Sashe 20
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushin ƙarfin hali Hajiya Fauziyya tayi don abin ya dake ta, tana son ta tambaye ta ko an kai mata kuɗi ma kuma nawa aka bata amma tana tsoron jin abinda yayi saɓani da sanin ta.
"Ina ga na manta ne da nazo haɗa kayan, kin san kai yayi zafi"
Saudat ma taya ta dariyar yaƙen tayi tace "gaskiya kam"
"Amma akwai wani a ciki, kafin ku tafi zan duba miki zaku ji daɗin shi sosai kamfani ne mai kyau"
"Allah ya saka da alkhairi dai Aunty. Ko godiyan abin da ya kawo mu bamu fara ba har an ƙara mana wani?!."
Ɗan hararan wasa ta cilla mata "Yaya kike wani magana kaman ba'a zama ɗaya ba?"
Kallon annurin dake fuskar ta tayi da kuma yanda ta rungume jaririn ta dake cikin tsumma a jikin kayan ta mai kyau ba tare da wani ƙyanƙyami ko makamancin shi ba.
Hawaye ne suka cika mata idanu sai da ta ɗan zamo daga kan kujerar tace "Aunty bani da bakin da zan iya gode miki. Abinda zan iya cewa kawai shine Allah yayi miki abinda kika yi mana, Allah ya rufa miki asiri duniya da lahira. Allah ya gwada mana ranar da zamu saka miki da kwatankwacin alkhairan da sanin ki ya jawo mana. Allah ya albarkaci zuri'ar ki aunty" sai ga hawayen ya gagara riƙuwa mata ya samu daman zubowa a kan fuskar ta sai ta kifa kai kawai tana yin shi a hankali.
Itama Fauziyyar ƙwalla ne cike a idanun ta, sai tayi gyaran murya tare da faɗin "Ameen Umman Yaseer. Toh yaya sunan baby?"
Ɗago kai Saudat tayi cikin muryar kuka tace "Sabir"
"Ashe shima sunan ƴan gayun ne da shi"
Sai suka saka dariya sannan Saudat ta fara share hawayen ta da ƙasan hijabin ta.
Tissue Hajiya Fauziyya ta zaro mata daga kwalin dake kan table ɗin gefen kujeran ta. Saudat ɗin ta karɓa ta share fuskar ta da hancin ta sannan ta miƙe ta nufi dan akwatin da take tunanin kwandon shara ne.
"Ki taka abin da ke gaban ki zai buɗe" cewar Hajiya Fauziyya da ta lura da ruɗun ta Saudat ta shiga.
Ta san kwandon shara mai irin takawan nan amma bata taɓa ganin irin wannan ba, cikin shi harda wani ɗan jan haske idan ya buɗe din.
Dawo da duban ta kan Yaran tayi yayin da suma suka dawo da duban su daga kan mahaifiyar su. Suna kallon juna ta sake musu murmushi, suma sai suka murmusa mata, kuma wannan murmushi daga ƙasan zuciyar Yaseer ya fito, yana ƙulla wasu alƙawura da zuciyar shi, yana ajiye su a matsayin su kuma a lokacin su. Wanda ya saka mahaifan shi murmushi shima sai ya murmusa, wanda ya saka su kukan daɗi shima sai yayi kukan daɗi.
"Yaseer yaya school? Yana maka daɗi dai ko?"
"Alhamdulillah Aunty, akwai daɗi"
Ta jinjina kai alamun gamsuwa.
"Ina Baby Reina?" Ya tambaya da saida mahaifiyar shi da ta dawo wurin zaman ta ta shiga mamaki har ya riƙe sunan da ta kasa tunawa.
