Sashe 1
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*REINA 💍*
_Book 1_
*By Saliha A. Na'ibi (Seemahwrites)*
*Women of words writers*
*Sadaukarwa ga my dear Hanifah shamaki da addaririya ta Ramlat abdulrahman manga(mai dambu). Ina godiya da sahihiyar ƙauna, Allah ya barmu tare❤️.*
*Disclaimer: Ban amince a sauya min littafi ta ko wace irin siga ko a ɗaura min a wata channel na youtube ba tare da izini na ba, yin hakan babban kuskure ne kuma zai sanya mu saka ƙafar matsatstsen wando ɗaya da mutum*
_Any resemblance to any figure or event, deceased or living is purely coincidental_
بسم الله الرحمان الرحيم
01...shi zumunci a wannan zamanin na mai shi ne, ga masu hannu da maiƙo ake sada zumunta mai bushashshiyar hannu kuwa saidai shi ya sada ta"
Taɓe baki Saudat tayi tana gyara kwanciyar Suhail a jikin ta wanda tunda iskar napep ta kaɗa shi barci yayi awon gaba da shi
"Amma abin yayi yawa Abban Yaseer. Ko wani hidima nasu muna kan zirya a hanya amma ko sau ɗaya! Ko sau ɗaya fa ban taɓa haihuwa mutanen nan suka ɗago ɗaya daga cikin su yazo mana barka ko suna ba saidai mu ko yaushe muna kan faman kashe kuɗin adaidaita zuwa gidajen su.
Yamutsa fuska yayi alamun baiji daɗin zancen ta ba, ga Yaseer ɗin dake zaune a tsakanin su ya kafe shi da idanu yana dakon amsar da mahaifin nasu zai bayar don da gaske ko shi mai shekaru 12 ya fahimci cewa yawan zirya da suke ma ƴan uwan mahaifin nashi ba buƙata ko appreciating suke yi ba balle kuma mahaifiyar da ta haife su.
"Ƴan uwana ne fa Saudatu. Ki taya ni son su mana"
Girgiza kai tayi "nifa ba son ƴan uwan ka bane bana yi, kawai yanda suke treating ɗinmu ne bani jin daɗi gaskiya. Su basu ɗauke mu a matsayin ƴan uwa ba sai kaman masu aikin su kuma ba don basu da isassun masu musu hidima bane A'a! Don kawai a gwada mana matsayin mu ne"
"Nima idan na shiga wasan su Jamal kora ta suke yi wai wasan su ba na ƴan ƙauye bane" cewar Yaseer .
Kama baki Saudat tayi. "Kaji marasa kunyan yara, duk baka girme musu bane don sun samu ma kai ke binsu har zasu na maka rashin kunya?"
Kamal ya ɗaura hannu saman cinyar Yaseer ɗin gudun kada ya biye wa mahaifiyar shi su mulmula ƙaramin zance zuwa babba.
"Kuɗi shi ke bada matsayi ba shekaru ba. Ku lura mana cikin su Alhaji Tahir ne ƙarami Amma shine gaba a komi na hidimar family, ko family meeting za'a yi ba mai fara magana sai yayi, kuma idan ya bada shawara a take zai rikiɗe ya koma umarni, ba mai ja dashi a kan adalci ko rashin adalcin sa ba don komai ba sai don Allah ya wadata shi fiye da sauran. don haka kada kaji komai don ka girme su tunda nasu gidan kazo sai ka lallaɓa su har su barka ka shiga wasan ko?".
"Oh shima koya mishi jurar wulaƙanci kenan zaka yi?" Saudat tayi kicin-kicin da fuska.
Bai samu damar bata amsa ba kasancewar sun iso. Motoci ne kala-kala jere har kusan ƙarshen layin, shi yasa a tsallake mai napep yayi parking yana jiran su fita su sallame shi.
