← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 57

Sashe 8

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin saudat ta bar ɗakin taji ana faɗin "A'a haba, wannan kayan barka muka haɗu muka yi, na suna kowa zai gwada bajintar sa ne...."

Saida suka fita daga cikin gidan suka ga yanda gari yayi duhu sosai, ashe hasken cikin gidan ne ya hana su ganin ƙurewar lokaci, wannan ai sai ayi sallar isha ma mutum yana zaune baiji ba, gashi babu masallaci a kusa da gidan.

Bata tsaya duba Kamal na nan har yanzu ko ya tafi ba suka bar gidan domin har yanzu haushin sa take ji.

Tafiya suke  a dogon layin da ya dauki shiru, security lights daga manyan gidajen unguwar shi ya haske musu hanya amma babu kowa a kanta sai motoci ɗai-ɗai da kan zo su wuce.
Tunani take Yanzu ta ina zasu fara samun abun hawa? Idan sun samu ma dame zata biya su? Don kuɗin da ke hannun ta kenan ta bawa Hajiya Fauziyya.

"Yaseer ina kuɗin da inna Larai ta baka?" Koda ba zai ishe su ba sai su ɗan taɓa tafiya kafin su tsari napep, don bata jin a yanayin da ta fara ji yanzun nan zata iya kai gida a ƙafa, ga uban nisa kuma.

"Gashi a nan" ya sauke Suhail a ƙasa sannan ya luma hannu cikin aljihun wandon sa saidai mene? Aljihun ashe ya ɓule don haka bai ji komai a cikin ta ba sai rami.

Daga irin kallon da ya bita dashi Saudat ta fahimci abinda ya faru.

"Allah ga baiwar ka nan, ka shiga lamarin ta ya Allah" ta faɗa a bayyane sannan tace Yaseer ya bar Suhail ya fara takawa da ƙafar shi in yaso idan ya gaji sai ya ɗauke shi domin tafiyar dake gaban su mai tsawo ne.

Su taka su zauna su huta, Yaseer ya ɗauki Suhail yabi ya sauƙe shi, yayi ƙoƙarin nima musu lift idan yaji numfashin mahaifiyar shi yana sama-sama basu samu ba, a haka dai har suka isa lokacin ƙarfe taran dare ta gifta ko sallar maghriba basu yi ba balle isha.

Ba don abincin da suka ci na yau daban yake ba da hanyar nan ya ɗibe shi duka, suna shiga Yaseer ya zari buta yayo alwala a tsakar gidan yayi Sallah don ɗaki har ya fara saka zafi. Ganin har ya gama biyan duka sallolin shi Saudat bata fito yin alwala ba ya saka shi shiga ɗakin amma halin da ya ganta a ciki ya matuƙar razana shi.

*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

*REINA 💍*

Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

06.... Durƙushe Saudat take a kan guiwowin ta cikin azabar ciwo, tana faman juya kai da ciza laɓɓen bakinta, har Yaseer ya shigo ya same ta a cikin wannan hali.
Da gudu yayi kanta ya riƙe ta cikin kaɗuwa yana tambayar abinda yake damunta.

Riƙo hannun shi tayi cikin dagewa tace "Yi gudu ka kira min danejo Yaseer" sannan ta hankaɗa shi kaman hakan zai ƙara masa sauri ne. Ya kusa faɗi ƙasa yaci da baki amma ya ƙoƙarta ya ruga a guje ya bar gidan cikin Sa'a Suhail har barci ya ɗauke shi dan ko shima yaji gajiyar a jikin shi.

Buga ƙofar falangen yake da iya ƙarfin shi wanda har sanda sauran maƙwafta suka leƙo shi ta katanga don ganin ko wani abun ne yake faruwa kafin jikar danejo ta buɗe ƙofar da magagin bacci a idanun ta.