Miƙewa tayi, "bari ma in duba ko sun gama sai in kawo muku Ita. Ku ƙaraso dining a kawo muku abun karyawa umman Yaseer"
Abun karyawa kuma da rana tsaka? Shine abinda tace a zuciyar ta a fili kuma ta furta "A'a Aunty a ƙoshe muke sai da muka karya muka fito, kuma ma yanzu zamu wuce"
A kan kujerar da yake Suhail ya shiga rawa "yayyy zamu ci Nama!!" Yaseer yayi saurin riƙe shi ya tsayar da shi wuri ɗaya cike da kunya.
"Ga ma bandan kifi da muka kawo muku tsaraba babu yawa yana bakin ƙofa," sun bar shi a waje ne kada ƙarnin kifin ya cika mata parlourn ta mai ƙamshi.
Da kanta ta fita ta ɗauko, tana shigowa mai aikinta ta ƙaraso da gudu ta karɓe kwalin zata wuce da shi kitchen ta tsayar da ita, babu daɗi ayi maka kyauta ka gwada oho da shi don haka ta buɗe kwalin ta ɗauko kifin guda ɗaya tana jujjyawa.
"Masha Allah sabon gashi ne ma, daman ina da yaji na mai daɗi yau babu cin abincin rana kenan a kai zan dira"
Duka suka saka murmushi kafin ta je ta ɗauko musu Reina bayan ta wanke hannun ta.
Ta matsa a kan su ci abinci zata saka a maida su da suka so yi mata fulako.
Ai ko bata saka a maida su ba wannan karon tafe take da kuɗin abun hawan ta, don ba zata taɓa manta hanyar wannan gidan da wancan daren ba, tafiyar da ya jawo mata naƙuda.
Sai da suka ci suka yi nakk suka huta ma kafin bayan sunyi azahar suka yi shirin tafiya.
"Yauwa saka min numbern ki a nan Umman Yaseer ana sada zumunci lokaci zuwa lokaci." Ta miƙa mata samsung ɗin ta bayan ta shiga mata yanda zata ajiye lambar.
Kallon wayan Saudat tayi na ƴan daƙiƙu tana jin sulɓin shi a cikin hannun ta, gashi ƙato amma bayi da nauyi.
Tana kaffa-kaffa ta saka mata lambar ta mayar mata da wayan da hannu bibbiyu sannan Hajiya Fauziyya ta danna kira.
Rakani kashin dake jakar Saudat ya ɗauki ruri da ƙara sosai kafin Hajiya Fauziyya ta katse kiran.
"Kiyi saving, kuma nima idan na samu fitowa zan zo miki. Gashi goron Arba'in, na gode"
Da ƙyar Saudat ta karɓi katon laidan, buɗewa tayi a wurin ta leƙa don ta san irin godiyar da zata sake yi.
Kayan shafan yara ne a cikin packaging ɗin shi kaman yanda tayi mata alƙawari. Sai turmin zanin atamfa da kuma lace ɗin da dangin uba suka yi ashobe a sunan Reina duk da Saudat ɗin bata san da hakan ba tunda bata je ba, sai turaren yara guda biyu, sai kuma Comfort na wanki.
Don taji yaron na ɗan ƙarnin nono da ta ɗauke shi.
Saliha A Na'ibi (Seemahwrites)✨
*REINA 💍*
15....... Lokaci! Lokaci!! Lokaci!!!.
Tafiyar shi kaman iska yake, baka ganin shi. Kaman fita da shigar numfashi, baka lura da shi. Kaman bugawar zuciya, bayi canzawa. Amma idan ka ɗan juya baya kaɗan zaka fahimci cewa kamar iskar, zaka ji shi a jini da jikin ka. Kamar fita da shigar numfashin, yana zuwa da sauye-sauye a lokacin zafi, sanyi, hunturu da kuma damina. Kamar bugawar zuciyar, ya tafi da shekaru, girma da canzawar halitta.
Fitowa tayi a siɗaɗe daga kitchen ɗin zuwa parlourn da masu aiki ke hada-hada, hannayen ta biyu riƙe da kwalin happy Hour ga bakin ta yayi kalan orange.
