← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 57

Sashe 23

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin hankalin shi ya dawo kan Yaseer dake tsaye a wurin yana bin su da idanu.
Lokaci ɗaya Alhaji Tahir ya haɗe fuska ya watsa mishi wani kallo kafin ya wuce ciki da sarauniyar shi.

......

"Ina yi don in samu kuɗi na amma ba ra'ayin wannan kalolin bidi'ar nake ba. Haba ace abu duk shekara babu fashi? Har na wata shida sai da ya saka aka yi mata fa."

Ta san akwai ne ya saka ake yi amma ko da ace tana da shi, da zata iya ɗin, ita kam abun yayi yawa kuma, bai bata sha'awa ba. "Amma da sadaka kuke mata kawai a ranar badday ɗin. Ko idan aka yi biki wannan shekarar a wani sai ku kai kuɗin yanda za'a yi mata addu'ar albarka ma rayuwar ta"

"Ina ƙoƙarin yin hakan tunda duk abinda nace ba fasawa zasu yi ba. Kayan ta ma idan aka cire akwai wani gidan marayu da nake kai musu sai in haɗa musu da wani abun."

"Toh hakan yayi. Allah yayi mata albarka ya ƙara shirya mana zuri'a. Tarbiyya ne a wannan zamani ba abu ne mai sauƙi ba"

Matse baki tayi tana ajiye piping bag ɗin hannun ta wanda yanzu ta gama frosting ɗin cake ɗin, sprinkles kawai ya rage ta zuba mishi ya ƙara haskawa.

Ta kalli Saudat, tana son ta buɗe mata cikin ta ko zata samu mafita, ko zata samu shawara, ko da rage damuwar ta ne ta samu tayi, amma bata san ta ina zata fara ba.

"Umman Yaseer" ta kira ta da wani irin muryar da ya sanya ta raba hankalin ta daga jikin cake ɗin da ta gagara gaskata cewa a kan idanun ta aka yi adon shi tun daga farko har zuwa ƙarshe, ta ɗora su a kan Fauziyya.

"Na'am"

Ajiyar numfashi tayi kana tace. "Abban Reina Ya..."

"Mai kuma na yi?"

Yace yana shigowa cikin kitchen ɗin ɗauke da ƴar gudaliyar shi.

Miƙewa tayi. "Babu komai, Sannu da dawowa"

"Yauwa matar aljannah" ya ƙaraso ya sumbaci goshin ta ya matso da Reina ma da nufin itama ta sumbace ta amma mugun kallon da Fauziyya ta watsa mata ya saka ta juyar da kanta daga kallon ta bakiɗaya.

"Daddy mu je a yanka cake" tace don su bar kitchen ɗin.

"Shikkenan, bari in canza kaya ko?"

Yayi ƙorarin sauƙe ta amma firr ta maƙe shi.

Sai a sannan Saudat tayi ƙoƙarin gaida shi sai dai ko jin ta ma baiyi ba don hankalin shi bayi kan ta.

"Fauzah me kika yi ma yarinyar nan a bayan ido na?" Ya bita da kallon tuhuma ganin tsoron da ke tattare da Reina.

"Ni babu abin da nayi mata, amma Allah ya ƙi ki kishiga hannu na Reina"

Ya ware idanu "Oh a gaban idanu na kike faɗan haka Fauziyya?"

"Ka tambaye ta abin da tayi tukunna, me ya haɗa ta da iyami? Ai gashi da ta san bata da gaskiya ai ɓuya take yi a jikin ka"

Ba wai don yaji laifin tan ya tambaya ba, sai dai kawai don ya san me ya haɗa ta da wacce aka kira da iyamin tunda yana da tabbacin mai aiki ne. Masu aikin da ya kafa musu sharaɗi a kan ta, kuma duk wacce ta tsallake wannan sharadin toh a bakin aikin ta ne.

"Me ya haɗa ki da ita Reina?"

