Sashe 16
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gobe da saurin zuwa yake Fauziyya. Zai ganta wani lokacin Amma lafiya ita ce uwar jiki don haka kada kiji komai ku tafi kawai zan miƙa masa saƙon gaisuwar ki".
Ummin ma ta miƙe alamun Rakiya kenan zata yi musu.
Da kanshi Alhaji Tahir ya ɗauka gyalen ta ya yafa mata Aina kuma ta ɗauka mata jaka itama tana mamakin wannan sabon salo.
Kallon Ummin tayi na sakanni Biyar ita kuma taƙi yarda ma su haɗa ido har suka gama sallama da Alhaji Tahir ya ajiye musu irin alkhairin da ya saba sannan yaja hannun Fauziyya suka fita bayan ya karbi Reina daga hannun ta ganin bata da niyyar motsawa.
Bayan sun fita Aina tayi dariya tace "kai Ummi, kora da hali fa kika musu"
Ko a jikin ta tace "toh ina zan iya da wannan mara kunyar? Gwamma ita da ta saba taje can su ƙarata abun su"
"Ai gashi daga gani shagwaɓaɓɓiyar kuka zata yi masa"
"Ke! Su suka ji wurin" ta ɗauki kuɗin ta miƙe zata shige ciki Aina tayi saurin bin bayan ta.
....
Buɗe mata bayan motar da yazo dashi yayi ta shiga sannan shima ya zaga driver ya buɗe mishi ɗaya bangaren ya shige da Reina a kafaɗar shi. Suka ɗauki hanya motar da ya kawo ta kuma na biye da su.
Wasa yake yi ma ƴarshi hankali a kwance ita kuwa ta sai murmushi dake ƙara narkar mishi da zuciya take yi.
"Fauzah kiga hancin yarinyar nan ya fara taso..." Maganar shi ta katse ganin hawaye sharr sharr a kan fuskar ta.
"Fauzah?! Me aka yi miki kuma yanzu dan Allah?"
Kaman tambayar shin take jira ta saki kukan da iya ƙarfin ta tare da haɗe kai da guiwa.
"Na shiga uku" yace yana ɗaura hannu a saman kafaɗar ta da niyyar ɗago ta.
Ture hannun tayi kafin ta ci gaba da kukan, sai ya rasa ta ina ma zai fara lallashin ta ga Reina a hannu.
"Fauzah I'm sorry. Ban san me nayi miki ba amma I'm sorry kinji?"
A zafafe ta ɗago tana watsa mishi harara "baka san me kayi ba? Kace baka san me kayi ba T? Fisabillilahi wannan dacewa ne? Awa nawa zanyi a gidan baki ɗaya? Kace in dawo da ƙarfe takwas na ji na amince, amma ba zaka barni in gana da mahaifi na da ƴan uwana cikin aminci ba? Bayan yaya Zeenat yaya Aina kawai na samu gani, kada ka manta ba ni kaɗai ka ganni ka ɗauko a cikin gidan ba" taci gaba da kukan ta mai gunji Reina kuwa ta zuba mata idanu.
"Harara ta kike yi Fauzah?"
Takaici ya kama ta ganin kaman bai ma ji abinda tace ba baki ɗaya. A hasale tace "Idona ne a haka!"
.....
"Yaro bayi da wayo"
Da gudu Suhail ya dawo jikin Yaseer dake dariya a gaban bokitin da yake wankin uniform ɗinsu ya kuwa ralla mishi cizo a gadon baya har saida yaseer din ya wani gantsare, sannan kafin ya kai mishi hannu har ya gudu wurin Saudat ya ɓuya a bayan ta yana leƙowa yana mishi gwalo.
Sosa wurin yayi don yaji zafi "yace ai gobe akwai boko zanga mai baka kuɗin tara"
"Umma tace zata bani" yace yana daɗa mishi gwalo.