Packet na uku kenan da ta ɗauko ba tare da sanin Auntyn ba domin na biyun ma ƙwacewa tayi kuma tayi mata faɗa. Sanye take da farin riga daddy mai adon purple iya guiwar ta, shima gaban rigan ya rine da kalar juice ɗin.
Kwalin ta kai bakin ta, ta kamo straw ɗin da harshen ta kana ta cigaba da zuƙa hankalin ta a kwance tana tafe tana kallon shirye-shiryen da ake a gidan.
Duk wani kayan fashewa ko na ado da yara za su iya ɓarnan shi suke ɗagawa zuwa ƙaramin parlourn auntyn masu decoration ma suna ta aikin su na jera flowers da balon balo a ƙaton allon dake ɗauke da hoton ta da Daddyn ta ya kira photographer na musamman aka ɗauke ta jiya, Gefen hoton an rubuta (Big 3) sai kuma sunan ta daga ƙasa.
Ƙarasawa wurin masu decoration ɗin tayi tana tura cikin ta da ya tashi ya tsaya kamar mai juna biyu, tana ci gaba da zuƙan kayan ta tana kallon abin da suke yi.
"Hajiya ƙarama Bari in ɗaga carpet ɗin ko?."
Ta jita sarai, ta fahimci da ita ake yi kasancewar haka duka masu aikin gidan suke kiran ta, Hajiya ƙarama, amma kula ta ne bata yi niyya ba.
"Hajiya ƙarama!"
Dj dake testing speakun shi ne ya saki kiɗa a wurin, ta washe baki sannan ta fara takawa a wurin tana tsalle, tama manta da halittar me aikin a wurin.
Har ta gaji da tsayuwa gashi juice ɗin dake hannun Reina ya fara zuba a kan Farin chinese carpet ɗin. Tsoro ya fara kama ta don an ajiye carpet ɗin a wurin ne saboda ado kawai ba na takawa ba, sai aka ɗaura masa wani ƙaramin bookshelf da kayan ƙarau da kuma fulawowi a kan shi, ba'a hawan shi saboda kalan shi.
Amma saboda an riga an ɗaga book shelf ɗin kuma an canza fuskar parlourn yanda zai bawa masu decoration abin da suke so shi yasa har ta samu daman hawa kai.
"Hajiya ƙarama dan Allah ki sauƙa" tace da ƙarfi cikin ƙaran kiɗan kaman zata saka ihu tare da ɗan taɓa ta kaɗan amma sanadin bata tsammaci haka ba yasa tayi tangal-tangal zata faɗi.
Riƙo ta mai aikin tayi kafin ta shiga uku, Reina tayi saurin ture hannun ta daga jikin ta tana bin matar da ta girme wa uwar ta nesa ba kusa ba da kallon banza, kafin ta saki kwalin juice ɗin ya fara zuba a kan carpet ɗin ta jikin straw.
Tayi saurin duƙawa ta ɗaga kwalin amma kafin ta kai ga miƙewa Reina ta wafce shi.
"Uwar ki!" Cikin Sa'a a lokacin Dj ya kashe kiɗan, yayin da amon ashariyar ya karaɗa cikin falon baki ɗaya hankalin mutane ya dawo kan ta da mamaki.
Tsoro ne yaso kama ta da yanayin kallon da suke mata, amma taga ai sauran yara ma haka suke faɗa idan anyi musu laifi, har su Jamal ma da suka girme ta.
Sakin kwalin ta sake yi sannan ta bishi ta daka tsalle ta dira a kai, lokaci ɗaya kwalin ya fashe juice ɗin ciki ya fantsamu a jikin ta da fuskar mai aikin dake duƙe har kan kujerar dake kusa da wurin. Farin carpet kan ma ba'a magana don yayi dama-dama.
Ta ware ƙananun yatsun hannunta duka biyu ta yiwa matar danƙwale kafin ta juya ta ruga a guje tayi ciki.
......