Sashe 7
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gefen ta Hajiya Fauziyya ta ɗan bubbuga mata alamun ta zauna, Saudat bata yi ƙasa a guiwa ba kuwa ta zauna sannan ta jawo Suhail jikin ta gudun kada yayi musu ɓarna, Yaseer kuma ta barshi a parlour.
*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*
*REINA 💍*
BookNest, Wattpad and arewabooks @seemahwrites
05..... Sai da suka gaisa da Inna Larai ta bar ɗakin don zuwa yin abinda ya kawota kafin Hajiya Fauziyya ta dubi Saudat tace "Hmm.. ai daga sha ɗaya ta gifta toh fa ba zamu rintsa ba sai safiya, haka zata kwana tana rikici gashi kuma bamu rabuwa da baƙi wataran har sha biyun dare, da safiyan ma haka" ta ƙarashe tana cire bakin Reina daga jikin ta nan kuwa ta shiga yamutsa fuska tana motsa baki alamun bata ƙoshi ba, ta gyara mata rufuwa a cikin towel ɗinta mai taushi da kyau yasha turaren yara mai daɗin ƙamshi. sannan ta miƙa ta a hannun Saudat da bata yi tsammanin hakan ba, tunda ranar da aka haifeta sun hana ta ɗauka shiyasa ta cire ranta daga taɓa musu ƴarsu.
A kan cikinta ta ɗaura ta ganin bata da nauyi sannan ta shiga ƙarewa fuskar Reina kallo lokacin da ita kuma ta fara ƙananun koke-koke. Jinjina kai Saudat tayi tace "toh kuma ba wani abun yake damun ta ba? Ko ciwon ciki? Ko tsamin jiki?"
"Ko ɗaukan ta ƴan gaisuwa basa yi Umman Yaseer saboda gudun ko hakan ne, maganin ciwon ciki kuwa har su jar gauta mun jiƙa mun bata Daddyn ta bai sani ba, na Islamic da na asibitin ma mun siya mun gwada shiru babu wani canji"
"Kinsan yaro ba baki yake da shi ba, ciwo zaiyi ta nuƙurƙusan su ba zasu iya faɗa ba, da kuje kuga likita kada wani abin ne" Saudat ta faɗi hakan ne kawai ba wai don tana tunanin wani abu yana damun Reina ba domin gashi ta cika fata tayi kyau fiye da yawancin jariran da basu samun kulawa kamar ta, amma kuma shi ciwo ba'a gane shi da ido.
"Nifa Inaga rikici ne irin na baby Hafsah ba komai ba, soboda bata ƙin karɓan nono ko kaɗan, kuma idan zamu kwana ina bata ba zaki ji bakin ta ba ni kuwa ina zan iya? watarana har amai take yi tsaban zalama"
Saudat ta murmusa tana jin sha'awar haihuwar ƴa mace yana daɗa shigar ta, fatan ta ace abin dake cikin ta mace ce da taji daɗin ta domin tafi sha'awar su a kan ƴaƴa maza. "Lallai yarinyar mai babban suna ce" tace tana mayar ma Hajiya Fauziyya Reina saboda kukan ta ya fara tsanani.
Sake zuge zip ɗin rigar ta ƙasa tayi tana faɗin "Aina'u haɗa mana Madara don Allah, daga wannan na gaji wallahi".
Mai aikin dake maida kayan Reina da aka wanke aka goge su cikin drawers ta miƙe a take tare da faɗin "toh Hajiya" sannan ta bar musu ɗakin.
Saudat bata lura ba ashe har Suhail ya siɗaɗa ya ɗauko abin wasa me kacau-kacau yana kaɗawa.
Ta miƙe da sauri ta wafce daga hannun shi tana mishi faɗa.
"Da kin bar mishi ai, tana da wani idan yana so ya ɗauka" cewar Fauziyya.
"A'a wallahi Aunty, ɓarna ne kawai yake ji dashi" Ta mayar da abin wurin da ya ɗauka, "saida nace ma ya zauna wurin yayan shi a parlour yaƙiya"
Ƙofar ɗakin ne ya buɗe Aina'u ta shigo ɗauke da rubber mai ɗauke feedern Reina a ciki wanda ta tafasa yanzu za'a haɗa mata madara a ciki.