Kwafa Yaseer ɗin yayi ya cigaba da wankin "ba Lallai sai gobe ba, zaka zo kace in siya maka wani abu ni kuwa sai na rama cizo na tunda da daɗi ai"
Saudat ne ta ture Suhail ɗin daga jikin babyn da ya koma sakawa yatsa a baki, shikuwa yaji ɗanɗanon gishirin datti ya kama ya fara tsotsa.
"Wallahi zan buge ka babana, baka jin magana ko? Kafi son sai na tara maka gajiya a cikin gidan nan?"
"Umma to ki ban kuɗi in garin buɗiɗis kuka"
Saida tayi masa danƙwale tace "ka ɓace min daga gani ko sai na tashi na riƙo ka? Fitinanne kawai kwaɗayayye"
Har ya manta da cizon da yayi wa yaseer don haka ya koma jikin shi yana muryar tausayi "Yaya garin buɗiɗis dan Allah."
Yaseer bai ce komai ba saida ya bari ya ƙaraso jikin shi kafin ya riƙo shi. "Wa na kama?!" Yace yana dariyan mugunta.
"Yaya sorry, dan Allah" ya fara ƙoƙarin kwacewa ya gudu don haka Yaseer ɗin ya miƙe yana faɗin "toh da wa yace ka yarda kudin aika idan dai kana da wayo? Shine zaka cije ni, kuma ka san an hana ka cizo?!"
"Yaya pleash, ba zan sake ba wallahi na bari"
"Ai nace sai na rama" ya sunkuya ya daidaici kunnen shi ya saka a tsakanin hakwaran shi ya ɗan danna kaɗan amma ihun da Suhail ya ƙwala zaka ce rai aka zare mishi.
"Wayyooo na shiga uku. Ya kashe ni Umma" ya fara kuka harda birgima a ƙasa.
"Me yasa kuke da wasan banza ne?"
Murmushi Yaseer yayi don yasan baiyi mishi komai ba.
"Da girman ka kake biye mishi Yaseer"
Hannu ya miƙa ma Suhail ɗin yana fadin "tashi muje a siyo garin buɗiɗis da tsami gaye ma" ai da sauri ya miƙe yana share hawaye. "Muje"
Dariya Yaseer yayi "toh bari in ƙarasa wankin nan sai muje, ka shiga ka ɗibo min na baby ma a kan gado " da gudu Suhail ya ruga ɗakin iyayen su lokacin da Kamal yayi sallama a gidan.
Ɗauraye hannun shi Yaseer yayi sannan ya miƙe ya tare shi tare da karɓan laidar hannun shi ya shigar ɗaki. Koma menene idan ummar su ta gani zata tantance me za'a yi dashi.
"Sannu da dawowa" tace tana gyara mishi zaman kujeran tsugunon dake gefen ta. Saida ya ƙarasa ya ɗauki baby da barci ya fara ɗaukan shi kafin ya zauna yana kallon fuskar shi.
"Shikkenan gobe yaro zaije yaga Jama'are" yace hankalin shi na kan jaririn amma da Saudat yake yi.
"Ai babana ma naso mu tafi tare amma bani son yayi fashin makaranta ko kuma ya saka mu dawowar wuri"
"Ki barshi kawai yayan shi zai kula da shi in sha Allah. Kuma nima zan saka musu idanu, kije ki huta ki murmure kafin ki dawo"
"Nayi kewar gida wallahi" tace tana jin ɗokin tafiyar na daɗa shigar ta.
"Amma kwana nawa kike da niyyar yi?" Ya tambaya yana taraddadin kada tace zata daɗe sosai, ko yara zasu jure rashin ta sosai ya san shi ba zai iya ba, domin ita ce komin shi a garin nan, idan ya kwaso zafin rana da nema wurin ta yake zuwa ya ji sanyi.
"Ba zan wuce sati biyu zuwa uku ba in sha Allah, danejo tace yaran suna zuwa karɓan abincin rana da na dare a gidan su saboda makaranta, na dai bata shinkafa da gari mai ɗan dama sai dubu biyar a cikin kuɗin da gwoggo ta bani domin babana akwai fitina Wallahi." Ta ƙarasa tare da miƙewa sannan ta ciro jakar sauran kuɗin daga kwalla ta fito da shi.
