← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 57

Sashe 52

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar mutum a cell koda bisa kuskure ne ba abin alfahari bane don haka sai Kamal ya sami kan shi da mishi ƙaryar sun yi accident ne ya faɗi a mashin saboda idan sun gan shi ya dawo da raunuka su fahimta.

Yayi musu Allah ya sawaƙe da alƙawarin zuwa yamma zai shigo ya duba shi.
Yana da yaƙinin zuwa lokacin an sake yaseer ya dawo gida, ya amsa da toh sai ya zo ɗin.

Cikin ƴan karɓan gaisuwan dake waje suka samu Kamal, ya ƙaraso wurin su don shima bai samu ganawa da Alhaji Tahir ɗin ba sannan ya jagorance su suka shiga ciki a tare.

Suna haɗa idanu da Alhaji Tahir ya fara ɗaga mishi hannu ya koma inda ya fito daman yasan zasu biyo sawu kuma ko duniya zata tashi a kan lamarin nan ba zai saurare su ba.
Kamal ya ja ya tsaya kawai yana kallon shi har Saudat ta shigo, goggo biye da ita.

Amma ko da yaga ƙanwar mahaifin shi, bai fasa musu alamun su koma ba, sai ma miƙewa da yayi a kan ƙafafuwan shi.

Goggo ta karɓi jagorancin tayi gaba zuwa gare su sannan ta rage tsayin ta ta gaida su, Saudat ta mara mata baya.
Ganin Alhaji Tahir ya ɗaga kai bai amsa ba yasa tayi mishi nashi gaisuwan na musamman.

Yaya haƙuri fa suke tambayar shi? Bayan ɗan su shi yayi sanadin da ya rasa Fauziyya! Bayan shi ya lalata Hafsatun da duk burin shi na duniya ya gama ɗaurawa a kanta, amma shine basu ji kunyar gwada mishi munanan fuskokin su ba?!

"Goggo! Kafin in yi miki abinda ba zaki iya ɗauka ba don Allah ku fice min a gida!"
Da ace bai ga wannan baƙar safiyar ba, da ace Fauziyya bata wurin, da ace bai danƙa amanar Hafsatu a hannun la'anannen yaron nan ba, wataƙil da yanzu Fauziyya tana ɗan hidimomin ta na cikin gida da bata gajiya da shi da cikin magajin shi a jikin ta, amma asarar da suka jawo mishi ba ɗaya ba har biyu, kar ma aga laifin duk abinda zai yi musu.

"Ɗahiru komai rikicin Duniya mutuwa tafi ƙarfin shi. Kayi haƙuri ayi addu'a wa mamaci komai zai iya zuwa daga baya"

"Goggo ki rufa ma tsufan ki asiri don Allah ki ɓace min da gani, darajar ki da ya rage a idanu na yasa ban haɗa da sauran yaran ki na rufe ba, don haka ki tafi kawai na gargaɗe ki"

Miƙewa Alaji Abdou yayi ganin kaman mutuwa ya zautar da Tahir ɗin ya riƙo shi ya juyo da shi.
"Yaya kaman bakka da tunani Tahir, damuwa batta saka hauka fah, ka natsu!.

Cikin ɗaga murya don ya fusata ganin Abdou ya san komai amma laifin shi yake gani yace "Wallahi ko ku fice min a gida ko in saka ku ma azo a fitar min da ku. Mutanen banza kawai wanda basu san halacci ba"

Goggo sai ta murmusa kawai don kalamin shi na ƙarshe ya bata dariya. Da ace Uban shi Kamalu zai iya tasowa daga kabari ne toh zai sanar da shi wanene ainihin wanda basu san halacci ba.

Meesha da ta samu fitowa tare da sauran mutane ta ƙaraso gaban goggo ta tsaya ita a dole shamaki take mata tsakanin ta da Alhaji Tahir domin tunda ta gan su tare da Saudat toh tabbas dangin Yaseer ne.

"Wani shaida kake da shi da zaka rufe ɗan mutane wanda bai ji ba bai gani ba? Don kawai zaka iya? Ko don kana ganin bayi da gata?"

Alhaji Tahir yayi mata kallo ɗaya sannan ya ɗaga murya ya fara kiran security wanda suka nufo su da hanzarin su.

"Kada ku kuskura ku taɓa su Wallahi" Alaji Abdou ya tsawatar tun kafin su ida ƙarasowa.

Ga su Alhaji kalabu da Alhaji salisu a wurin amma an rasa mai tsawatar ma Tahir, wannan wacce irin rayuwa ce?!.

......

"Wallahi babu inda zan je. Ai ni na kawo muku shi" Meesha ta shiga tirjewa ta ƙwace kanta a hannun Hajiya Hauwa dake ƙoƙarin fitar da ita daga parlourn da ƙarfi.

"Rabu da ita Hauwa, ai itama laifin ya shafe ta tunda haka ne" cewar Alhaji Salisu sannan Hajiya Hauwa ta sake ta tana wurgin ta da harara.

Alaji Abdou ne ya miƙe bayan kowa ya zauna ya fuskance su yana tunatar dasu a irin yanayin da ake ciki ganin kaman sun manta, Fauziyya ko kwana bata yi a cikin kabarin ta ba tukunna, addu'a ya kamata suke mata ba rikici ba, ya ɗan yi musu wa'azi mai razanarwa a kan mutuwa don su farga, koma menene a warware shi cikin lalama.

"Yanzu goggo mai yake tafe da ku?" Alhaji Kalabu ya tambaya bayan jikin kowa yayi sanyi.

Numfashi ta furzar sannan ta fara magana. "Taaziyyar muka zo yiwa Tahir kaman kowa a nan saboda tabbas yayi babban rashi. Amma tunda abin har ya kawo haka bari kawai ayi ya wuce."

Sannan ta dubi Tahir "ka sani, ba zallan shekaru bane suka tsufar da ni. Haƙuri, sanin ya kamata da kuma hangen nesa suna daga cikin abinda ya kawo mu har wannan lokacin nake zaune a gaban jikoki na. kuma ni Halime ban yi ma tsatso na horo da ɗaure ma ƙarya gindi ba.
Saboda ka hukunta Yaseer a kan dai-dai da ba dai-dai ba ba zai saka na tako ƙafa na gidan ka har ka ga dama na ba ɗahiru. Amma abinda kuke zargin shi da shi ba ƙaramin abu bane har a addinance, don haka muna so mu san da wani hujjoji ka kama shi ka saka a kulle shi, don idan yana da laifi mu masu goya maka baya ne ka saka doka ko wani iri ne tayi aiki a kan shi"

Cikin jin daɗi Meesha tace "yauwa! Tambaye shi kam goggo."
Hajiya Jummai dake ɗaya gefenta ta ɗane mata baki, Meesha ta ja mata Allah ya isa a ƙasan maƙoshi.

Tsoro ya so kama Hajiya Hauwa da Alhaji salisu amma da ikon Allah sun toshe ƙofar ko wani ɓaraka, babu wani shaidar da zai gwada Yaseer ne yayi ƙoƙarin lalata Reina kaman yanda babu wanda zai gwada ba shi ɗin bane Jamal ne.
Sannan har ita victim ɗin ma sun toshe bakin ta.

"Goggo kin gama?! Toh nayi miki rantsuwa da wanda yake busa min numfashi babu uban da ya isa ya saka in sake la'anannen yaron nan. Da idona na gan shi ganin annabi musa da firauna."

"La'ananne kuma?" Saudat ta tambaya cikin ɗacin rai. "Mu bamu yi masa baki ba, sannan bai yi abinda Allah zai la'ance shi ba"

"Ni zan yi ƙarya ma Yaseer kenan? Me ya kai shi ɗakin baƙi tare da ƴata Hafsah? Mai yake yi a ɗakin tana cikin mummunan yanayi? Wa yayi mata hakan bayan shi da yake tsaye a wurin?" Ɓata bakin shi ma yake yi da har ya tsaya yana bayani ma mutannen nan.