"Kije parlour ki shigo min da Yaseer Aina'u" tace ba tare da tabi ta kan Saudat ba, daga uwar har ɗan halin su ɗaya.
Sai da aka bashi izinin shigowa bayan yayi sallama kafin ya turo ƙofar ɗakin a hankali. Ganin shi bai sauƙa a ko'ina ba sai kan Hajiya Fauziyya dake bawa Reina Nono, yayi saurin sauƙe kanshi ƙasa tare da faɗin "Aunty gani"
"Toh ƙaraso ciki mana, ko har mun fara surkuntakar ne?" Tace cikin sigar zolaya.
A kunyace ya sosa ƙeyar shi kafin ya taka wurin da suke zaune saman gado.
"Zauna in baka ƙanwar ka" tace tana mishi nuni da tsakanin ta da Saudat da Ido.
"Aunty kema kina da biyewa yara wallahi" Saudat tace tana dariya, har cikin ranta wani karama da daɗi take ji. abinda take buƙata a gare su kawai kenan, suma ayi treating ɗinsu kaman sauran mutane wanda Allah ya yassarewa abin duniya, a daraja su a mutunta su shikkenan abin ba wahala, ba don Allah bayi son su bane ya zaɓi ya hana su, idan da yaso sai sufi kowa arziƙi ma a gidan duniya duk wannan abu mai yiwuwa ne a wurin shi, amma tasu kalar jarabawar kenan, domin da ya hana su kuɗi bai hana su zaman lafiya da ƙaunar juna ba.
Yaseer ya zauna Hajiya Fauziyya ta saka mishi Reina a kan cinyar shi, ya kuwa riƙeta da kyau yana kallon farar fuskar ta da har yellow-yellow yake masa a idanu ga bakin da take faman turo shi yawan tsotso yasa yayi jajawur, ga kuma nanannen hanci. Amma kuma kumatun ta abin sha'awa .
"Yanzu kam Reina ta fara kyau ko yaro na?"
Da sauri ya ɗago kai ya ware idanu kaman ta karanci zuciyar shi. Gyaɗa mata kai kawai yayi, yana tunanin amma fa idan hancin nan bai taso ba akwai matsala.
Suna zaune aka fara shigo da trays ɗin abinci, ganin yawan kulolin yasa Saudat yin tunanin kodai baƙi Hajiya Fauziyya zata yi don haka ta miƙe tare da saka hannun ta a bakin zanin da take ɗaure da shi ta zaro dubu ɗayan da kamal ya bata da safe wanda za'a kaiwa mahaifiyar shi tunda tana da wani in yaso sai ta mayar masa.
Ta cikin hijabi ta warware kuɗin sannan tace "Aunty bari mu wuce, Almuru ta gabato, Allah ya raya mai babban suna ya baki lafiyar shayarwa" sai ta ajiye mata kuɗin a gefen ƙafarta "gashi ba yawa" bata san ma me zata ce a siya ma jaririya da dubu ɗaya ba, donmin tana da tabbacin ko abin goge kunnen ta ya bawa dubbanni baya.
"A'a Umman Yaseer saida aka kawo mana abinci kuma zaku tafi? Saboda ku fa na jinkirta mana wankar yamma"
Maganar su ya saka cikin Yaseer ƙara yin ƙugi ya lumshe idanu a kunyace, shi ba kwaɗayin abincin su yake ji ba kawai yunwa ne ya dame shi domin yasha trekking daga hadda babu komai a cikin sa.
"Na san Almuru ta gabato ne aunty samun abin hawa."
Ta nuna mata agogon dake bango "kinga ma yanzu za'a kira sallah, ku tsaya kawai idan mun gama in saka a maida ku."
Suhail da yaga abinci har ya ajiye kacau-kacau ya dawo jikin umman shi yana tsallen murna yana nuna mata manyan yankan naman da suke masa Hi yana nuna su wa Saudat, "Umma nama" yace cikin jin daɗi. Sai faman buge mishi hannu take yi saboda kunya Fauziyya kuwa yi tayi kaman hankalin ta bayi gare su.