Kamal ya ɗauki Suhail dake barci saudat kuma ta janyo ƙaton cikin ta da ƙyar ta fito tana gyara zaman wuyan hijab ɗinta da baƙar jakar ta ƴar kullum wanda kwance ne Hajiya Fauziyya ta bata shine ya zamo mata na shiga taro.
Ta riƙo hannun yaseer yayin da Kamal ya biya mai adaidaita ya tafi sannan suka nufi gate ɗin tamfatsetsen gidan suna gaisawa da masu gadi don an riga an san su aka buɗe musu ƙofa suka shige. Saida suka ɗan taka suka sake shigewa gate na biyu kafin girman gidan ya daɗa bayyana da kuma mutanen dake hada² a cikin ta.
Saudat bata san me yasa jikin ta yayi sanyi ba ganin ta kusa saduwa da su sai dai shima kamal ɗin haka take a gurin sa, taya su murnar biki suka zo yi amma ba lallai a basu muhimmanci ba domin jiya da shekaran jiya ma haka ta kasance idan suka gama musu ayyukan da suke buƙata toh har su tafi ma babu wanda yake lura, kuma ko sallamar kayan biki ba'a musu tunda su ba komai suke kawowa ba. Saudat da tayi musu gudumawar kayan su muciya, bulogari, ƙoƙo, mara, tsintsiyar kwakwa dana laushi harma dasu kuka, busasshen kuɓewa, daddawa, barkono da kanwa daga ƙauye ce mata sukayi sun gode ba'a buƙata don an daina amfani da irin wannan tarukucen yanzu, shara da injin vacuum cleaner ake yi kaɗa miya kuma ga whisker. Shine tace musu har sharar harabar gida ma da injin ake yinta? To ai sai ayi mata da tsintsiyar sauran tarukucen kuma tayi kyauta da su ga masu buƙata. Haka dai ba daraja suka amsa ballantana ta saka ran samun godiya, bata bar gidan ba tana ji tana gani aka yi rabon kayan ma sauran ƴan aiki.
"Ke da Suhail ku shiga ɓangaren matan, zan tafi da Yaseer mu gaisa da masu gidan" Kamal ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Gyaɗa kai tayi ya ɗan bubbuga Suhail ɗin ya buɗe ido kafin ya sauƙe shi a ƙasa Saudat ta kama hannun shi sukayi cikin gidan yana mutstsuka idanu. Da duk wanda suka ci karo a hanya Saudat sai ta ɗan duƙa ta gaida su haka ma Suhail har suka isa babban falon da manyan hajiyoyi ke manne a kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya kowa tana faman kaɗa warwarayen gold ɗinta don yafi na ƴar uwarta ƙara, wa'inda basu kai su matsayi ba kuma ke kai komo na hidimar biki.
Samun wuri a ƙasa Saudat tayi ta zauna tana gaida su Suhail ma ya zauna gefen ta, wa'inda suka ga dama suka amsa gaisuwar sauran kuma suka yi kaman basu san da halittar ta a wurin ba.
Hajiya Hauwa da fitowar ta kenan daga uwar ɗaka bayanta biye da Hajiya Fauziyya ta kalli Saudat, ko damar gaida ta bata bayar ma Saudat ba tace "yauwa Saudatu sai yanzu kika iso? Dama ana niman masu wankin waken yin alalar yamma wajen Inna larai, kije ki same su a can".
Bata amsa ta ba sai cewa tayi "ina wuni Hajiya yaya hidima?"
Ɗan ƙaramin tsaki tayi sannan ta amsa da "lafiya lau"
"Toh Allah ya bada zaman lafiya, Allah yasa gidan zamanta ne"
Cikin ƙosawa tace "ameen ba zaki iya taimakon bane in samu wata?"
Nan ma bata amsa ta ba ta gaida Hajiya Fauziyya wanda ta amsa da murmushi saman fuskarta itama tana ɗauke da zungureren ciki aihuwa yau ko gobe tace "ina Yaseer ko ba'a zo mana dashi bane?"