Bai tsaya sauraron tambayoyin ta ba ya faɗa cikin gidan zuwa ɗakin da ya kasance na ƴar tsohuwa mai shekaru 61 a cikin gidan, da aci balbal ɗinta a bakin ƙofa yana haska mata duk mai shiga da wucewa don yin aikin gadin ta na sa kai.
"Danejo muje, Ummana dan Allah" yace yana mata rawar banjo kamar mai jin fitsari saboda matsuwa.

"Haihuwar ce tazo?" Ta miƙe da ƴar saurin ta sannan ta janyo zanin ta daga kan ƙofa ta ɗaura a kan underwear dake jikinta ta nemi riga da hijabi ta saka sannan suka fice a gidan.

A yanayin da ya tafi ya barta suka dawo suka same ta ga baki ɗaya ta jiƙe sharƙaf da zufa amma ruwan naƙuda bai fashe mata ba tukunna sai nuƙurƙusuwa take dai tukun.

"Jeka ka kira min mahaifin ka" tace da Yaseer. Sai ya tsaya turus, gidan Alhaji Tahir kenan zai koma? Idan yaje zai same shi a can ɗinma a irin wannan lokaci ?.

"Bayi kusa Danejo gani nan ko menene ake buƙata zanyi mata" ya gyara tsayuwar shi yana saka fuskar jarumta dukda kuwa gabaki ɗaya jikin shi kyarma yake yi.
Tsakanin shi da Suhail shekaru 6 ne harda rabi an haife shi lokacin bayi da wayo don haka yaune rana ta farko da yaga mahaifiyar shi na naƙuda da idanun shi.

Ta ɗan gutsiri goron ta kafin tace "to jeka gidan malam iro ka kira min Huwaila, kace tazo Saudatu na kan guiwa."
Toh yace, ta Juya ta koma ɗakin shi kuwa ya ɗiba a guje ya fice zuwa gidan da aka aike shi.

Tun da ya hango Yaseer a guje zuciyar shi ya tsinke, Kamal yayi saurin tsare shi don Yaseer baima lura dashi ba. "Ina zaka je? Me ya samu Saudatun?"

"Danejo ne ta aike ni gidan malam iro"

Sai kawai Kamal ya fashe da kuka, shikkenan tashi ta ƙare mishi, Saudat ta mutu a haihuwa ta barshi, sanin cewa Malam iro shine limamin masallacin da ake bada hayan makara da motar ɗaukar gawa. Kyarmar da jikin Yaseer yake yi ya tabbatar mishi da tunanin shi, wataƙil an ɓoye mishi ne shi yasa shima bai fara kukan ba, amma har ya fara jiye musu rashin uwa.

"Saudatu na yafe miki, Allah ya yafe miki, Allah yasa kin huta matar aljannah" yace yana riƙe da hannun yaseer ɗin gamm hawaye nabin idanun shi.

"Abbah babyn bata zo ba fah, ance inyi sauri ne in kira Umma Huwaila"

Kamal ya ɗago kai yana hanzarin share hawaye, "yanzu Saudatun suna tare da danejo?"

Gyaɗa kai Yaseer yayi, kamal yayi saurin angiza ƙeyar shi, "yi sauri kaje ka kira ta, ka tabbatar kun taho tare" da toh Yaseer ya ci gaba da calla gudu a cikin lunguna.

.....

Yana jin ihun ta, yana jin nishin ta, yana jin kukan ta, ba kuma za'a barshi ya shiga ya ganta ba, sannan ya rasa abu ɗaya da zaiyi takammamme ya samu nutsuwa a ranshi, yayi ƙoƙarin shigar da hadda amma kaman yana zuba ruwa a kwando, har zuwa yanzu da yake da tabbacin dare ya raba a cikin hali ɗaya ake, har kukan wahalar da Saudat take yi galabaita yasa ya disashe sai gunji kawai ake ji.

Fita yayi kawai yin alwala ya hango mahaifin shi kwance a ƙofar ɗaki saman tabarma yana shaƙar bacci se faman kai duka yake wa sauro, ai ko halin da Saudat take ciki bai dame shi ba sautin kukan ta ya isa ya hana shi rintsawa. Yaseer ya girgiza kai ya ƙarasa ya ɗauro alwala ya koma ɗaki yaci gaba da nafilolin shi yana yiwa umman shi addu'ar sauƙa lafiya.