Aka gama saka musu abincin duka suka sauƙa ƙasa, Fauziyya kuma aka ɗaura mata nata a kan ɗan ƙaramin coffee table sannanta karɓi Reina ta ajiye ta don Yaseer ya samu jona maman shi da ƙanin shi, shima anyi masa plate ɗin shi daban yaji komai.
Kiran Alhaji Tahir ne ya shigo wayarta ta ɗauka suna magana ƙasa-ƙasa, Saudat kuma ta riƙe hannun Suhail duka biyu tana bashi abincin a baki gudun kada ya ɓata musu carpet.
Sun kusan kammalawa aka yi knocking ƙofa sannan ba tare da niman jiran izini ba suka turo ƙofar suka shigo, nan hankalin su baki ɗaya ya koma kan masu shigowa, suma masu shigowar idanun su ya sauƙa kan Su saudat, sai kawai aka tsaya kallon kallo na ƴan sakwanni.
Buɗar bakin Hajiya Hauwa tace "me zan gani haka ni kuluwa, Fauziyya? Su waye kika kawo uwar ɗakin Tahir?"
Yaseer ne ya fara tsame hannun shi daga cikin abincin ya kawar da kanshi gefe hawaye na taruwa a cikin idanun shi, cin fuska ko wani iri ne zai iya jurewa amma yaƙi jinin ana cin mutuncin mahaifyar shi.
Murmushi Hajiya Fauziyya ta daura saman fuskar ta kafin tace "Sannun ku da isowa Umman Jamal, sannu da zuwa Hajiya Addah Bismillah" tace da hajiya lubabatu wanda isa ma ya hana ta magana sai kallon banza da take bin su Saudat dashi, jin kanta take yi kaman itace uwar su Alhaji Tahir ɗinma.
Haƙura dai suka yi suka shigo ɗin ganin yawan mutanen dake parlourn, bayan su ma'aikata ne ɗauke da akwatuna niƙi-niƙi suka wuce dasu gaban gadon Hajiya Fauziyya suka dire su a jere sannan suka fice tare da rufo musu ƙofa. Saudat ta so ta jasu su bar ɗakin a lokacin da ake shigo da kayan amma dandazon su har ya cika ɗakin duk girman shi, bata da zaɓin da ya wuce ta ci gaba da zama a wurin har suka isota.
"Baki bamu amsa ba Fauziyya, su waye wannan?" Hajiya hauwa ta sake tambaya kaman irin basu san sun nan ba ganin Hajiya Fauziyya ta share maganar.
"Au, umman Yaseer ne tazo min barka"
"Barka? Shine har cikin uwar ɗakin Tahir?"
Miƙewa Saudat tayi, Yaseer ma yayi saurin miƙewa. Kallon kayan da suka zo dashi tayi, akwati ne mai huɗu-huɗi set biyu irin manyan nan da basu da kit.
"Aunty mun wuce, Allah ya ɗayyiba"
"Ameen umman Yaseer na gode Allah ya saka da alkhairi, ku gaida gida" gudun kada ta jawo musu wulaƙanci yasa ta manta zancen kaisu gida da tace za'a yi.
Saudat ta zaga su zata wuce sai Suhail ya sake ɗaukan abin wasan da ya ajiye saboda abinci, da sauri Jamal yazo ya fauce da ƙarfi sai Suhail ya ɗaga idanun shi da suka cika da ƙwalla yana kallon cikin idon Jamal da ya zaro su cikin son firgitarwa. ƙarfin hali kawai Yaseer yake kallo ganin cewa mai abun ma ta mishi izinin ya tafi dashi. "Idan baka daina kallo na ba I'll slap you" ya faɗa yana ɗaga hannu da niyyar sauƙe mishi marin.
Yaseer ne yazo ya ɗauke shi yana zare nashi idanun ma Jamal da duk taurin kanshi saida ya firgita sannan Yaseer yayi saurin barin ɗakin dashi.