"A'a yana waje tare da Abban shi."
"Toh yayi kyau" ta juya wurin Hajiya Hauwa "Umman Jamal barin je in shigo da su aunty Zeenat"
"A'a da dai kin bari an tura a shigo dasu, ke da kike fama da tsohon ciki amma sai ɗawainiya kike tun Safiya "
Kallon cikin jikin ta Saudat tayi, girman shi ɗaya da na Fauziyya ko ma ya fishi girma tunda ita ƙibar hutu dama cikin yasa jikin ta ya shanye shi, amma na Saudat gashi a ƙasa ranƙwalele shine kuma ake saka ta surfen wake bama yanka salad ko irin haɗa su zoɓo ba. Ko ita ba ɗan adam bane a cikin nata?.
Murmushi Hajiya Fauziyya tayi tace "zan iya, yanzu idan na shigo dasu zan samu in zauna"
"toh shikkenan a kula dai kar a wahalar mana da ɗa"
Nanma murmushi Hajiya Fauziyya tayi ba tare da ta sake cewa komai ba ta nufi hanyar barin parlourn.
Itama Saudat tashi tayi kafin Hajiya Hauwan ta sake cewa wani abu tace "barin je toh"
"Yauwa da yafi" cewar Hajiya Hauwa sannan ta shiga gaisawa da sauran hajiyoyin da zuwan su kenan cikin fara'a da annashuwa.
Haka Saudat ta ƙarasa ta bayan gidan wurin da ake faman haɗa kalolin abinci cikin manya manyan tukwane wanda zai ciyar da ɗaruruwan mutane. A cikin dandazon masu aikin ta tsinto Inna larai ta riƙo hannun ta don ta samu hankalin ta suka gaisa sannan tace. "Inna ance ana buƙatar ƙarin masu surfen waken alala, shine nazo"
"Lalala ƴar nan! Da wannan tsohon cikin zakiyi surfe kalan ki haihu a gidan biki ace ni na takalo miki naƙuda!"
Saudat tayi murmushi kawai "toh kije can ga su Rabi suna haɗa salad sai ki kama musu yanka kabeji ko kankare karas"
taji daɗin sauyin aikin da Inna larai ta bata duba da yanayin ta wanda wancan makauniyar ta kasa, haka kuwa tayi mata godiya sannan taje ta fara aikin ta cikin azama suna taɓa hira dasu rabi don sun ɗan saba.
...
Kamal da ya duba bai samu ko ɗaya daga cikin mazajen bane ya koma wurin masu gadi suna ɗan taɓa hira shima don zaman cikin gida ba nashi bane. Suna nan zaune motar yankakku kuma feɗaɗɗun shanu har guda 3 ya iso nan suka tashi ya shiga cikin su don taya mahautan sauƙewa sannan suka ɗunguma yanka naman gunduwa² da kuma faskaren ƙashi, don haka kafin a gama farar shaddar shi ta Sallah wanda sawa ta 3 zuwa 4 kenan da yayi mata tayi caɓa² da jini.
...
Wuraren ƙarfe 4:30 na yamma an gama cike motocin kai amarya da suka ƙaraso, saboda girman cikin ta Alhaji Tahir ya gargaɗi Hajiya Fauziyya da kar ta bisu. Hakan yasa ta yanke shawarar yin zaman ta har masu kai amaryar suje su dawo in yaso aka zo tafiya dinner da daddare sai taje, gashi dama bata wani jin ɗaɗi tun da rana ta fara yin sanyi.
Dagewa suka yi saidai ta kai musu amarya mota tunda ba zata bi ayari ba, haka kuwa akayi, ta rungume amarya Sakina tana faman turawa har jikin danƙareren farar jeep ɗin da aka kawo don ɗaukar ta suka amshe ta daga nan sannan ita ta koma ciki.