Sashe 2
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanyar ta na komawa Yaseer yayi saurin shan gaban ta. Ta ɗan firgita da gudun da ya ɗibo ganin sauran kaɗan ya mangare mata ciki amma tana gane shi sai itama ta saki fuska. "Yaseer yaya school" ta tambaya hannun ta a kan cikin tana fitar da numfashi.
"Ina wuni aunty" ya rusuna har ƙasa don gaida ta.
"Lafiy..." Amsar ta ya katse ganin Yaseer ɗin ya miƙe hannun shi riƙe da ɓawon ayaba da aka ci aka yasar akan interlocking ɗin wanda ba don Yaseer ɗin yayi saurin tsare ta ba, toh da tabbas ta taka shi zamewa zata yi ta faɗi.
"Wayyo Allah yarona na gode. Ka ceci rayuwar ƙanwar ka" ta shafa cikin tare da faɗaɗa murmushi.
Shima murmushin ya mayar mata don shi dai matar tana birge shi ba don komai ba ko dan yawan fara'ar ta. Bata da yawan magana sai murmushi kuma ita kaɗai ce idan ya gaishe ta ko iyayen shi suka gaida ta take amsawa cikin mutuntawa.
"Kaci abinci?" Ta tambaya cikin kulawa.
Girgiza kai Yaseer yayi alaman A'a.
"Muje ciki a saka maka kaci" ta fada cikin dakakkiyar murya sanin cewa zai iya mata musu don yana da kawaici, yana buƙatar abu amma idan ka bashi sai yace maka 'A'a na gode' ko kuma 'ki barshi kawai'.
Babu musu ya bita a baya har cikin babban parlourn Hajiya Lubabatu uwar amarya. Sannan tace a saka mata abinci.
Babu ɓata lokaci aka kawo mata plate ɗauke da fried rice, gefe ga stir fried spaghetti mai ɗauke da veggies yasha nama sai kuma kwatan kaza a saman shikafar da coleslaw a gefe ga alalen laida da aka riga aka ɓare mata aka saka wuƙa aka yanka gida hudu sannan aka zuba onion sauce a kai don a tunanin su ita ce zata ci. Sai kuma disposable cup dake ɗauke da kunun aya an rufe da murfin shi an zura straw a ciki don sauƙin sha.
Kiran Yaseer tayi ta ajiye mishi plate ɗin a kan dining table sannan tace ya ja kujera ya zauna ya ci.
Ya haɗiyi miyau ganin kayan daɗin da aka shaƙe plate ɗin dashi sannan a maimakon ya zauna sai ya ɗauki plate ɗin a hannun shi.
"Zan kai muci da Umma na Aunty" haka kowa yake ce mata Aunty tunda bata taɓa haihuwa ba tukuna ballantana a lanƙaya mata sunan abinda ta haifa.
"Umman kan itama bata ci abincin ba?" Fauziyya ta tambaya cike da mamaki.
Sanin cewa Saudat ba zata iya samun abinci taci ita kaɗai ba tare da ta kira shi, shi da Suhail ba yasa ya girgiza mata kai kawai.
"Indo kawo wani plate ɗin abincin" ta umarta.
"Ma waye ne aunty?" Indon ta tambaya gudun kada ta sake zuba bajintan ta a sake kyautarwa.
"Ma nice, ki saka min tuwo da zobo kuma ya ji nama"
"Toh Aunty" bata da zaɓin da ya wuce tayi yanda aka ce da ita.
Saida aka gama zubawa aka ajiye a saman dining sannan tace da Yaseer "kaje ka kira umman ka da ƙanin ka kuzo ku ci a nan" ta faɗa don itama bata kiyaye sunan Suhail ba. Shima da "Toh Aunty". Ya amsa, Ya fita da gudu don kiran umman tashi".
