← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 57

Sashe 30

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta ja iya iskar da huhun ta zasu kai ga ƙarshen huruwa kafin ta saki ihu iya ƙarfin ta tare da zubewa a wurin, abun da ƙwaƙwalwar ta ya bata na gaba kuma shine kai hannu tana murza wurin da man ya ƙona ta koda zata ji sauƙin raɗaɗin azaba da take ciki, Amma a maimakon haka sai ta kwaile farar fatar da a yanzu tayi jaa kafin ta fara yin duhu -duhu.

Ihun da tayi ya ankarar da bibalo da kuma sauran ma'aikatan da suke wurin, cikin azama duka suka bar tukwanen su dake kan wuta ba tare da damuwa da lalacewa ko ƙonewar abin da ke cikin ta ba suka yi kan Reina.

Bibalo ta riƙo hannun da take murje ƙafar da shi ta riƙe su gamm tana ganin yanda take mazari kamar mai farfaɗiya.

"Innalillahi mun shiga uku! Hajiya! Inna Larai!!"

Cicciɓar ta tayi zata yi ciki da ita yayin da mutan gidan suka fito itama Inna Larai lokacin ta dawo daga banɗaki, duk suka yi turus na tsawon second guda suna kallon Reina a hannun Bibalo kafin ƙwaƙwalwar su ta fara aiki. Rabon Inna Larai da tayi gudu har ta manta amma yau kam shi ta ɗiba zuwa sashen su na masu aiki ta wuce kitchen, cikin bokitin da suke ajiye kamu ta tsoma hannun ta biyu za ta ɗibo.

Hajiya Lubabatu kuma karɓan Reina tayi daga hannun Bibalo bayan ta gama narka musu ashariyar da har yanzu bata ji alamun ya ishe su ba. Sai ma ƴar ta ne tayi tunanin kiran driver da wayar ta ya fito da mota cikin gaggawa.

Inna Larai na dawowa ta shafe ƙafafuwan Reina da kamun nan sannan ta ciccibeta daga hannun Hajiya Luba tayi hanyar waje da gudu, tana fita kuwa taci karo da driver da kuma mota na diri alamun an riga an sanar da shi, bata yi wata-wata ba ta saka ta cikin motar.

Zata shiga ta daya ɓangaren Hajiya Lubabatu tazo ta fisgota ta yasar har ƙasa. Kafin ita da yarinyar ta suka shiga cikin motar da ya karaɗe da kukan Reina, ta gama jiƙewa da zufa, hawaye da majina, driver ya zuge su zuwa asibiti mafi kusa.

.....

Zai iya rantsewa ko lokacin da aka kira shi aka sanar masa cewa mahaifin shi ya rasu bai shiga irin tashin hankali irin na yau ba.

Bankaɗe ƙofar ɗakin asibitin Alhaji Tahir yayi ya faɗa ciki kai tsaye.

Hango ƴar shi kwance ƙafafuwan ta zuwa guiwa naɗe a cikin bandeji ya gaskata masa abin da aka kira shi aka sanar da shi mintuna 17 da suka wuce.

Barci ya ɗauke ta, amma kana gani ka san ba a daɗin rai take yin shi ba. Ga wasu ƙananun kuka da ke bin numfashin ta Saboda wanda ta sha ɗazu.

Ya ƙarasa gaban gadon ya durƙusa a kan guiwar shi yana kallon ta tun daga kai har ƙafa, Tsoron taɓa ta ma yake ji, yana ƙoƙarin kimanta yanayin da take ciki a ran shi.

Ya fi tsawon mintuna goma a ɗakin, su kuwa sun ƙame a jikin garu kowa yana tsoron numfashi mai ƙarfi don basu san da me yazo ba.

Daga ƙarshe dai ya miƙe, ya juya ya fuskance su ɗaya bayan ɗaya, kowa ya sha jinin jikin sa.

Amma kafin ya buɗe baki yayi magana sai ƙaran sauƙan mari suka ji tass.