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)
*REINA 💍*
BookNest, Wattpad and arewabooks (Seemahwrites)
12.....Saida ta mayar da samiran da ta ɗauko jakar kuɗin kafin ta fito dashi wurin da Kamal yake zaune har Suhail ya ɗibo mishi ruwan sha amma can ƙasan kofi.
"Nagode baban maman shi" yayi dariyan ganin yawan ruwan yasan babu inda ze kai mishi amma sai ya kwankwaɗe ya miƙa masa kofin. "Ƙaro min, amma ka bar kofin ya shiga cikin randar sosai"
Da fara'ar shi na yayi abun arziƙi ya karɓa ya sake rugawa jikin randan ƙasar kana ya tsumbula kofin silver a ciki, saidai bai ɗibo wani abun arziƙi ba yanzun ma saboda an ɗaura randar a kan daron ƙasa yayi masa sama.
Ganin zaiyi ta wahalar da Abban ne yasa Yaseer sake ɗauraye hannun shi ya miƙe ya wafce kofin a hannun shi ya ciko kofin har baki sannan ya tunkari Kamal da shi. Zubewa Suhail yayi a ƙasa ya riƙo ƙafar shi yana kuka suran kaɗan Yaseer ya zubar da ruwan amma sai ya cigaba da jan ƙafar da Suhail ɗin ke riƙe dashi kayan jikin shi na daɗa tumurmusuwa a ɓaɓɓakakken simintin tsakar gidan har suka isa gaban Kamal a haka sannan ya ajiye mishi ruwan "gashi Abbah"
Ɗagowar da zaiyi idanun shi suka sauƙa a kan Suhail ze kai masa cizo a sha raɓar sa yayi saurin buge masa bakin ai kuwa ya fasa ihu.
"A'a me yayi maka zaka buge shi Yaseer? Bani son zalunci fah!" Kamal yace bayan ya shanye ruwan.
"Ai daman ba'a cizon mumini sau biyu a rami ɗaya. Madallah, shine maganin ka tunda baka ji" Saudat ta gwada Suhail dake riƙe da baki da yatsa. "Kuma kazo min nan wallahi sai na ƙara maka. Ka ga yanda kayi da kayan jikin ka! Jiƙa maka su zanyi sai ka wanke"
Yana tsoron zuwa jikin Abban sun ma ta riƙo shi don haka ya juya ya faɗa jikin Yaseer ɗin yana kuka. Dariya ne ya kama shi yace "toh muje a siyo kayan daɗi, amma sai kayi min alƙawarin ka bar cizo"
"Wallahi na bari" yace yana murza idanu.
Cewa yayi ya jira shi ya ɗauko kuɗi amma kafan shi ƙafar Suhail suka shige ɗakin ya ɗauko Naira hamsin a cikin jakar makarantar shi, sannan suka fice daga gidan.
"Alhamdulillah, Allah ya ƙara shirya mana yaran nan, Allah kasa su zama madafan jinginar juna a lokacin da bamu tare da su" Kamal yace yana bin su da kallon sha'awar shakuwar dake tsakanin su duk da ratar da suke dashi a shekaru.
"Ameen, amma ka sani don Yaseer yana da haƙuri ne, ba don haka ba ko ni bani iyawa da babana"
"Haka ne, Allah ya ƙara mishi haƙuri toh"
Kuɗin da ta ciro a cikin jakar ta miƙo mishi. "Bani son tafiya da kuɗin nan wallahi don zanje nayi ta kashe su a banza ne koma su ƙare a tsakanin ziyara, kuma kaga goggo sana'a tace in fara da shi".
Murmushi yayi ganin wayo wai take son mishi yace "Saudatu nace ba zan karɓi kuɗin nan ba, ke da kanki kika ce goggo tace kada ki kuskura ki bani Amma shine zaki saka ni saɓawa umarnin mahaifiyata ko?"