Kamal ya girgiza kai. "Baka ga dai-dai ba dai, duk da na shiga ban ɗauka ba bayi fidda ɓarawo amma ko ita yarinyar da kun tuntuɓi abin da ya faru zata faɗa muku tunda ita ce babban shaida, zata faɗa muku Jamal ɗin Alhaji Salisu ne da bakin ta, Yaseer yayi ƙoƙarin kare mata cutarwa ne"

Dududum!! Zuciyar Hajiya Hauwa da Alhaji Salisu suka haɗa baki wurin bugawa.

Kallon ta yayi tunda ita take da alhakin rufe ɓarakan da suka jawo. Ɓarakan da ta lura da samun shi tun bai yi girma ba amma taƙi sanar da shi. Saboda ta kama Jamal tun wurin shekara guda da ya wuce sanadiyyar mantawa da yayi bai rufe ƙofar ɗakin ba, suna kallace kallacen banza hannun shi cikin rigan Reina.

Ranan ta buge shi sai da yayi zazzaɓi amma bata faɗa ma uban ba Saboda tana tsoron abinda zai biyo baya. Yanzu idan ya zuciya sai ya ƙi cika burikan da suke da shi a kan Jamal ɗin ya saka masa ido da takunkumi.

Ashe ita da kanta ta ƙara ma barakar girma.
Tun da yana ganin yayi ya sha, toh yanzu bayi tsoron abinda zai biyo baya tunda mahaifiyar shi ta sani. kuma yayi Gaskiya domin daga baya ma lokacin da ya fara shan gida aka kawo shi ma mahaifin shi shima ɗan dukan shi yayi ya shiga bayan uwan ya ɓuya tana kan guiwowin ta tana roƙon shi ya rabu da shi.

Shikkenan kuma ya sha, don haka ya fara shan kayan shi har a cikin gidan.

"Wani Jamal kamalu? Jamal ɗin da bayi ƙasa?. Tun ranar juma'a ya tafi Ghana makaranta, abinka da Allah ya so wanke bawan shi, da yanzu sai ku ɗaura masa ko?"

Suka kalleta da mamaki don sun san Yaseer ba zai yi musu ƙarya har da kama suna ba. Tun da yace shi ne toh shi ɗin ne.

"Yanzu abun da yafi kawai a kawo ita Hafsatun ta faɗi abinda ya faru tunda ita kaɗai ta sani".

"Hakan yayi, amma shima Yaseer ɗin a kawo shi saboda aji ta bakin shi a fita hakkin shi."

Alhaji Tahir ya shiga girgiza kai.
"A'a za'a firgita ƙaramar yarinya ta kasa magana daman tsoron shi take ji ni na gani"

Goggo ta amshe da "idan haka ne suma iyayen Jamal sai dai su fita saboda zasu iya firgitata ta amsa abinda ba shi bane.

....

Sun rasa haƙuri ko rashin shi ya saka su zama ba tare da sun ƙosa ba har police suka fara kawo Yaseer kafin ala kawo Reina daga gidan Ummi tazo ta shige jikin mahaifin ta.

Sai tabi mutanen ɗakin da kallo a tsorace, ita fa har yanzu bata ga Auntyn ta bane shine damuwar ta.

Idanun ta da suka sauƙa cikin na Yaseer ya saka ta miƙewa tsugul zata yi kan shi. hawaye na cika a idanun ta ganin jikin shi da ciwon mutuwa kaman yanda Hajiya Hauwa tace.

~~~~~~~~~~~~~

Please To be clear document sai an kammala haɗa labarin kafin a same shi, wanda basu samu a lokacin da ake posting bane idan an haɗa document kuɗin shi daban. Amma mai son sai an gama zai iya biya ya jira.

Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.
Chapter 52 · 0% Book details