Sashe 31
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Daman a masallacin idi da safe ne na haɗu da malamin mu na Hadda. Shine yake min tayin koyarwa a makarantar na wucin gadi tunda ba yanzu zan fara zuwa makaranta ba. Yace ko wani wata dubu Sha uku albashin, kinga ko na wata 5 nayi zan tara wani abun da zai yi amfani idan admission ya samu."
Ta saurare shi har saida ya kai aya kana tace. "Toh yanzu yaya kake so ayi?"
Ɗan muskutawa kusa da ita yayi yace "dan Allah ki roƙa min Abbah ko zai yarda. Wallahi ina son zuwa, kuma kinga nima zan samu dama in duba wasu litattafan da bani da ilimin su in sake tisa wanda na fara mantawa. Kuma ai yafi zaman hakan nan ko Umma?"
"Shikkenan, idan ya dawo zan tunkare shi da zancen in sha Allah"
"Yauwa na gode Umma na. Allah ya saka muku da gidan aljannah"
Ta kalle fara'ar dake fuskar shi, da gaske yana son zuwan ne ba don kuɗin ba. Kana ta amsa da "ameen"
.....
_Sallah da kwana 8_
"Assalamu alaikum" Sallamar su yayi daidai da shigowar su saboda an riga anyi musu Iso.
"Wa'alaikumus salam." Hajiya Fauziyya ta amsa da rabin nutsuwar ta. Sauran rabin kuma na wurin Reina da take ƙoƙarin kai wa lomar abinci baki amma ta kawar da kai tana ta kuka.
Dungure Bowl ɗin Hajiya Fauziyya tayi ta miƙe cikin ƙosawa da kafiyar ta tana faɗin "kada ki ci!" sannan ta ɗan saki fuska domin ta gaida su Saudat don baki ɗaya tun da ta dawo a rikice take.
Reina ita ce da ciwo a jikin ta amma ita ke shan wahala.
"Me ya saka ta kuka kuma?" Saudat ta tambaya tana zama a gefen Reina cikin kulawar kada ta fama mata ciwo don ga ƙafafuwan nan a ɗaure.
"Wallahi ɓaci ne dai da kika santa da shi tun da. Kullum ayi ta fama da ita sai kace ita kaɗai ne ƴa!"
"Toh ana haƙuri dai Aunty, shi jinya daman sai an kai zuciya nesa, musamman ma na yaro don takura su zama wuri ɗaya yake yi."
Jinjina kai kawai tayi ta canza zancen zuwa tambayar anyi Sallah Lafiya?, saboda idan ma tana complain a kan ɓacin Reina ranta ƙara ɓaci yake yi.
itama Saudat tayi mata sannu da dawowa da addu'ar Allah yasa anyi Hajji karɓaɓɓe.
"Yauwa Umman Yaseer mu ɗan shiga daga ciki" hajiya Fauziyya ta buƙata tana fara wucewa.
Miƙewa tayi ta bita a baya suka shiga ɗakin ta dake ƙasa suka rufo ƙofa.
Yaseer ya kalli Reina dake faman sheshsheƙar kuka duk sai ta bashi tausayi ganin ƙunan da aka ce ta yin har wurin guiwar ta.
Haɗa su Sabir da kayan ciye-ciyen da aka kawo musu yayi kafin ya tashi ya koma kusa da ita.
"Reina"
Ɗagowa tayi ta kalle shi da fuskar ta da yayi caɓa-caɓa.
Ta ƙara girma, ta yi ƙiba, kaman ta ya ƙara canzawa.
"Kukan me kike yi?" Ya tambaya tare da bata dukkan attention ɗin shi don yaji menene damuwar ta.
"Ka kira min Daddy na pleash" tace cikin gunjin kuka amma sai dariya yaso kama shi ganin har wa yanzu bata da S. Sabir bai shekara uku ba harshen shi yayi kyau amma gashi tayi shida da sauran ta.
"Me yasa?"
