Sashe 57
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Bai samu barin garin ba ta suntumo ɗanta namiji, sai tsintar zance na yawo Kamalu yayi wai tayi mishi takwara. Ana gobe suna ya cire naira dubu biyar ya bawa maman ɗahiru ta bata ya tattara ya gudu.
Amma duk wanda yazo sunan Kamal sai da Halime ta gwada masa dubu biyar ɗinnan da sunan yaya Kamalu ne ya bawa takwaran shi, sai kuma zani da Maman ɗahirun ta bata, amma sauran matan shi ko biyar.
Ba'a ɗauki lokaci ba yazo da sunan ɗaukan iyalan shi su bar Jama'are baki ɗaya, ya gama ginin shi a cikin Bauchi. Ƴan uwa aka tattaru zuwa mishi murna, kawunan su sai da ya kusan tarwatsewa ganin irin girma da kyawun ginin da Kamalu ya ɗaga.
Amma tun daga wannan Ranar ganin shi a idanun su ya ƙara musu wuya. Domin yakan yi shekaru biyu ko fi bai leƙo ba, sannan sai ka tattari ƙafa tun daga Jama'are kaje gidan ace maka basu nan haka dole zaka juyo, koda Halime ce kuwa.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Kamalu na daɗa arziƙi da hakkin Halime a kan shi wanda bayi da niyyan sauƙewa, yaran shi ma suka tashi da zafin nema ta ko wacce irin hanya amma babu kaman ɗahiru domin shi tun da ƙananun shekarun shi ya san yanda ake juya biyar ya koma goma, gashi yana da ɗan maƙo irin na uban ba kaman su kalabu da idan suka saka kuɗi a gaban su sai sunga bayan shi ba.
Kamalu bai tashi waiwayan Halime ba sai da mutuwa ta ƙwanƙwasa mishi kofa, a wannan lokacin tausayin shi yasa yafe mishi duk abinda yake tsakanin su. Kaman yanda tayi tsammani yana mutuwa rikici ya tashi a kan gadon shi kasancewar yaran shi 7 sun raba uwaye.
Yayi aurarraki bayan komawan shi Bauchi amma duk babu wanda sauran matan suka bari yayi lasting, kuma ko kin samu ciki da boka da taggu sai sun zubar da shi, har Maman ɗahiru ma basu barta ta sake haihuwa ba. amma duk da haka sai da suka tada tarzoma a kan gadon yaran su.
Saboda wasiyyar da kamalu ya bari aka ɗaura Halime a kan komai kuma tayi iya ƙoƙarin ta wajen ganin an yi adalci ba'a tauye ma ɗahiru hakkin shi ba domin shine mai ƙasa da shekaru 18 a lokacin.
Kuma Ɗahirun shine Allah ya zaɓa domin da ya tashi yin dukiya sai da ya ninninka mahaifin shi ya dawo shine ƙarfin sauran ƴan uwan sa baki ɗaya, har suka yi ƙwarin suna a baki ɗaya Nigeria da kewayen ta.
~~~~~~~~~~~
Halime ta yafe hakkin ta amma Yaseer fah?
Ina makomar rayuwar shi da aka gurɓata?
Ina makomar goben shi?
Ina makomar goben Hafsatu Reina?
Shin mummunar ƙaddaran da ta shiga tsakanin su zata ci gaba da bibiyar su kokuwa?
Waye uncle B?
Yana da wani tasiri a cikin rayuwar su?
Mu haɗu da ku a littafi na biyu domin cakwakiyar yanzu aka fara. It will be available on arewabooks by 12/07 and on WhatsApp by 14/07.
Ina miƙa saƙon godiya da jinjina ma Aunty Nafisa usman tafida @Maman Maama
Alkhairin Allah ya kai miki a duk inda kike. You're such an amazing woman with a heart of gold. I wish you all the good things in this world and hereafter ❤️.
Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.
Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 300fcfa posting, document kuma 600fcfa.
*Seemahwrites ✨*