Sashe 24
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka yi shewa tare da sake tafawa, Hajiya Hauwa ta taɓe baki cikin ranta tana takaicin missing wannan show da tayi.
"Toh mune mugayen sirakanan kenan?"
Hajiya Lubabatu ta tambaya, tana saka abun da bai samu shiga jakar ta ba a cikin na ƴar ta.
"Toh wa ya sani. Idan ma an kanne mana idanun mu dai bamu gani ba"
"Hajiya nace ban ga Rai na ba" Saudat tace daga bayan kujerar da Hajiya Jummai ke zaune.
"Idan ma zuciyar ki ne baki gani ba ina ruwana! Shine zaki tsaya min sheƙeƙe a ka?" tace tana juyowa ta fuskance ta.
Amma Ashariyar da ta mulmulo mai zafi ya saka duka hankalin su ya dawo gareta.
Bai kai ga hucewa ba Hajiya hauwa ta rako shi da wani.
"Ke Saudatu, uban wa ya baki kayan da ke jikin ki?" Hajiya hauwa ta tambaya tana kallon leshin jikin Saudat Saboda jiƙewar da hijabin jikin ta yayi tun ɗazu ta kai shi kitchen ta shanya, damuwan gaban su yasa basu lura da ita ba sai yanzu.
Gwada Saudat da yatsa Hajiya Farida tayi ta juya ta gwada Hajiya Hauwa dake sanye da irin lace ɗin sakk kafin ta tuntsire da dariya.
"Uban waye ya kyautar da ashoben shi a cikin ku bai sanar da ni ba ya saka ni anko da mutanen karkara?" Ita dai yau bata fito a Sa'a ba.
Kafin ta kai aya Hajiya Lubabatu ta fara girgiza mata hannu ganin tana niman wuce gona da iri "A'a kama kan ki ki iya bakin ki baiwar Allah. Idan ba ƙaranta da rowa ba ma wa ke ajiye sutura har tsawon shekaru 3?"
Ba zata iya jiran su, su gama musayya a tsakanin su ba don haka ta kawar musu da shakkun da suke da shi.
"Hajiya Fauziyya ce ta bani, kuma ya daɗe a wuri na ba kunce bane. Yanzu haka kuma ƴar ta nake nima na rasa, mun duba baki ɗaya gidan da ma'aikatan ta bamu ganta ba"
"Ko dai mahaifin ta ya ɗauke ta sun tafi tare?" Hajiya Farida ta fara shan jinin jikin ta domin rikici idan ba da kai ake ba ya fi daɗin kallo. Tana tsoron wani abun ya rutsa da ita a cikin gidan nan don Tahir ba mutunci yake da shi ba.
Kaman ta tambaya a kunnen shi sai ga kiran shi ya shigo wayar Hajiya Lubabatu.
Tsawa ta daka ma yaran dake ta hayaniya tare da saka yatsa a saman bakin ta, nan wurin yayi tsitt kafin ta danna ta amsa kiran.
"Hello Tahir, ai ina ta ƙoƙarin kiran ka ya ƙi shiga, yaya Fauziyyar ta farfaɗo? Mu ma gamu nan mun kusa isowa"
Yarinyar ta dake daga gefe da ƙyar ta iya ƙunshe dariyar ta jin yanda mahaifiyar ta ke yanko ƙarya, ga muryar ta ya canza zuwa na damuwa lokaci ɗaya.
Ta cikin wayar Alhaji Tahir yace "sun shiga ta ita tiyata kafin a rasa abun cikin ta. Dan Allah Addah idan akwai wa'inda suka rage a gidan su duba mana Reina a zo mana da ita." Daga jin muryar shi ka san ya ci kuka ya ƙoshi. Kafin ta sake cewa wani abu ya katse wayan.
Nan suka bazama niman ta har ɗakunan sama amma shiru, zuwa lokacin kam da gaske hankalin su ya tashi. don haka Yaseer ya fita cikin ruwan ya sanar ma security, babu ɓata lokaci suka sako rigan laida da tochila sannan suka shiga zagaye gidan.