"Yunwa nake ji"
"Yunwa kuma? Ba ga abinci ba?" Ya ɗago kwanon dake kan coffee table ɗin gaban su. Wani abu ne kaman macaroni a ciki amma tun da yake bai taba ganin kalan wannan ba, ga wani abu kaman kindirmo a jiki, shape ɗin shi wani iri amma kuma yana da kyau ko a idanu.
Kawar da kanta tayi "Ni bana ci,"
"Toh me zaki ci a kawo miki?"
"Daddy yace zai kawo min, donut da browniesh da cake ma. Ka kira shi don Allah" sai ga wasu hawayen ɓaci zirr suna bin kuncin ta.
"Yana aiki yanzu amma idan kika ci abinci zai kawo miki idan zai dawo"
"Toh ai babu daɗi ne"
Da mamaki ya kai cokali ɗaya bakin shi, sai yaji akasin abinda tace.
"Wannan da daɗi fah Reina, taɓa ki ji"
Kawar da kai tayi tana ƙara gudun hawayen ta "ni dai bani shoo"
Ya sauƙe numfashi, dole ran mahaifiyar ta ma ya ɓaci ne, amma barin ta da yunwa ba shine maslaha ba.
"Toh in barbaɗa mana nama a kai sai mu ci tare?"
Sai da ta ɗan tsaya tunani kafin ta gyaɗa kai. Ya ɗauko laidar da suka zo da shi sannan ya ciro kwanon samirar dake ɗauke da nama da cin-cin, ya ɗibi dambun nama mai ɗan yawa ya saka a kan abincin ya cakuɗa kafin ya kai mata lomar farko.
"Taɓa kiji, yayi ko a ƙara?"
Jan hanci tayi kana ta gyaɗa kai "yayi"
"Yauwa idan kika cinye har cin-cin zan baki mai daɗi sosai sai kunnen ki ya tsinke" yace don ya lura tana da son kayan zaƙi. kana ya ciro handkie a aljihun shi ya shiga share mata fuska, harda majinan dake hancin ta, sannan ya miƙa mata handkie ɗin "toh riƙe mana wannan"
Babu musu ta karɓa ta riƙe, tana cin abincin yana share mata baki da bata ruwa har ta tada bowl ɗin tass tana ɗan ƙaramin gyatsa.
Fitowar Hajiya Fauziyya kawai sai cin karo tayi da plate wayam.
~~~~~~~
*Zaku iya samun labarin daga farko zuwa wurin da aka tsaya a kan shafi na na Wattpad.*
*REINA 💍*
22....Wasa-wasa lokaci ya tafi.
Lokacin da Yaseer yake ganin zaman gida yayi masa yawa, ya tafi.
Lokacin da Hajiya Fauziyya ta ɗauka na Jinyar Reina, ya Tafi.
Lokacin da Alhaji Tahir ya ɗauka na jirar amincewar Alaji Abdou a kan sabuwar kasuwanci inji shi da faɗa, shima ya tafi.
Kusan za'a ce abubuwa da yawa ne suka faru a Rana guda amma lokaci mabanbanta.
.....
Kai kawo yake a cikin office ɗin shi, yana kallon agogon dake manne a bango, da wanda ke ɗaure a tsintsiyar hannun shi, da ma wanda ke fuskar wayar shi.
Tun daga lokacin da ya yanke shawara da zuciyar shi, da ilimin shi, da kuma experience da yake da shi na shekara da shekaru a kan harƙar samu da kuma sarrafa kuɗi, Hankalin shi ya samu wuri ya kwanta kaman tsumma a randa. domin yana da tabbacin sai yayi dariya ma Alaji Abdou, kuma zai goranta mishi rashin amfani da damar da yazo har cikin tafin hannun shi kuma ya bar shi ya suɓuce.
Saidai fa a yau ɗin da lokaci ya ƙarato, a maimakon ya samu kan shi da murna sai kuma fargaba tazo ta shanye shi. Bayi son zana ko ɗigo na shakku a kan zuciyar shi amma yana tsoron harsashen alaji Abdou ya zamo gaskiya.