Mrs Imran ✨
*REINA💍*
BookNest, arewabooks and Wattpad @ Seemahwrites
بسم الله الرحمان الرحيم
02...... "Toh aunty" ya amsa mata sannan ya fita kiran Saudat. Hajiya Fauziyya bata bar wurin ba har saida Yaseer ya dawo tare da umman shi da ma Suhail wanda yake ta mata mitan yana jin yunwa shine Inna larai tace bari taje ta karɓo masa tuwo, kafin ta dawo ne Yaseer yazo yace Aunty na kiran Saudat amma bai faɗa mata dalilin kiran ba.
"Gani Aunty" Saudat ta faɗa tana shirin kai duka ma Suhail wanda yanzu ya fara kuka saboda yin arba da abincin dake kan dining a gaban Hajiya Fauziyyan. Miƙewa tayi da ƙyar sannan ta nuna ma Saudat ɗin kujeran da ta tashi.
"Ki samu ki bawa yaran abinci. Ni barin shiga ciki in ɗan watsa ruwa ko zan ji daɗin jiki na" da faɗar haka tayi shigewar ta ɗakin dake kusa da dining area wanda na musamman aka bar mata ta tare a cikin sa har a gama hidimar biki duk da kuwa ba a gidan take kwana ba, da kanshi Alhaji Tahir yake maida ta gida duk dare saboda kiyaye abinda ke cikin ta.
Tana ƙulewa ciki Saudat tayi saurin zama don itama yunwar take ji. Anyi rabon abinci bayan sun gama aiki amma ba'a bata ba ganin itama ƴar cikin gida ne tana da damar shiga ciki ta ci, Itama kuma sai bata yi magana ba har saida Suhail ya fara mita kafin Inna larai ta fahimci halin da suke ciki.
A nutse Yaseer ya fara cin tuwon domin ya bar musu shinkafar su ci. Saudat tasa cokali ta fara baiwa Suhail a baki amma sai ya janyo plate ɗin saboda ƙaguwa ya luma yatsun shi ciki yana dunƙulo manyan loma yana jefawa a baki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ɓata wurin ya kuma ɓata kayan shi da maiƙo.
....
Hajiya Fauziyya na shiga ciki ta sanya wa ƙofar sakata kafin ta shiga rage kayan jikin ta ta ɗaura madaidaicin towel. Har ta isa ƙofar bathroom Amma murɗin da taji cikin ta yayi wanda saida ya saka ta saki ƙaramin ƙara yasa ta dawo a hankali ta cire sakatar sannan ta shiga ban ɗakin, haka shima tura ƙofa kawai tayi ta daidaita temperature na ruwan da ɗan zafi sannan ta sake ma kanta shower.
A daddafe ta ƙarasa wankan ta kashe shower, taso ta tsane jikinta tun a cikin bathroom amma abin da take ji yana niman wuce tunanin ta hakan yasa ta tako a hankali ta fito tana kama garu. Niman wayan ta ta shiga yi saidai ta manto shi wurin da ta zauna a kan dining.
Fara jero 'hasbunallahu wa niimal wakeel' tayi tana addu'ar Allah ya bata ƙarfin sanya sutura a jikin ta kafin wani ya shigo ya same ta cikin wannan yanayi.
Ta samu nasarar maida undies ɗinta da ƙyar, amma kafin tayi aune ruwan ta ya fashe!.
Wai-wai ta fara tana yarfa hannuwa, sai dai ganin zata iya kwana a haka babu wanda ya jita gashi abu sai gaba-gaba yake yi yasa ta ƙwalla ƙara, tana buga jikin gadon da iya ƙarfin ta tana matsar ƙwolla.
....
Sun kusan tada abincin dake plates ɗin duka suka fara jiyo sautin bugun da Hajiya Fauziyya take yi amma sai Saudat ta basar ganin ba abinda ya shafe ta bane.
"Umma kinji kamar ana bugun ƙofar can" Yaseer ya nuna ƙofar ɗakin da Hajiya Fauziyya take.
