← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 57

Sashe 41

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago jemammun idanun ta tayi ta zuba mata don yanzu kukan ya fara gagaranta, tayi shi har ta gaji gashi har yanzu babu abinda ya ragu a cikin laulayin da take fama kaman ta ajiye cikin ta huta.

Tayi kewar yaranta, babu kamar Maama ma wanda take ƙarama ga ƙuna a baki, sannan ko Reina bata san ina Tahir ya kaita ba balle ita. shima Tahir ɗin tayi kewar shi, amma tun da ta dawo ko sau ɗaya bai sake yarda ko kalmar baki ya shiga tsakanin su ba. Kullum a cikin kiran shi take yi, da tura mishi sakonnin ban haƙuri amma bayi ɗauka bayi reply kuma shi bai yi blocking ɗin ta ba don haka bata fasa ba itama. Ita ko ɗauka yayi ta tambaye shi jikin Maama da Reina ɗin ma amma har a text ta tambaye shi ya share.

Baki ɗaya ta gama fita hayyacin ta a yanzu, ta rame ta lalace fatar ta yayi duhu.

"Fauziyya magana nake yi"

"Ummi mai zan ce? Tahir ya raba ni da yara na" sai ta fashe da kuka da muryar ta dake a dishe.

"Ashe baki ga laifin da kika yi ya raba ki da su ɗin ba? Kina tunanin idan wani ne a matsayin shi ɗin barin ki zai yi? Ni naga ƙoƙarin shi ma ai, domin da shi yayi wa ƴata haka wallahi sai nayi Shari'a da shi ko me yake taƙama da shi kuwa".

"Ummi bayan shi kike bi?"

"Bayan gaskiya dai nake bi"

A lokacin Sajida ta shigo da sallama itama ta samu wuri a ƙasa ta rakuɓe, duk ta gama saka damuwar Fauziyya a kanta.

Bata da wani shekaru aka yi auren yayar tata amma kowa ya shaida irin dramar da aka kwasa kafin auren, idan haka ne tunda Alhaji Tahir ya iya sakin Fauzee toh ita waye da namiji ba zai iya wulaƙantata ba?.

Ummi ta ɗaura ma Fauziyya daga inda ta tsaya "kina son yaran ki su tashi da tsanar juna ne Fauziyya? Kina son su tashi basu shan inuwa ɗaya kaman masu ganin hanjin juna? Nace Kina son yaran ki su zamo abokan gaban juna?! Toh ki ajiye banbancin da kike gwadawa a kan su tun kafin lokaci ya ƙure miki"

"Ummi duk yanda kayi ƙoƙarin jawo Reina a jiki wallahi sai haƙurin ka ya ƙare, kaman sheɗanu suna yiwa yarinyar nan fitsari a kai. Ga taurin kai kaman jaka, ita ce rashin ji, rashin fasali, shegen son jiki da kyuya ba'a magana, kanta yanda kika san ba ƙwaƙwalwa bane a ciki ba ko kunnen ƙashi gareta, kullum girma take yi amma ƙasa take ƙara ci..."

Ganin kaman har yanzu bata gama ba Ummi ta dakatar da ita cikin takaici "ba sheɗanu bane suke mata fitsari a kai ba Fauziyya, kalaman harshen ki ne suke dulmuyar da duniyar ta. Ta ina ɗan da uwar shi take iya faɗan irin wannan kalaman a kan shi zai taɓa ganin dai-dai?."

Sauƙe ajiyar zuciya tayi bata iya amsawa ba.

"Fauziyya ke kika ɓata Hafsatu, da kunsan ba zaku iya mata tarbiyya ba da baku bata sunana ba don baku min gwaninta ba."

Cikin matsanancin kuka da ya ƙwace ma Sajida ta fara magana "Ummi ki yafe ni amma me yasa a duk lokacin da ɓaraka ya samu a gidan aure mace kawai ake bawa laifi? Ke kin san irin haƙurin da Yaya Fauzee take da shi amma ace duk abinda ya faru iyayen mu ma sai ku take musu baya? Nima idan aka zalunce ni na kawo kuka na haka za'a yi min?"

