Sashe 33
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lafiya lau" ta amsa tana wani kashe murya sannan ta ƙara da "kada in ɓata maka lokaci mu shiga ciki"
Hauka take yi zata saka shi jerawa da ƴammata? Itama yayi imani ko sunan ta bai sani ba.
"No, Ina jiran abokina ne bai ƙaraso ba, kuyi gaba kawai kada in tsayar da ku"
Bata ji daɗi ba don tana ganin shi tace ma ƙawayen da tayi a zuwan ta ɗaya makarantar cewa shi friend ɗinta ne, amma sai bata gwada a fuskar ta ba ta ciro ƴar IPhone ɗinta daga cikin side bag ɗinta ta miƙa mishi.
"Toh gashi saka min number ka idan mun gama sai in nime ka"
Kallon wayar yayi zuwa kan fuskar ta kai tsaye yace "bani da waya"
Ba zallan ƙawayen ta ba har maza guda biyu da suka zo wucewa ta bayan su saida suka juyo suka kalle shi.
Daidai lokacin Muhammad ya ɗaura hannu saman kafaɗar Yaseer yana cewa "aboki na iso muje" sai kuma idanun shi ya sauƙa a kan fuskar yarinyar a take ya washe baki yana faɗin "summy kece?"
Bata kula shi ba ta karɓi wayan ta daga hannun Yaseer cikin ɓacin rai, Bata taɓa haɗuwa da ɗan rainin hankali irin wannan ba. Ta juya tayi gaba abinta ko bin ta kan kawayen tan bata yi ba, amma haka suka rufa mata baya, shi kuwa Yaseer an barshi tsaye kasake don bai ga abinda yayi ba, gaskiyar shi kawai ya faɗa mata.
Hannun Muhammad dake kafaɗan shi ya fara sauƙewa ya ɗan harare shi kana yace "mufa yanzu ba ƴan secondary bane"
Baki Muhammad ya taɓe tare da faɗin "sorry, let's go" suke jera a tare suka shiga makarantar bayan sun gwada ma security admission letter ɗinsu an basu damar wucewa.
Student market suka fara zuwa domin su bayar da kuɗin makarantar a biya musu.
Shaguna sun riga da sun cika da wasu ɗaliban don haka suka tsaya a wurin wanda suka baza na'urorin su a tsakiyar fili sai manyan lema da yayi musu rumfa, suka yi sallama tare da zama a wani benci, saitin wata budurwa da itama tazo nata registration ɗin sai faman yauƙi take yi kaman karkashi.
Bai bi ta kanta ba domin bai ma lura da ita ba suna taɓa hira da Muhammad, sai yayi ƙasa da murya tare da raɗa masa "my friend kalli wata zillaziya a gaban mu don Allah."
Zai ɗago ɗin kaman yanda yace sai kuma ya danne kafaɗar shi tare da faɗin "a fakaice, kada kayi ta gane ta raina mu please"
Bai damu ba ya ɗago ya dubeta, ai kuwa suka yi ido hudu. Fara ce ƙar kuma tana da kyan fuska irin na fulanin usuli ɗinnan amma bayan nan bai ji ta wani burge shi ba. Mummunan hararar da ta watsa mishi ya saka shi tamke fuska ya mayar da hankalin shi wani wurin, cikin rashin Sa'a kuma duk dagowan da zai yi sai sun haɗa idanu kuma bata fasa hararar shi ba, shima sai ya sha kunu kawai.
Sai da aka gama da wata mai niƙab kafin aka zo kanta, tana bada bayanan ta kaman bata son bayarwa amma shi mai shigarwar sai wani rawar ƙafa yake yi da ta gama ma cewa yayi ta bar kuɗin aikin da ya mata ba sai ta biya ba, a yatsine ta ciri miƙaƙƙun dubu-dubu guda uku ta zuba mishi a wurin tayi gaba.
Bai damu ba tunda ya ɗauki number wayar ta a kan profile ɗinta ya juyo kan su Yaseer.
Da Muhammad aka fara kafin aka zo kan Yaseer, ya bashi kuɗin da yazo da su ya ƙirga sannan yace masa saura 1500 kuɗin generating RRR da kuma registration ɗin, harda shirya mishi profile ɗinshi.
Bai san da wannan ba amma cikin Sa'a akwai wasu kuɗin a jikin shi don haka ya cire ya biya, aka gama komai akayi printing musu aka basu daga nan kuma zasu wuce department su biya deparmental dues sai kuma kuɗin SUG.
Kafin wani lokaci Yaseer ya cire wurin dubu goma sha biyar wanda bai san da lissafin su ba daga cikin kuɗin koyarwar da yayi a islamiyya. Ba don Allah ya taimake shi yayi tunanin zuwa da kuɗin ba ma da bai san yaya zai yi ba.
Cafeteria suka je cin abinci, jin kuɗin plate ɗin abincin yasa ya gwammace siyan eggroll da pop cola suka samu inuwar cooldown suka zauna suka ci suka wuce masallaci suka yi sallar azahar, zuwa lokacin har ya fara jigata domin bai ɗauka ɗawainiyar ta kai haka ba.
Daga nan suka wuce bursary domin yin changing teller to receipt. Dogon layin da suka gani yau ɗin ya ƙara sanyaya musu guiwa amma haka suka jona na freshers suma, domin Muhammad ya bada shawarar ko su tafi gida suyi sammako gobe amma yaga gwanda su gama baki ɗaya kawai su huta.
Zaune a gefe idanun shi suka hango mishi Summy da mabiyan ta, sai mamaki ya kama shi na dalilin da ita bata shiga layin ba amma babu daɗewa ya samu amsar shi yayin da wani saurayi ya ƙaraso da receipt ɗinsu duka ya riga ya shiga gaban wasu ya karɓo.
Wato har a tsakanin ɗalibai ma akwai connection, idan kana da ƙafa babu abinda ba zaka samu a cikin sauƙi ba. Shi dai saurayin daga ganin shi ba fresher bane saboda ya ɗan manyanta ga kuma ID card dake saƙale a wuyan shi da tambarin SUG An rubuta 'How may I help you' a jiki, taimakon na masu shafa tozali ne kenan.
.......
A ɗan zaman da Hajiya Fauziyya suka yi a Nijar Aicha ta samu kulawa sosai daga gareta, ga ƙanwar mahaifiyar ta ma dake iya nata ƙoƙarin sai duk ta dawo ƴar gata bayan damuwar rashin uwa da take ciki.
An bar Reina da gallafiri a tsakani tunda kaman ma uwar ta bata da lokacin ta ne, ga daɗin cewa Aicha bata son ganin ta a kusa da ita. Don haka sai ta wuni tana wasa ko game, Alhaji Tahir shi ke niman ta ya bata abincin safe, rana da kuma dare idan ba haka ba sai dai tasha yunwa abunta ba damuwar Fauziyya bane, gata da bala'in zaɓe shi yasa ta daɗa fita sha'anin ta.
Amma ko dan rashin shan faɗan auntyn nata a kullum da kuma rashin zuwa makaranta tana jin daɗin zaman ta a gidan.
Zaune Alhaji Tahir yake yana fuskantar Alaji Abdou dake riƙe da kai.
"Ko kwana bakwai Malika bata yi a cikin makwancin ta ba amma wai so suke yi su ɗaura min wani auren" yace cikin ƙunan rai.
"Kana buƙatar mai kula da Aisha" Alhaji Tahir ya mayar mishi.
Ɗago kai yayi ya kalle shi da idanun shi da suka gaza daidaita kala na tsawon kwanaki "ba zan samu mai kula da ita ba sai nayi aure? Ashe dalilin aure yakan iya zama komai? Ƙanwar ta fa suke son aura min? Ta yaya za'ayi in iya rayuwar aure da wacce na ɗauke ta a matsayin tawa ƙanwar? Idan kai ne haka ya faru da kai sai ka yarda"
Da sauri Alhaji Tahir ya girgiza kai. "Allah ya kiyaye, Ba zai faru dani ba ma in sha Allah. Ka bamu ita mu koma Nigeria zata samu kulawar da take buƙata a hannun mu sai kayi ƙoƙarin daidaita komai a nan ɗin"
"Zata takura ma ƴar ka, ka bari in nemi wata hanyar kawai."
Numfashi Alhaji Tahir ya ja ya furzar don ya san gaskiya ne, ba zai iya jurar hantarar Aicha a kan Reina na tsawon lokaci ba.
"Yauwa maganar meye kace kana son muyi jiya?"
Girgiza kai kawai Alhaji Tahir yayi don bayi son ƙara ma Alaji Abdou damuwa a kan damuwar da ya riga yake ciki amma sanar da shi alkhairin da ya samu a kan wannan project da yaso hana shi yake son yi da kuma niyyar shi na sake komawa a karo na biyu da yawan kuɗin yayi niyyar zubawa tun farko.
"Kada ka damu, babu komai, Allah ya jiƙan Malika"
Da ameen ya amsa ya maida kan shi baya ya jingina yana ci gaba da mata addu'a da nima mata gafara a wurin Allah lokacin da kawunan shi da mahaifin Malika suka shigo ƙaramin parlourn da sallama.
Niman wuri kowannen su yayi ya zauna sannan suka dubi Alaji Abdou da idanun shi ke rufe dukda yaji shigowan nasu amma sanin abinda suke tafe dashi yasa ba zai kula su ba.
Da faransanci suka fara mishi faɗa a kan yanda ya saka mutuwar a ran shi yana jin su bai tanka ba har suka ɗaura da zancen auren da suke da niyyar mishi.
"Kaga yanzu ma ɗaura auren ga, ba sai jimawa ba, sabida dukkanin ku kai da ɗiyar ka ku samu nutsuwa, Mariama zata kula da Aicha kamar ita ta haife ta"
Sai a sannan ya buɗe idanun shi da suka tara ruwan masifa ya zuba musu "haba! Lalla Malika kwana bakwai batai ba cikin kabari!"
"Ai ba munce tarewa zata yi yanzu ba. Amma a matsayin mu babannin ka hakki nai kanmu mu kyautata rayuwar ka, don haka sadaki zaka kawo"
Alhaji Tahir dai ya dawo ