← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 57

Sashe 37

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki yaja ya miƙe zai bar wurin ya hango Meesha na tahowa da dorinar da ta aro a wurin security.
Ya sake jan wani tsakin tare da faɗin "mahaukaciya kawai" dolen sa ya koma ya zauna, ita kuma ta ƙaraso wurin ta zauna tayi banke-banke tana cinye abin motsa bakin da ta kawo ma Yaseer ɗin.

Haka dai aka yi koyarwar ranar cikin aminci da taimakon Meesha amma Jamal dai kaman kurma duk abinda Yaseer ya tambaye shi ya gane sai kawai ya gyaɗa kai shi kuwa ya wuce abun sa.

Saboda tsare shi da tayi da surutu bai bar gidan ba sai bayan sallar maghriba. Tun kafin ya fita tace masa bari taje ta ɗauko mota amma yayi banza da ita yayi wucewar shi.

Motar Hajiya Hauwa taje ta aro ta fito ta same shi yana takawa a sayyada kasancewar dare abun hawan ba sosai ba a layin.

Horn ta matsa da ƙarfi kafin ta zuge glass ɗin ɓangaren shi haɗe da faɗin "shiga mu tafi"

"Mu tafi ina? Hankalin ki yaje aika ne zaki ɗauki gardi a mota da daren nan? Idan muka je ki dawo ke da wa?"

"Me zai same ni toh? Ai ba yau na fara fita ni kaɗai a mota ba balle, kuma babu inda zan bi, ina sauƙe ka zan juyo"

"Ni dai ki koma idan baki son mu ɓata" ya cigaba da tafiya itama taci gaba da bin shi a motar.

"Idan baka shiga ba haka zanyi ta bin ka ina cika maka kunne har mu isa" ta ƙara matse horn da ƙarfi fiye da na da.

Haka dole ya shiga yana mata kwatance har suka isa unguwar su.

"Ko in biyo ka ne in gaida Umma?" Tace bayan ya sauƙa daga motar.

Harara ya watsa mata "amma kin fara zauncewa ko? Kuma ki saka a maida ke gida a daren nan kinji na faɗa miki"

"Toh my Yaseer " ta amsa tana daga mishi hannu, ya tsaya yaga ta tada motar ta bar unguwar kafin ya juya zai shiga lungun da zai kai shi gidan su sai Muryar Abban shi ya ji a bayan shi.

"Har gida suka dawo da kai? Lallai sun kyauta" yace cike da jin daɗi.

Rage tsayi Yaseer yayi ya gaida shi sannan ya amshi ƴar laidan hannun shi wanda ya siyo rake. Suka jera har gida yana tambayan shi wai ya bashi labarin abinda ya faru a gidan koyarwar shin.

Saudat da yara suna ɗaki saboda akwai wutar nepa suka shigo. Yaran suka yi ma kamal oyoyo tare da gaida shi kafin ya zauna yana mayar mata abinda yaji daga bakin Yaseer da kuma wanda ya gani.

"Saudatu kinga ƙudirar Allah ko? Har mun fara ganin ribar karatun yaron nan tun ba'a je ko ina ba"

"Hmm" kawai tace domin baki ɗaya hankalin ta ya gagara kwanciya da zancen shigan Yaseer cikin mutanen nan. Basu da daɗi, basu daraja ɗan adam sannan kan su kawai suka sani, tana tsoron suyi ma yaronta wani abu na cutarwa.

Kusan kamal shi kaɗai ya ƙaraci hirar shi har aka tashi daga kallon lokacin da aka kira Isha sannan ta kira Yaseer ya dawo bayan kowa ya fita.

Hannun shi na dama ta riƙo cikin nata biyu, "Dan Allah Yaseer ka iya zaman ka da mutanen nan, babu ruwan ka da sha'anin su kayi abinda ya kai ka kawai. Kaga mu ke nima a ƙarƙashin su don haka a kai zuciya nesa dan Allah, sannan ko shi yaron da kake koyarwar ban yarda da hukunci ba, dukda na san baka da saurin hannu amma ka bishi a lalama har a gama lafiya"

In sha Allah umma, ya amsa da sakin fuska don hankalin ta ya kwanta, daman shima hidiman su ba tsole mishi idanu yayi ba.

.......

Da Hajiya Fauziyya ta gama faɗa ma Reina a kan yanda take saka Maama a gaba da duka kaman jaka bayan ita babu wanda ya isa ya taɓa ta shine tayi fushi ta koma parlourn daddynta suka ƙarata a can har ya shiga ɗaki ya barta tana kallo.

Tashar Nickelodeon take kallo daga farko kafin ta ɗauki remote ta shiga canje-canjen channel har ta kai wani wanda ake gwada program 18+ sai ta gyara kwanciya tana tunanin inama ace da yaya Jamal suke wannan kallon, suna yi tana tambayan shi abinda bata ganewa yana mata bayani, harma yana gwada mata wasu abubuwan da yanzu sun fara mata daɗi ta fara sabawa dasu.

Ana cikin haka Hajiya Fauziyya ta shigo yin light off idanun ta ya sauƙa a kan abinda ake yi a TVn ta ƙaraso zata kashe shi sai ta hango Reina kwance a kan 3 seater. Ita tama manta da tana nan don har taje ta kwantar da Maama ta kashe musu wuta.

"Reina?" Ta kira ta domin ta tabbatar ita ɗin ne take kallon wannan abun.

A take ta haɗe fatar idanunta ta rufe su ruff kamar mai barci. Har Hajiya Fauziyya ta zago gaban kujerar bata ko motsa ba banda zuciyar ta dake lugude.