Gyaɗa kai Ummi tayi alamun ta fahimta sannan ta juya wurin ƴar uwar tan tace"Fauziyya kiyi min adalci, sau nawa ina bin bayan ki a bayyane ko a ɓoye a duk lokacin da kike kan gaskiya ko dai-dai? Sau nawa ina baki shawarwarin da baki nima ba ma a kan zaman aure da kuma tarbiyyar yara?."

Gyaɗa kai tayi alaman haka ne "Kiyi haƙuri Ummi in sha Allah daga yanzu zan gyara nayi alƙawari"

"Ba wa ni zaki faɗi kin gyara ba sai ma shi wanda kika yi wa laifi, ba'a kashe wuta da wuta Fauziyya na sha faɗa miki zafi da ikon ki a kan Reina ba shi zai sauya ta ba.
Na san kinyi fama da ƙuruciya a lokacin da kika haife ta amma da haka kowa ya fara, ni lokacin da aka yi min aure ma ban kai hakan ba kuma nima na kamanta irin kuskuren ki a kan Aina da Zeenat.
Yayun ku maza basu bani damuwa ba amma su sun tashi basu shaƙar inuwa ɗaya sai faɗa, ganin Aina ce babba ko ita ta takalo Zeenat sai ba zan bincika abinda ya faru in bata gaskiyar ta ba har wasa-wasa abun su ya ƙazanta suka koma kaman masu ganin hanjin juna. Ke kuma a lokacin da kike naki ƙuruciyar hankali na yana kan shirya su bani da lokacin ki ga wasu yaran suna kan zuwa. Shi yasa kika tashi mun da mugun riƙo, fushi da zurfin ciki dukda kina da sauƙin kai amma wannan halayen sun isa su wargaza ayyukan ki har a wurin Allah ba zallan miji ba.

.....

A tsawon wata guda yaga sauyin da bai yi tsammani ba daga gare su, daga yaran har Jamal. daman tsananin sake ne yasa suke nan kaman dolaye amma da ya matse musu lamba duk suna ƙoƙari musamman ma Reina, bata da nauyin harshe a yanzu koyar da ita tajwidi ba zai yi wahala ba.

Suna tsaka da karatu Alhaji Tahir yayi parking ɗin mota sannan ya fito gani ma idanun shi sauyin da ya fuskanta a tattare da ƴar shi a kwanakin nan. Ya fito hannun shi ɗauke da farin envelope fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushin da ya ƙara girma lokacin da ya jiyo muryar Reina tana rera Al-ƙur'ani.

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

29........Har ya ƙaraso wurin bata lura da shi ba hankalin ta yana kan karatun ta sai mamaki ya kama shi, anya wannan Hafsatun shi ne?

Yaseer ne ya fara hango shi, yayi mishi sannu da zuwa.
Jin yace Alhaji Tahir yasa Reina juyawa da sauri, ganin Daddynta tsaye yasa tayi firo da ƙur'anin izu biyar da Yaseer ya siya mata, ta miƙe za ta nufi wurin mahaifinta da gudu amma tsawan da ya daka mata ya saka ta daskarewa a hanya, ita bata je ba ita bata juyo ba ga hawaye har ya fara taruwa a idanun ta.

Shi kuwa Yaseer bai san ma yayi ba, wurgi da ƙur'anin da tayi shi ya razana shi, amma kwanannan yana ƙoƙarin sake mata sosai don tausayi take bashi.

"Ƙaraso sarauniya ta" Alhaji Tahir ya yafato ta da hannu murmushin kan fuskar shi na bajewa.

A maimakon ta je ɗin kaman yanda yace sai ta juyo wurin Yaseer cikin karyayyen murya tace "yaya Yaseer in je?"

