nima daban, kuma ta fahimci hakan sai ta ciro iPhone 16 pro ɗinta da faɗin "bari na tambaye ta"

Danna kira tayi babu ɓata lokaci aka ɗauka suka shiga gaisawa "Aunty Hauwa ina wuni, daman maganar Lesson teacher ma Jamal da muka yi magana ne shine na sami wanda nake faɗa mikin ya yarda amma yana so ya san duration da kuma pay"

Cike da jin daɗi tace "sau biyu a sati ma yayi, duk weekends daga tara na safe zuwa sha biyu na rana sai kuma da yamma ƙarfe huɗu zuwa shida. Sannan ko na wata shida aka samu zai yi, idan kuma zai yarda har zuwa ya rubuta exams ɗin toh zamu fi son haka"

"Okay, salary ɗin shi fah"

"50 thousand ne."

Tayi saurin girgiza kai tare da yatsina fuska kaman tana gaban ta tace "50k yayi kaɗan Aunty hauwa, kiyi doubling ɗin shi gaskiya. Na faɗa miki guru ne sosai nima shi yake koya min karatu"

"Toh shikkenan Meesha, sai ki turo min numbern shi shima ki bashi tawa"

"Okay no problem, amma fa muna exams sai mun gama zai fara zuwa. And idan aka samu ƙarin student ko ɗaya ne gaskiya sai an ƙara masa kuɗi"

"Baki da matsala dani Meesha, indai zaiyi abinda ake so kuɗi ba matsala bane" da haka suka yi sallama.

Ta juyo wurin Yaseer da yayi ƙoƙarin rufe bakin shi kafin ta fahimci tsananin mamakin da yake ciki.

"You're hired. The pay is 100k sau biyu ne duk weekends, sai ka tura min account details ɗinka in tura mata"

Da ƙyar ya iya buɗe baki yace "last week na buɗe opay."

Danne danne tayi na mintuna biyu sai ya sake jin alert yana dubawa yaga 30k ne ta tura masa.

"Wannan kuma na meye?" Ya tambaye ta mamakin shi yana ƙaruwa.

"Baka yi kama da charity foundation ba, don haka ko ruwa ka siya da wannan ka jiƙa maƙoshi, sorry ba yawa semester yayi nisa"

Dama ta daɗe tana niman account number ɗin shi don tana tallafa mishi da wani abun amma yaƙi bata, kuma har opay da su moniepoint ta duba bayi amfani da su sai yau tayi nasarar cika ƙuɗurin ta kuma taji daɗin da ya kasance a lokacin da yake tsananin buƙata.

Idan Yaseer yace bai ji daɗin kyautar ta ba yayi ƙarya don haka yayi mata godiya cike da jin daɗi suka ci gaba da karatun.

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*

*REINA 💍*

25....... MAFARI.

_A cewar malaman falsafa 'wani lokaci zuciya na jin abinda idanu basu iya gani, sai daga baya a gane cewa ji ne na gaskiya'_

Amma Yaseer ya gagara fayyace abin da yake ji a tashi zuciyar fargaba ce ko kuma tsana.

Shekaru tara! Shekaru tara kenan rabon shi da wannan gidan.

Tun Haihuwar Sabir da ya rako umman shi yawon Arba'in aka barsu a waje kuma matar gidan ko fitowa su gaisa bata iya ba har suka ƙaraci zaman su suka tafi.

Tun daga ranar Saudat ko yaranta basu sake taka ƙafar su a cikin gidan ba, har hajiya hauwa ta aurar da yara uku, mata biyu da namiji ɗaya, sai a yau da buƙatar su ta tashi gashi sun nimo shi har inda yake sun gayyace shi ya zo gare su.

Riƙe yake da hannun ƙofar parlourn, yana tunanin ya shiga ne koko ya juya yayi tafiyar sa? Saidai kuma idan ya tafi asarar waye? Tunda dai ko ba shi ba ya san zasu samawa Jamal wani lesson teacher amma shi idan ba a nan ɗin ba a ina yake tsammanin samun kuɗi mai yawa haka a ɓagas?.

Da kuzarin shi ya tura ƙofar haɗe da sallama.

Alhaji Salisu ke zaune saman kujera mai zaman mutum Uku yana kallon tashar BBC, sai kuma waya da yake amsawa a lokaci guda.
Chapter 35 · 0% Book details