← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 57

Sashe 53

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

38..... Jamal ne!.

Jamal ɗin da ta bada amanar Yaseer a hannun iyayen shi, ashe su ke da alhakin duk abinda yake faruwa. Meesha ta ayyana a ranta.

Da sauri Alhaji Tahir ya riƙo Reina ta dawo jikin sa sai kawai ta fashe da kukan tausayin Yaseer.

"Yaya Yaseer, wa ya ji maka ciwo?"

Ɗaga ido yayi ya kalleta.

Abun mamaki, yana cikin halin ha'ula'i amma tausayin ta yake ji. Yaya zata fara rayuwa babu mahaifiya? Da ƙananun shekaru?.

Bai furta komai ba don bayi da ƙarfin magana yanzu.
Mahaifiyar shi, Meesha da goggo kuka suke yi sosai, har mahaifin shi a yanzu sai da ya zubar da hawaye.

"Yanzu idan a kan gaskiyar shi kuka mishi haka fah? Sai kuce yayi haƙuri?" Kamal ke magana.

Alhaji Tahir ya kalle shi sheƙeƙe. Yanzu wannan mabaracin har ya kai ya kalli idanun shi ya gaya masa magana? Yo ko da gaske bai kama Yaseer da kan shi ba ko kuma ace bai aikata abinda yake da tabbaci a kai ba zargi ba ma ai Yaseer be kai wanda zai buɗi baki ya bashi haƙuri ba, da girman shi da darajar shi a tsakanin al'umma. ko iyayen shi basu isa ba, kai ko ita goggon ma.

"Toh ai gata nan, zamu ji daga bakin ta, idan ba hakan bane za'a san abun yi" Alhaji Kalabu ya mayar ma Kamal, ya kuwa yi sa'ar dawo da duban shi garesa yana masa wani irin wulaƙantaccen kallo, bai taɓa sanin ƙananun mutane bane su sai yau.

Babu wanda ya sake magana, babu abinda yayi saura a faɗa, shaidar Reina kawai ya rage. Gaskiyar ta kawai zai warware wannan rikicin da kuma barazanar farawar gaba ta har abada a tsakanin ƴan uwan da suka haɗa jini. Amsar ta shi zai tantance makomar tarihin da ba a yanzu aka fara rubuta shi ba, da daidaitaccen alƙalami, a littafi mai daraja da kyakkyawar rubutu.

Sai dai farkon tarihin ne kawai yayi kyau, tsakiyar rubutun yazo da gargada, gashi ƙarshen sa na neman dagulewa yanda ba zai yi daɗin karatu ma ƴan baya ba.

Alhaji Tahir ya kwantar da ita a jikin shi kafin cikin ƙasa da murya yanda ba zai razana ta ba ya kira ainihin sunan ta na yanka a karo na farko.

"Hafsatu na." Sai dai saboda yanda wurin yayi shiru ko allura aka jefar za'a iya jin karar haɗuwar shi da ƙasa, ba don hayaniyar ƴan gaisuwa dake shigowa sama-sama ba.

Reina ta ɗago ta kalle shi da idanun ta dake zubar da hawaye, ya saka hannun shi yana share mata, yana auna tambayar da zai yi mata, yanda zai yi daidai da tunanin ta.

"Sarauniya ta... A gidan Umman Jamal da su wa kike wasa?"

Sai ta fara tunani a ranta, Wani irin wasa yake nufi kenan? Wasan da suke yi da su Zaheera da Abdallah? Ko wanda suke yi da Jamal?

"Ina yi da su Zaheera da Abdallah sai kuma yaya Jamal"

"Yauwa kun ji ba?!" Saudat ta furta tare da ɗan jin sanyi a ran ta. Daman ta san idan yarinyar tazo gaskiya zai fito.

Caraf Hajiya Hauwa tace "Ai wasa aka ce? Ɗan uwan ta bayi da ikon wasa da kanwar shi iye? Ko baku ji ta ambaci sauran ƴan uwan ta bane?"

"Mun ji mun fahimta ɗan uwanta ne. Amma a tambaye ta wani irin wasa suke yi mana?" Yanzu abun ya koma tsakanin Saudat da hajiya hauwa.