Haske ya dallara ma abun da ya gani yana motsi cikin duhun rumfar wurin.
Ta rintse idanun ta tare da kare fuskar ta da hannun ta, sai ya sauƙe hasken kana ya ƙarasa wurin cikin sassarfa.
Sake haskata yayi da isar shi don ya tabbatar da lafiyar ta. Kayan jikin ta da ya kasance kalar rigan jikin shi a jiƙe, amma har ta fara bushewa saboda daɗewar da tayi da samun mafaka.
Sai kuma ƙaramin cake ɗin nan ta ɗauko shi sukutum ta ajiye a gaban ta ga hannun ta na hagu da take cin cake ɗin da shi yayi dama-dama.
"Me kike yi a nan?" Ya tambaye ta a dake.
Hannun tan ta ɗaga mishi don ya gani da idanun shi. "K...ket ina ci" tace muryar ta na rawa ko na tsoro ko kuma na sanyi.
Ya san magana da ita ma ɓata lokaci ne don haka ya riƙo hannun ta mai kyau ɗin.
Ƙoƙarin tirjewa ta fara yi. "Aunty duka, ta hana cin ket"
Sai jikin shi yayi sanyi tuna halin da Auntyn take ciki.
Yanzu idan wani abu ya same ta tabbas koda wasu sun riga Reina kukan rashin ta Saboda ƙarancin shekarun ta, amma babu wanda kuka da kewar shi zai kai nata tsayi. bayi mata fatan tashi cikin maraicin uwa, domin wahala yake da shi duk irin daular da kake ciki kuwa.
"Muje zan bata haƙuri ba zata dake ki ba"
Ɗazu ma da ya roƙa mata Auntyn bata dake ta ba dan haka yanzu ma sai ta gyaɗa kai.
"Toh ɗauka min ket ɗin"
Babu musu ya ɗauka.
"Goye ni"
Sai da ya ja numfashi kafin ya tsuguna a gaban ta, ta hau bayan shi ta kwanta luff don sai yanzu ta fara jin sanyin na ratsa ta.
A haka suka isa parlourn yanda mutanen cikin ta suka yi kansu yuuu.
Bai samu damar sauƙe ta ba Hajiya Lubabatu ta fisgo ta da ƙarfi har sai da ta saki ƙara tace "ke sake ni!"
Bata saurare ta ba ta raɓa ta a kafaɗa sannan ta fara bin Yaseer da kallon tuhuma.
"A ina ka samo ta Yaseer?" Saudat ta tambaya.
Ya buɗe baki zai amsa Reina ta amshe da "Yatir ne ya kai ni cin Ket"
Sai ya ɗan waro idanu jin yanda ta juye laifin kan shi.
Kiran Alhaji Tahir ne ya sake shigowa don haka ba su bawa abinda tace muhimmanci ba tunda a gaban idon su ya fita nemo ta don haka basu kawo komai ba a ran su, suka yi shirin tafiya asibitin don ruwan ya tsaya.
......
_Tsakanin Gini da Rusau_
_Tsakanin Rayuwa da mutuwa_
Wani ɗan sanyi ne mai sosa jiki ya ratsa ta kafin komai ya fara. Tana jin shi a sihirce, yana shige mata cikin ƙashushuwa da ɓargo.
Idonta a rufe, zuciyarta na kaɗawa kamar na mutum da ke neman gudu amma ƙafafunsa na sarƙe da igiya.
A hankali.. wani haske mai sanyi ya fara bayyanuwa a cikin duhun zuciyarta. Muryoyi masu nisa suna mata raɗa a cikin kunnuwar ta. Tana ƙoƙarin buɗe ido amma sun yi mata nauyi. Ta so ta motsa hannunta amma tamkar an daure ta da karfe. Sai zuciyarta ta hau bugawa da ƙarfi – da sauri – da ƙarfi – da azama!
Cikin kankanin lokaci, jikinta ya hau karkarwa. Haƙoranta suka matse da ƙarfi, fuskarta ta tsame, ta soma jan numfashi a wahalce.