Shiru tayi tana cin farcen hannun ta cikin fargaba kada Daddyn tan ma yace hukunta ta zai yi.

"Ta yi min yashin kunya ne shine nace Uwar ki!"

A tare Saudat da hajiya Fauziyya suka riƙe baki cikin kaɗuwa don basu san da wannan zancen ba, sai dai zasu iya cewa tambayar da Alhaji Tahir yayi ma Reina shine abin da yafi kaɗa su fiye da wannan nannauyar ashariya.

"Wani irin rashin kunya tayi miki?" Shine abin da ya tambaye ta.

"T!!!. Fisabillilahi baka ji abinda tace bane? Ni na koya wa Reina ashar ko kai da ba zaka tambaye ta a ina ta koyo ba?."

Ya buɗe baki zai yi magana, ya dubi Saudat da ta kafe idanun ta a kan kantar kitchen ɗin tana jin dama ta dawo tsuntsuwa tayi filfili ta bar musu wurin.

Sai kawai ya fasa, suka juya da Reina suka bar mata kitchen ɗin, yayin da ƙafafuwan Fauziyya suka gagara ɗaukan ta ta koma jikin kujerarta ta zuba a kai idanun ta a jikin ƙofar kamar sun fita sun bar tabon zagin ne a wurin.

"Na shiga uku!"

......

Bakin ta da na mahaifin ta har kunne, hannun Reina cikin na Fauziyya, nata kuma cikin na Tahir suka yanka cake ɗin bayan an ƙirga musu daga ɗaya zuwa uku. Nan kuwa wuri ya ɗauki tafi da suwwa Dj ya cigaba da aikin shi.

Dukkan su uku suna cikin shiga ta alfarma musamman ita celebrant dake cikin wata buɗaɗɗiyar riga mai walwali iya guiwa kalan emerald green. Kanta da tiara kalar rigar, sai kuma fairy wand da ta riƙe irin dai na fairy ɗin cikin cartoon ɗin da take son gani mai suna tinkerbell.

Cake ɗin ya fara yanka ya kai bakin Reina ta gutsura sannn itama ta karɓa ta kai bakin mahaifin ta, ya ci ya goge hannun ta saboda kada ta ɓata jikin ta kafin aka shiga haska su da kyamarori. sun ma manta da duniyar Fauziyya a wurin, wanda itama a nata ɓangaren ta manta da tasu duniyar.

Cikin gidan da haske sosai amma gari ya gama baƙiƙƙirin hadari sai ƙugi yake, kiɗan da ya cika falon ya hana su jin buƙatuwar da ruwan sama yake da shi don ya sauƙar da Ni'ima.

Ji take yi duk girman gidan kaman so yake yi ya matse ta, numfashi yana niman kasa mata, ga zufa dake yanko mata a cikin sanyin Ac da kuma ruwan da ya kece yanzun kaman da bakin ƙwarya.

Daman yanayin damina ya saka su yin hidimar a ciki, ta fara takawa a hankali saidai tana jin ƙafar ta kaman ba a kan ƙasa yake tafiya ba.

Su Hajiya Farida da suka gama kashe hoto yanzu suka nufo ta suna maganganu sai dai ba zata iya fayyace me suke faɗa ba. Ba ma zata iya gane su waye a kan ta ba.

Ita dai kawai ta san ganin ta yana dishashewa a hankali har ta daina ganin komai, ta daina jin komai, sannan ta daina tunanin komai na wani lokaci.

Baki ɗaya mutanen parlourn kowa yayi kanta, Alhaji Tahir bai san lokacin da ya dire Reina a wurin ba, ya shiga tutture mutanen da suke tsaye a hanyar shi na ƙarasawa gare ta sannan ya zuba a kan guiwowin shi yana bubbuga fuskar ta cikin tsananin tashin hankali da firgici.