Ɗaga musu hannu Alhaji Tahir yayi ganin Reina ta fara tsorata. Suka yi shiru zuciyar Hajiya Hauwa ya tsananta bugu kaman wacce take filin tsere na Olympics, Saudat kam ta samu nutsuwa zuwa yanzu, ƙarƙare shirin kawai ya rage.

"Yaseer fa?" Ya cigaba da tambayar ta cikin kulawa.

"Yaya Yaseer dai ko?" Ta gyara masa, Saboda itama shi Yaseer ɗin ne ya haramta mata kiran sunan babba gatsau.

"Eh shi ɗin. Baku wasa da shi?"

Sai ta girgiza kai "karatu yake mana ni da su Zaheera, bayi min wasa"

Yaseer ya saki numfashi, haƙiƙa ya tsorata da lamarin amma komai ya zo ƙarshe. Yayi kyan kai da ya yanke shawarar koyar da su duka ba ita kaɗai ba.

Alhaji Salisu da Hajiya hauwa kam kaman a buɗe musu ƙofar nan su fice da ɗan iskan gudun da ba za su tsaya ba sai sun isa birnin sin.

Ganin kaman Reina bata fahimci yanda tambayar tashi ya dosa ba, ya saka shi canza shawarar fito mata a mutum kawai.
"Reina. Waye ya taɓa ki lokacin da kuka je asibiti da Aunty aka baki gado? Waye yake cire miki kaya da wando a gidan Umman Jamal?"

"Wallahi Alhaji bayan gaisuwa babu abinda yake shigar da ni cikin gidan. Tsakani na da su duka a waje ne Wallahi" Yaseer yayi maganar a wahalce.

Yanzu shine kawai dama ɗaya da yake da shi ya kare kan shi, dama ɗaya ne kawai aka bawa gaskiyar shi ya cece shi.

Idan hakan ne ta yaya aka yi ya kama shi a cikin ɗaki a tare da ita?.

"... Yaya Yaseer ne!"

Reina ta katse maganar Alhaji Tahir da ma duk wanda ke da niyyar tsoma baki a wannan gaɓar, suka juyo suna kallon ta, ita kuwa shi take kallo. Ceton shi ne kawai burin ta, ba zata juri rasa Auntyn ta ko shi ba, bata son ya mutu, don ta tseratar da shi daga mutuwa zata yi ƙarya ɗari ba ɗaya kawai ba.

Shima ita yake kallo, cikin wani irin yanayin da bai sani ba. Wani abu yake ji a cikin zuciyar shi mai zafi, zafin da yake ƙona tsokar jikin shi yana tsinka jinin jikin shi ya ƙara gudu. Wani abu mai kaifi ya taso tun daga yatsar ƙafar shi yazo ya tokare shi a ƙirji kaman mashi. Ɗacin da yake ji a maƙogwaron shi kaman bai taɓa ɗanɗana wani abu mai zaƙi ba a rayuwar shi.

"Hafsatu kiji tsoron Allah, ki san zaki mutu, dan Allah ki faɗi gaskiya kin ji?" goggo ke roƙon ta Saudat kam fama take yi da numfashi.

"Ai daman na faɗa. Idan bata ji tsoron Allah ba naki zata ji? Ko kun fi son ta ƙala ma wanda bai ji ba bai gani ba?" Hajiya Hauwa ta miƙe hannun ta a ƙugu tana girgiza. Gani take yi kaman zaƙewar ta shi zai daɗa aza ƙasa a kan komai ya bisine shi yanda har abada babu wanda zai iya tonowa.

Zancen mutuwan da aka yi shi ya ƙara firgita Reina ta saka kuka "Wallahi shine. Wallahi yaya Yaseer ne!"

A lokaci ɗaya wuri ya hautsine, ɗaki ɗaya ya karkasu da rikici daban-daban.

A ɓangare ɗaya, fifita goggo ke yiwa Saudat kamal na ƙoƙarin sheƙa mata inhaler kada suyi har biyu babu, domin Yaseer kam suna da tabbacin a yanzu ta ƙare masa.