"Fauzah! Kina ji na?" Allhaji Tahir ya damƙi hannun ta sannan ya shiga girgiza ta a hankali, kaman idan ya kira sunan ta zata buɗe baki ta amsa komai ya dawo dai-dai.
Alhaji kalabu da suke tare a ɗakin ne yayi dabaran danna abun kiran likita daga jikin gadon da take kwance.
Babu ɓata lokaci har su biyu suka shigo ɗakin da gudu suka yi kan ta.
“Convulsion!” likitan ya faɗa, yana kallon agogo.
“Postpartum eclampsia. Magnesium sulphate, yanzu!”
Ɗayan yabi umarnin shi ya shiga haɗa abun buƙata don sun tsammaci hakan ganin yanda jinin ta ya hau ga halin da aka kawo musu ita asibitin.
Shi kuma ya fara lallaɓa Alhaji Tahir ya fita ya basu wuri, domin baki ɗaya ya gama rikicewa.
Cikin mintuna kaɗan aka dora mata drip, aka saita na’urorin kulawa. Hancin ta na yoyo, idonta a buɗe amma ba ta ganin komai. Jikinta na rawa kamar wacce take tsaka da cin karo da wata duniya marar iyaka.
A can cikin zuciyarta kuma, tana jin wani murya... mai sanyi, mai laushi.
“Fauziyya! Reina na jiranki. Maama ta zo duniya, amma ke ce ke da ita, na yi alƙawari.”
Luff idanun suka koma suka lumshe, a hankali jikin ta ya sake, ta ja dogon numfashi kafin a hankali numfashin nata ya daidaita.
.....
Tsoro yake yi kada yanzun ma ta sake tashi a yanayin da zai ɗaiɗaita zuciyar sa.
Duk da cewa yana da jibgin ayyukan da basu rabuwa da shi a kullum, duk da ba rasa masu kula da ita aka yi ba amma ya gagara matsawa ko nan da can.
Ya kasa ci ko shan komai, ko Sallah ma a ɗakin yake yi.
Idan wani abu ya samu Fauziyya yaya zai yi da jaririyar kwana biyu? Yaya zai yi da Reina? Ba wannan ba ma yaya zai yi da kan shi?.
Ummi ne ta shigo da basket ɗin abinci. Ya share hawayen idanun shi tare da jan hanci kafin ya gyara zama yana mata sannu da zuwa.
Ƙura masa idanu tayi yanda ya faɗa ya zabge a cikin kwanaki 2 kacal, kafin ta saki murmushin da bai kai zuciyar ta ba.
"Idan damuwar da kake ciki har ya kai ka dawo haka Tahir ni kuma in ce mene?"
Kallon ta yayi sheƙeƙe, ba don matar nan ita ta haifi Fauziyya ba da yace bata da hankali. Yaran ta nawa? Yanzu ko mutuwa Fauziyyar tayi ai bata da asara amma shi ita kaɗai yake da, Kuma bayi jin akwai kamar ta a faɗin duniya. Ta ina ma zai fara hango rayuwar Reina a hannun kishiyar uwa?...
"Gashi cinye min yanzun nan" ta katse tunanin shi ta hanyar miƙo mishi plate mai ɗauke da tuwon semo miyan taushe.
"A ƙoshe nake Ummi"
"Toh zaka fita ka bar min ɗakin nan kuwa. Kuma ina da hurumin Shari'a da kai a kan dalilin da yasa kuka bari hawan jini yayi mata tsanani har ya jawo mata sarƙewar haƙori ba tare da sanin mu ba. Idan Fauziyya tana da ƙaramin tunani kai ma shi gare ka?"
Karɓan plate ɗin yayi yana jin nauyin ta na ƙaruwa mishi.
Yana taryo watannin baya tabbas da laifin shi a cikin damuwar ƴar ta, da ya fahimci tsananin ta yayi yawa a kan Reina, da yake ganin kamar son ta ne bata yi, ga wasu salon takurawa da ta ɗaura mata da sunan tarbiyya.