"Anya kuwa? Wataƙil wani abun dai take bugawa a ciki". Saudat tayi ƙoƙarin kawar da ko wace irin mummunan tunani a ranta suka ci gaba da cin abincin su.
Wayar dake gefen plate ɗin tuwon Yaseer ne ya fara ruri, ya jawo ta sannan ya miƙa ma Saudat.
"Umma wannan kamar wayan aunty"
Serviette ɗin da ke tsakiyar dining Saudat ta ciri ɗaya ta goge hannun ta da na Suhail don kada shi ma ya damƙi wayar ya ɓata musu sannan ta karɓa wayar yayin da kiran ya yanke a take kuma wani ya sake shigowa ta duba sunan mai kiran don tabbatar da wayar wacece.
'Habeeby Da'eeman' ta gani as caller ID sai kuma hoton bikin Alhaji Tahir ɗin tare da hajiya Fauziyya da aka yi shi shekaru 2 da suka wuce ya bayyana a ɗan ƙaramin zagayayyen akwati.
Saurin miƙewa tayi ta ƙarasa jikin ɗakin sai a sannan ta fara jiyo kukan Hajiya Fauziyya tare da ihun niman taimako, ai ko da azama ta bankaɗe ƙofar ɗakin ta shige. Nan ta hango ta yashe a jikin gado daga ita sai bra and underwear wanda ruwan naƙuda dake bin ƙafar ta yayi soaking ɗin shi.
"Subhanallahi!" Saudat ta ƙarasa jikin ta sai kuma ta rasa yaya zata yi don bata tunanin zata iya ɗaga Hajiya Fauziyya da cikin dake jikin ta. Wani kiran ne ya sake shigowa wayar Hajiya Fauziyya Saudat tayi saurin ɗagawa don bata tunanin Aunty zata iya amsawa cikin halin da take.
"Hello Fauza!" Muryar Alhaji Tahir ya doki dodon kunnen ta. Bai tsaya jin ta amsa ba ya ƙara da "kina ina ne nake ta kira baki picking duk kin saka hankali na ya tashi?."
"Ba ita bace Saudat ce matar Kamal "
Rage sautin damuwar da ya bayyana a Muryar shi yayi "Toh ina Fauzan take?" Ya tambaya a kaikaice.
Kafin Saudat ta bada amsa Aunty ta saki razanannen ƙara da ya saka harta Alhaji Tahir dake ta cikin waya sai da ya firgita.
"Wayyo Allah Tahir zan mutu ka taimake ni innalillahi!"
"Naƙuda ne ya tashi mata a gidan Hajiya Luba, yanzu zan fito da..." Bai jira sauraren ƙarshen zancen ta ba ya katse kiran. Itama Saudat jefar da wayar tayi a kan gado sannan ta ɗauki doguwar rigar Hajiya Fauziyyan ta suturta mata jikin ta.
Fita ƙofar ɗakin tayi, Yaseer yana nan wurin da ta barshi, Suhail ya komo kan cinyar shi.
"Yi sauri ka kira min indo Yaseer" ta umarta tare da hanzarin komawa ciki. Shima Yaseer ɗin sauƙe Suhail yayi ya fita da gudu jin desperation ɗin dake cikin muryar mahaifiyar shi.
Ba'a daɗe ba ya dawo tare da indo suka samu har Saudat ta riƙo Aunty sun fito. Nan indo ta kama mata suka yi hanyar waje, ganin halin da ake ciki yasa Yaseer sake ɗiban gudu ya fita kiran driver. Sai aka ci Sa'a har Alhaji Tahir ya kira drivern ta ya faɗa mishi tunda shi yayi nisa kuma zai ɗauki lokaci kafin ya ƙaraso duk da kuwa a take ya taso.
Driver yana jiran su a daidai mashiga na babban farlour suna fita duk suka faɗa motan, Yaseer ma ya shiga gidan gaba ya zauna suka zugi mota suka nufi asibiti aka manta da Suhail.