Wuraren assalatu Danejo ta fito daga ɗakin itama tayi sharƙaf da zufa don da gaske haihuwar tazo da gardama. Da kamal wanda yayi pillow da dantsen hannun shi taci karo bakin shi a buɗe yawun barci na dalala.

Ƙafa tasa ta shure shi ya tashi a firgice ya zauna. "Ta sauƙa ne?" Shine abinda ya fara tambaya.

"Ban sanin ba soko kawai! Kaje ka taso mana malam Iro yazo da motar gawa kuma"

Tazo zata koma ciki yayi saurin riƙo ta. "Motar gawa dai kika ce Danejo?" Sai ya sake fashewa da kuka "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Shikkenan na shiga uku na a duniyar nan! Yaya zanyi rayuwa babu Saudatu? Me yasa zaki tafi ki barni a irin wannan lokacin Saudatu?"

"Bata tafi ba tukun amma ta kusan tafiyar tunda sokon miji gareta. Dalla yi saure kuzo da mota mu kaita asibiti, ko akwai inda zaka samu abin hawa da wannan lokacin?"

Yayi saurin share hawayen "me yasa zamu je asibiti danejo? Naga duka haihuwanta a gida take yinsu asiri a rufe"

"Toh wannan da gardamar shi yazo ko ni kake so in shiga in jawo shi?" Girgiza kai yayi sannan ya saka takalmi ya fice da hanzari har yana tuntuɓe da ƙofa.

Haka aka zo da motar bakin lungun su, Yaseer ya ɗauki Suhail ya kai shi maƙwafta da aka ce suje can su zauna har su dawo daga asibitin idan ta sauƙa amma yana ajiye Suhail yayi saurin dawowa domin bama zai fara iya zaman har sai sun dawo yasan halin da mahaifiyar shi take ciki ba.

Ya ɗauka musu ƴar jakan kayan haihuwar Saudat da yanzu Huwaila ta haɗa mata ɗan abinda ta samu a ɗakin sannan huwailan da Kamal suka taimaka mata har zuwa jikin motar, jikin ta duk ya gama laushi, a bayan motar duk suka jibgu kaman ragunan layya Yaseer yana faman mata sannu, kamal da malam iro suna gaba har asibiti.

Da ƙyar da suɗin goshi suka yarda suka karɓe ta ganin saida suka bari ta zama sauran gawa kafin suka kawo ta, sai a Sannan ne Yaseer ya zubar da hawaye domin abin ya fara wuce ɗan ƙaramin tunanin shi, Kamal kuwa tunin cewa kuɗin da ya samu ya amso daga wurin Alhaji Tahir yanzu duk karɓewa zasu yi yake yi. Shiyasa bayi son zuwa asibiti, abu kaɗan zasu yi maka amma sai sun ƙwaƙwule maka aljihu.

Ai kuwa ana shiga sallan asuba basu fito ba Saudat ta santalo ɗanta namiji. Aka kintsa su kafin aka bawa su kamal daman shiga su gansu bayan an gyara su an maida su ɗakin hutu sannan kuma Akwai kuɗin kayan amfani da suka ara masa aka yi musu amfani, kuɗin buɗe file, kuɗin gado da kuma kuɗin magani, wai a hakan ma karɓan haihuwa kyauta ne tunda babban Asibitin gwamnati ne.

Saida suka tabbatar ya lale musu dubu sha ɗaya da ɗari shida kafin suka barshi ya shiga ganin jariri, gashi dai yana murna Amma duk sun gama kwashe mishi tattalin arziƙi daman Dubu ashirin ya samu ya karɓo daga wurin Alhaji Tahir yanzu sauran dubu takwas da ɗari huɗu.
Chapter 8 · 0% Book details