Numfashi ya ja sannan ya gyaɗa mata kai. sai ta gyara nutsuwarta ta fara takawa a hankali taje ta rungume mahaifin ta wanda ruwan mamaki ya shanye shi.

Daman bautar masa da ƴa ake yi?.

Hannun ta ya kama suka haura wurin yana kallon sauran yara biyu suna ta kwafan abinda ya rubuta musu a allo, suka gaida shi sannan Yaseer ya saka mishi kujera ya zauna kana suka gaisa.

"Amma malam Yaseer ba za'a rage tsanantawa ba haka, idan ma wani abu ake buƙata da zai sanyaya ran malam ko ya saka yaran karatu ai sai a faɗa a bayar"

Kaɗan ya rage yayi mishi kallon banza amma sai ya daure ya sauƙe idanun shi. yana ji a ran shi lallai ba don Hajiya Fauziyya ba ko nawa wannan mutumin zai bashi bayi da lokacin ɓatawa a kan sakaltacciyar ƴar shi, domin bayi jin zai taɓa mantawa da abubuwan da suka faru a kan idanun shi a shekarun baya har abada.

"Babu abinda ake buƙata Alhaji, kuma suna karatun sosai" ya mayar mishi ganin ya tsare shi da idanu. bayi raba ɗayan biyu mamakin yanda ya girma yake yi domin shima sun kwana biyu basu haɗu ba.

"Nima kawun ka ne ka ji?" Ya shafa kan ƴar shi dake rufe cikin baƙin hijabin da ta kamo ƙasan shi ta saka a baki tana ci, murmushin alfahari na samuwa a kan fuskar shi "kuma ina son ganin Sarauniyata tana karatu, idan ta samu ilimi mai yawa zan yi farin ciki"

Itama sai ta murmusa domin Daddyn ta kullum a cikin yabon ta yake komin kashin abinda zata yi kuwa, amma Aunty ko tayi wani abu domin ta burge ta sai ta ɗauko kuskuren ta na baya tayi mata faɗa a kai, sannan ko Maama ne zallah ta ɓata mata rai saita haɗa su duka biyu tayi ta faɗa.

"Nima buri na tayi karatun, kuma Insha Allah a tsawon lokacin da zan ɗauka a nan zan tabbatar da hakan" ya ɗauki zancen shima kawun shi ne a matsayin sharrin kunne da ya jiyo mishi ba dai-dai ba.

"Zuwa Jamal ya rubuta Jamb ne ko?" Alhaji Tahir ya tambaya wani tunani na zuwa kan shi.

Gyaɗa kai Yaseer yayi "eh Alhaji"

Bai ji daɗin yanda ya sake kiran sa da Alhaji ba, alama ne na shi bai ɗauke shi a yanda yake so ba kenan.

"Toh idan kun kammala ɗin me zai hana sai ka ɗaura a namu gidan har zuwa itama lokacin da zata kammala secondary ɗin ko bayan nan ɗin ma ai zai yiwu ku ci gaba"

"Yaseer ya ɗan waro ido"

Alhaji Tahir yayi saurin ɗaurawa da "zan iya ninka maka abinda suke baka, na san ko aikin gwamnati ka samu idan ba gwaɓi gare shi sosai ba bazaka samu kamar hakan ba. Kuma ni nayi alƙawarin sama maka aikin ma"

Duk ƙoƙarin shi saida sautin "Hmm" ya kuɓuce daga bakin shi.

Wato tunda morar shi zasu yi har alƙawarin aiki ake yi mishi tun ma bai gama karatun ba amma mahaifin shi da yayi ta musu daako na tsawon shekaru sai matar shi ne ta iya rufa mishi asiri.

"Toh zan duba in gani Alhaji" yace don a bar maganan.

Ya miƙe cikin jin daɗi "yauwa, yanzu koda ta koma gidan ma zan saka ana kawo ta har ku gama da nan ɗin"

Yaseer ya gyaɗa kai "toh"
Chapter 41 · 0% Book details