Itama Hajiya Fauziyyar dake bata jin daɗi don haka bata bada abun muhimmanci ba ta fara canza channel ɗin kafin ta kashe TVn ta shiga wurin Alhaji Tahir.

Yana zaune a bakin gadon sanye da jallabiya ash yana lissafi kaman yawancin lokuta ta shigo.

"T. kai ne ka bar channel ɗinnan a kan wani program ga yarinyar nan a kwance a wurin? Idan ta farka taga abinda bai dace ba fah?"

Da mamaki ya ɗago ya kalle ta, yace "SpongeBob ake yi a Nickelodeon tace in bari mata, saidai hala da aka gama ne take neman wani channel ɗin barci ya ɗauke ta shi yasa ya tsaya a kan wancan ɗin"

Sauƙe numfashi tayi "Idan na samu zama ma duk goge su zanyi"

Yayi dariya "kullum dai haka kike cewa Fauzah".
Sannan ya tura littafin gefe ya miƙo mata hannu, a kasalance ta ƙaraso ta zauna.

"Yaya kufayin jikin yanzu? Ai da kin bari ma yau ni nazo"

"Na ɗan ji daɗi bayan ruwan da aka ɗaura min ɗazu har na samu ma naci abinci"

"Alhamdulillah, amma wannan ɗan daddy yana wahalar damu."

Juya idanunta tayi tace "waye yace maka ɗan daddy ne? Idan kuma wata Princess ce aka sake samu fa tunda kana da sarauniya"

"Ni ina ji a jiki na ma ɗan daddy ne, In sha Allah namiji zaki haifa" ya amsa yana shafa cikin da bai fara tasowa ba kasancewar tana cikin watan ta na biyu kenan.

Sai taji jikin ta ya ɗan yi sanyi ganin kaman yanzu ma idan ta sake haifar mace ba zai yi farin ciki da hakan ba.

"Toh kaje ka kai Reina bedroom ɗinsu sai ka dawo"

"Toh Hajiya. Ya amsa tare da miƙewa"

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*

*REINA 💍*

26....... Washe gari da Yaseer ya koma gidan su Jamal bai samu Meesha ba, don haka ya saka ma ran shi wannan karon ma taji maganar shi ne ta koma gida.

Samun wuri yayi ya zauna bayan ya gaida su kaman jiya, shiru yau ma har ƙarfe 10 ta gifta Jamal bai fito ba. Ya kuma rasa waye zai tura a kira masa yaron gashi bayi son ɗaura ma Meesha nauyi don kawai tayi mishi Lamuni.

Haka ya ciro wayan shi yana ɗan daddannawa sai ga Jamal ya fito, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san ba lesson ya fito ba, domin yana sanye ne da wata baƙar leather jacket da skinny jeans, ya ɗaura jan bandana a goshi, yatsun shi na kaɗa key ɗin motar uwar shi.

Haka suna kallon kallo shi da Yaseer, yana faman fiito ya faɗa cikin motar ya ja yayi masa wuta ya fice a gidan.

Bayi juran wulaƙanci bayi ɗaukan ta ko kaɗan, amma ai Jamal ba shi ya ɗauke shi aiki ba, don haka ci gaba da zama yayi duk da ran shi nayi masa ƙuna.

Sai bayan fitan shin da kusan minti talatin kafin Hajiya Hauwa ta saka a fito a bawa Yaseer haƙuri wai ita ta aiki Jamal.

Shi kuwa sauƙin shi, da Jamal ya maida hankali da bai maida hankali ba idan wata yayi dole zasu biya shi albashi tunda ya zo, don haka ya koma gida yaje yayi wankin kayan da ya dawo dasu daga makaranta masu datti.

.......

"Wallahi sai na faɗa ma Aunty" cewar Maama cikin muryar kuka tana matsar ƙwolla, Reina kuma ta matse ta a jikin bango tare da taka mata ƙafa cike da mugunta.

"Ki faɗa mata don Allah baƙar munafuka, Idan naga dama ko Auntyn bata isa ta ƙwace ki daga hannu na ba!" Tace tana ɗibe ta da ƙananun maruka saboda kada yayi ƙara a jiyo su a kawo mata ɗauki.

Sanye suke da uniform maroon domin dawowar su kenan daga islamiyya, saboda Fauziyya bata jin daɗi Aina'u ta basu abinci a parlourn sama, idan sun ci sai ta canza musu kaya. Bayan sun gama ci ne kowa ta ɗauki plate ɗinta ta wuce da shi kitchen domin ta wanke kaman yanda Fauziyya ta mayar doka a gidan, shine rashin ganin idon Auntyn ya sanya Reina saka nata plate ɗin mai kyau da tsada a shara saboda kada ta wanke.

"Kuma wallahi sai na faɗa mata abinda kike kalla kullum a tab ko TVn Daddy, ai ina kallon ki ba barci nake yi ba!"

A razane Reina ta makure ta cike da tsoro, ta san ta kuskura ta yi sake wannan maganar ya shiga kunnen Aunty toh wallahi sai dai buzun ta a gidan.

"Ke ni sa'ar ki ce? Don kinga Auntyn ta fi son ki shine zaki na ƙulla min munafurci?!"

Ganin Maama ta fara ƙaƙari tayi saurin sake ta lokacin da idanun ta ya sauƙa a kan Lighter irin na gas a saman cabinet ɗin sama. Ɗalewa kan kanta Reina tayi da nufin ta ɗauko sanin cewa tsayin ta ba zai kai ba, Maama kuma na ganin ta saketa ta ɗiba da gudu ta fice daga kitchen ɗin tana ƙwala ma Auntyn kira.
Chapter 37 · 0% Book details