A wani ɓangaren kuwa kururuwa Meesha tayi zata yi kan Reina Hajiya Farida ta riƙo ta don babu abinda zai hana Alhaji Tahir kutubol da ita ta kuskura ta nufe su a halin da ake ciki.
"Wallahi ƙarya kike yi! Munafukar yarinya, an kitsa miki munafurci don a ga bayan shi ko?"

Lafiyayyar mari Hajiya Hauwa ta ajiye mata a kunci tana gwada ta da yatsa. "Ki shiga taitayin ki Wallahi, kema bari muje gida sai mun duba ki mun gani idan bai gama da ke ba wannan zaƙewa haka.

Ɓangare na ƙarshe, mafi tasiri, wanda a wannan gaɓa, a wannan lokaci, a wannan yanayi, alƙalamin ƙaddara ta fara rubuta babi na ƙarshe a cikin littafin tarihin nan.

"Wallahi sai na wulaƙanta ka, sai na tozarta ka, sai na ga bayan ka, sai na saka iyayen ka sun yi danasanin haihuwar ka, la'anannen yaro, sai ka gagara gwada fuskar ka a ko ina saboda ƙasƙanci, sai na ga bayan ka matsiyaci ɗan matsiyata!!"

Ba don riƙon da yayi ma Reina dake kuka a hannun shi ba da babu abinda zai hana shi sake yi ma Yaseer lilis.

Laɓɓen bakin Yaseer ke sake zubar da jini saboda yanda ya datsa ta da haƙorin shi, burin shi zafin zai dishashe azabar wutar dake cin zuciyar shi, amma bayi jin kaman gangar jikin shi na fahimtar wani yanayi a yanzun.

Kan shi ya sauƙar ganin yanda ake fama da mahaifiyar shi da ta rasa numfashin ta ga yanda suke kuka kaman ran su zai fita.

Duk shi ya jawo.

Da bai fara ba da ba'a zo wannan gaɓar ba.

Ashe zuciyar taimako na iya kawo maka cutarwa?

Ashe ba ko wani alƙawari ke buƙatar sai an cika shi ba?

Yayi danasanin sanin Hafsatu a rayuwar shi!.

Sauƙe kan shi ƙasa yayi hawaye na bin kuncin shi, yayin da ɗan sandan dake tsaron shi ya ƙara tsananta riƙon da yayi mishi. Sun cire mishi ankwa ne saboda shiga cikin mutane amma yanzu babu amfanin hakan sai ya sake cirowa daga aljihun shi ya haɗa hannun Yaseer guda biyu ya garƙame su.

Yana tsaye kawai sai yanda aka yi da shi, kunnen shi na jiyo masa ɗiban albarkar da Alhaji Tahir da ƴan uwan shi ke masa.

"Ku tashi ku bar min gida matsiyata wa'inda basu gaji arziƙi ba, kotu ne zai raba ni da ku Wallahi. Idan kuka ga ban rufe shi ba toh wallahi sai idan bani raye, amma sai naga bayan ka" Alhaji Tahir ya gwada Yaseer da yatsa, kana ɗora ma sauran "mutanen Banza mutanen wofi" shima kukan zuci yake yi, domin ya tabbata an cutar mishi da Reina, an raba shi da Fauziyya.

Kalaman shi sun yi ma goggo zafi
"Ka san wacece Halime a wurin Kamalu ɗahiru? Hannun mahaifin ka cikin nawa Allah ya karɓi ran shi, ciwon ajali da ya kama shi bai iya ba sai da ya dawo Jama'are yaga gida yaga Halime, Halime da ƙauyanci da jahilcin ta ita ta tsaya a kan rabon gadon ku ta tabbatar an fitar da hakkin kowa yanda ya dace. Amma koran kare kake min saboda an jarrabi ƙarfin zumuncin mu?"

"Kai, ko ke kika haifi ubana albarka! Haba! Sai kace maita?"

A zuciye Kamal yayi kan Alhaji Tahir, su Alhaji Salisu suka shiga tsakani zasu buge shi.

Amma kukan Fauziyya yake ji a cikin kunnen shi, kuka take yi sosai a cikin kan shi.
Chapter 53 · 0% Book details