Goran ruwan da ɗaya daga cikin mutanen tayi hankalin miƙowa ya karɓa ya shiga shafa mata amma inaa babu numfashi. Ganin ɓata lokacin shi kawai yake yi yasa ya ciccibeta da zungureren cikin ta suka yi hanyar waje da gudu mutanen ma suka bisu yuuuu.

~~~~~~~~~~~~

*Ku faɗa min idan akwai gajiya mu ajiye posting sai bayan Sallah. Wataƙil ko shi yake hana yawan comment*

*Saliha Ahmad Na'ibi Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

17...... A cikin ruwan nan? Ga yara, mura ya kama su a ɗaura min jinya? Ai sai dai idan ya lafa ko kuma gobe ma je" Hajiya jummai ke wannan bayanin bayan Alhaji Tahir ya cicciɓi Hajiya Fauziyya sun yi asibiti.
Daga farko sun bi shi yuuu kaman sun damu amma yana shiga cikin mota da ita dukkan su suka dawo ciki.

abokan arziƙi kam da suka gayyato duk sun bi su a baya cikin motocin su, sai matan ƴan uwan shi aka bari kawai da yaran su, cake ɗin da aka fara yankawa ma suke ta kasawa a tsakanin su da ma sauran kayan taɓa ka lashe.

sai kuma su Saudat da basu da tasu abin hawar kuma ƙarfin ruwan ba zai bari su fita har can babban hanya su samu keke napep ba, Amma hankalin ta dama Yaseer a matuƙar tashe yake don gani suke yi kamar ba zata tashi ba.

Amma fah duk cikin wannan tashin hankalin bata ga Reina ba, lokacin da iyayen nata suka fita ta so ta bi su da kukan ta aka ɗauke ta amma tun daga nan bata sake ganin ƙyallin ta ba.

Sai dai Babu wanda ma ya lura, ta kansu kawai suke yi. Na musamman suka ɗauko foil paper a kitchen suna ƙunshe abin da suke buƙata a wurin don suna da tabbacin bikin birthday ta watse.

Ƙarasawa ta yi wurin da Yaseer ya haɗe kan ƙannen sa ya nutsar da su wuri guda, saboda banɗashen da ake a wurin ya fara jan hankalin su.

ta taɓa shi. "Ka ga Hafsatu?"

Miƙewa yayi ya bi ko ina da kallo amma babu ita babu alamun ta. "Ko sun tafi tare?"

Ta girgiza kai, "taya ni mu duba ta"

Sai da ya kashe ma Suhail warning don ya fi Sabir kwaɗayi da fitina kafin suka raba hanya suna dubawa.

Suna barin parlourn Ƙofar shi ya buɗe duk idanun wanda ke cikin ta ya kai wurin, kar dai ta farfaɗo ne suka dawo!. Amma ganin yaran da suka fara shigowa ya saka su sauƙe ajiyar zuciya kafin Hajiya Hauwa ta biyo bayan su, tana karkaɗe ruwan da ya taɓa ta daga mota zuwa cikin gidan.

"Amma baki iya kiwo ba wallahi" Cewar Hajiya Farida dake lulluɓe kajin da ta tattare kaman babu a gidan ta.

"Kada ki ce min an ci an cinye babu ni dan Allah, aiki ne ya min yawa a office Wallahi" tace tana ƙarasowa kusa da su.
" ko zama fa ban yi a gidan ba daga canza kaya na kwaso yaran muka zo"

"Hmm ba wannan ba, show muka sha. Acting dai ko a Bollywood albarka mutuniyar ta iya shi"

Ta bata hannu suka sha kafin ta ce "dan Allah bani in sha, yau kuma wani episode kuka gani?"

"Ina irin scene ɗinnan da mace zata yi suman ƙarya ta ɗaga hankalin miji ya tattare ta sai ta kanne ma muguwar sirikar ta idanu da murmushin cin Nasara?..."

Hajiya Hauwa ta gyara zama tare da gyaɗa kai.

"Toh fa episode din aka gwada mana a zahiri"
Chapter 23 · 0% Book details