Cikin saabo da hanzari, dogon hannun agogo ya tsallaka kan lamba ta sha biyu yayin da shi kuma guntun hannu a kasalance yayi nuni da lamba ta goma daga nesa.
Lokacin da suka bashi ya cika!.
Numfashin Alhaji Tahir ya ɗauke cakk na sauran sakwannin da suka ratsa har sai da saƙon Email ɗin da yake jira ya shigo lokaci ɗaya tare da wani saƙon, wanda ya bayyana sunan ɗaya daga cikin bankunan da yake amfani da shi a fakaice kafin ya koma sama ya ɓuya, zuwa lokacin da buƙatar mai saƙon zai tilasta shi ya janyo shi don ya duba.
Sai komai ya tsaya mishi, kunnuwan shi suka daina jin wani abu bayan bugun zuciyar shi, Idanun shi suka daina ganin komai bayan wayan da ke hannun shi, yayin da yatsar shi ya danna kan saƙon email ɗin ya buɗe ta sannan ya shiga karanta abinda aka rubuto.
Bai gama yarda da abinda ya gani ba har saida ya janyo saƙon ɗazu da yayi masa ƙwalele ya shiga ciki, idanun shi suka yi arba da maƙudan kuɗaɗen da suka shigo account ɗin shi.
Dala miliyan ɗari da hamsin.
Jiri yaji kaman yana shirin ɗiban shi, ya ɗan dafa jikin teburin gaban shi amman bai zauna ba. Sake karanta yawan kuɗin yake yi, yana jin wani diri a cikin kan shi. Ba don bayi da kamar hakan ba, amma ko a shekara Ribar duk wani reshe na TK Kingdom idan aka haɗa ba zasu ɗare hakan ba. Kuma ba nashi shi kaɗai bane harda sauran masu hannun jari. Amma yau a cikin wata uku kacal ya samu ribar Dala miliyan ɗari ba tare da zufar shi ba, wanda idan aka juya shi zuwa naira toh biliyan ne da ɗoriya mai yawa ya samu a ɓagas!. Sai kawai ya shiga nanata hasbunallahu wa ni'imal wakeel a kan harshen shi don ya samu nutsuwa ta dawo mishi.
Ruwa ya sha kana ya samu wuri ya zauna ya dannan kiran lambar Fauziyya.
Har ya shiga bugu ɗaya sai kuma yayi saurin yankewa kafin ta kai ga ɗauka, ya maida kiran ma Alaji Abdou, domin so yake yi ya nuna mishi ɓacin ran shi da ya hana shi shiga da dala miliyan 200 kaman yanda yayi niyya, ƙarshe da ya gaji da jiran shi ne kawai ya shiga da dala miliyan 50 a sirrance. Gashi ta hayayyafa har da jikoki.
Saidai ya kira har sau biyu ba'a ɗauka ba. Saida na ukun ma ya kusan tsinkewa kafin Alaji Abdou ya ɗauka tare da yin sallama muryar shi a sanyaye.
"Wa'alaikumus salam. Abdou daman mai na faɗa maka?... Pro"
"Malika Ta Rasu Tahir. Yanzu zamu kaita makwancin ta" ya faɗa muryar shi na karyewa. "Idan na dawo zamuyi maganar koma menene, ko zuwa gobe ma, ko anjima da safe, ina zaka iya jira?"
Abinda bai taɓa fata ba shine ganin abinda zai rikita Alhaji Abdou, duk tashin hankali da bala'in ka saidai kayi ka bar shi, amma yau gashi ya gani.
"Ina hanya nan da awa ɗaya in sha Allah" shine abinda yace amma bayi da tabbacin Alaji Abdou ɗin ya ji saboda katse kiran da yayi a lokacin.
A gaggauce ya kira Hajiya Fauziyya ya sanar da ita ta shirya zasu wuce Nijar yanzu.
....
Ajiye wayar tayi tare da duban Reina da ta ƙwace glass bowl ɗin hannun Maama wanda ke ɗauke da butter da kuma sugar a ciki tana ta faman juyawa.