Hajiya Lubabatu ta sauƙe shi ma Inna Larai.

Riƙe da kunci ta ɗago tana kallon matar da ta girmewa nesa ba kusa ba. Matar da aka yi zaman amana da daɗi ba daɗi, ta zauna da ita tun tana cikin ƙuruciya har ta hayayyafa ta aurar ta fara samun jikoki a yanzu.

"Ha...jiya zagin bai... Isa ba harda mari?" Ta tambaya bakin ta na rawa, ga ƴar ta bibalo tsaye a wurin tana kallo.

"Wallahi kika yi wasa sai na ƙara miki, matsayiyata mutanen banza kawai, wanda basu san mutunci da alkhairi ba. Duk yanda mutum ya kai ga saka ku a inuwa Sai kun kai shi rana. Ko mene ƙaramar yarinya tayi miki kamar wannan sai ki ɗau fansa ta hanyar ƙona ta? Saboda tsananin zalunci da baƙin hali?"

Ta yi ƙoƙarin gyara wasu daga cikin halayen Reina, ta so tsanantawa a kan gyaran, ta taɓa hukunta ta a kan laifin ta, yarinyar ta kalli cikin idon ta tayi mata zagin da ta shekara wurin 30 rabon ta da jin shi. amma tunda ta kai ƙarar ta wurin Hajiya Lubabatu gudun ta ɗauki mataki a hannun ta aka bi bayan ta tare da kashe mata warning na ta fita harƙar ta, daga nan ta sare da lamarin Reina.

"Haba Hajiya! Haba Hajiya! Ko menene Hafsatu tayi min me zan ribanta idan na mata lahani? Alkhairan da Fauziyya tayi min a lokacin da nake tsananin buƙatar su yafi ƙarfin in kalli ƴar cikin ta da wani abu bayan soyayya. Zagawa nayi ban ɗaki na dawo na samu hakan ta auku, tsautsayi ne Hajiya"

Alhaji Tahir dai na tsaye zuciyar shi na tafasa. amma kuma yana son yaji yaya aka yi har aka haihu a ragaya shiyasa bai ce komai ba.

"Ni dai ki tattara naki ya naki da sauran wanda kuka haɗa baki. Kaii bani son ganin wata mai aiki ko ɗaya dake a ƙarƙashin ki a gida na, tunda da su aka haɗa baki, ah toh, idan ba haka ba ace suna zaune a wurin kuma su ba makafi ba? To wallahi kafin in dawo, duk ku tattara ku bar min gida, idan nan da minti 30 yayi baku tattare komatsan ku kun fice ba sai na saka anyi min fata-fata da ku da shirgin ku"

Babu shakka ta fahimci don ta wanke kanta a gaban mahaifin yarinya take wannan magananganun, amma menene sai ta ɗaura mata laifi.

"Shekaru Ashirin da bakwai, muna tare tsawon shekaru Ashirin da bakwai Hajiya, anci an birne tare da ni..."

"Ko minti ɗaya ba zan ƙara a kan talatin ɗin nan ba Larai!" Ta gwada mata haryar waje tana mata muzurai.

"Allah ya bata lafiya, sai anjiman ku" ta juya ta fita sauran suka bi bayan ta. Ya rage daga Hajiya Lubabatu da ƴar ta sai kuma Alhaji Tahir da mai ƙuna a ɗakin.

Ta juyo zata fara magana "wallahi, Tallahi, Tahir ban..."

Nuni yayi mata da ƙofa shima. "Kije kawai sai na nime ki"

A kiɗime ta zare idanu, mai yake nufi da sai ya nime ta? Ina zancen sabon kasuwancin da zasu haɗa hannu su buɗe shi tare? Wanda shine ma ƙarfin tunda shi zai bada kashi 65 na Jarin, shi yasa ma taji daɗi da ya zaɓe ta a matsayin wacce zata riƙe Reina.

"Billahilla..."

"Addah babu ruwan ki da abinda ya shafe ni ko iyali na daga yau. An baki amana kuma kin ci, na gode. Dan Allah ki bani wuri kafin alaƙar dake tsakanin mu ma in datse shi"

Cikin sanyin jiki ta tunkari ƙofa idanun ta ya sauƙa cikin na sauran ƴan uwan su mata da maza da suka iso lokaci guda kaman haɗin baki. Ratsa tsakanin su tayi ta wuce, itama ƴar ta na biye da ita, amma babu wanda yayi ƙoƙarin tsaida ta ko kuma ya bi bayan ta, sai ma ƙoƙarin kutsa kai da suka yi cikin ɗakin amma a kan fuskokin su Alhaji Tahir ya rufo ƙofar ya saka masa lock.

Ya ƙara ma Reina gudun Ac saboda zufan da ke kan keto mata kafin ya ƙarasa jikin gadon ya ciro wayar shi.

Hoton raunin ta ya ɗauka ya tura ma Fauziyya ta Whatsapp tare da saƙon da yake cewa 'Idan kinga dama ki dawo' ya maida wayar aljihu Sannan ya koma ya zauna cikin rasa abun yi.

.....

Share zufan kan goshin shi yayi da handkerchief ya mayar cikin aljihun 3 quater ɗin jikin shi kafin ya sauƙe tukunyar daga kan murhu saboda wutan yanzu yayi ƙasa sosai.

Ya zazzage tokan da ya taru, kana ya miƙe zuwa wurin da aka jingine buhun gawayi ya saka parker ya ɗibo. Juyowar da zai yi yaci karo da Suhail ya saka hannu ya dumbulo dambu yana zubawa a cikin rigan shi, sai yarfe hannu yake yi saboda zafi.

Taku ɗaya biyu Yaseer ya riƙo shi.
"Mayar!"

"Yayan mu dan Allah, ma su Ibrahim zan kai wallahi, basu yi yanka bane su" yace yana ƙoƙarin ƙwacewa.

Ajiye parkern gawayin Yaseer yayi ya riƙe shi hannu biyu. "Don basu yi yanka ba sai aka ce kai kayi sata ka basu? Bari yanzu umma zata zo ta same ka".

Motsin fitowar Umman da suka fara ji ya saka Suhail tsurewa. Gashi ko motsi ya gagara balle ya ƙwace ya gudu, kuma ya san idan ya kuskura ta kama shi toh Allah ne kadai mai iya ceton shi.

"Yayan mu dan Allah kayi haƙuri, wallahi Allah ba zan sake ba, na tuba."

Sai da Yaseer ya mayar da naman tunkunya kafin ya sake shi ya ɗiba da ɗan banzan gudu yayi waje lokacin da Saudat ta fito riƙe da bokitin wanka.

Kwafa tayi bayan taga ƙyallin wucewar shi.
"Ai da ka jira ni nazo na same ka kayi min bayani da harshen larabci"

Duba suyan dambun tayi tace Yaseer ɗin ya ƙara kaɗan kawai ya sauƙe,

Sannan ta wuce ɗaki don shiryawa.

Da ya gama ya haɗo da tsokar da ta soya ya shigar mata ɗaki. Babu ɓata lokaci ta fara kakkasawa a cikin laidoji ana ƙara mishi auki da ƙashi da cin-cin tunda naman dama ba wani yawa can yake da shi ba. Adashen layya su kamal suka yi a wurin aiki fiye da su goma a kan saniya ɗaya madaidaiciya sai kuma naman da aka basu kyauta daga kamfani.

Amma alhamdulillah duk an ƙuƙƙulla ma maƙwafta kuma su ma zasu samu wanda zai kwana musu biyu suna motsa baki.

"Umma nace ba" Yaseer ya kira ta yana ƙulle laidar bayan an gama kaso.

"Ina jin ka" ta amsa tana kai soyayyen hanta baki.
Chapter 30 · 0% Book details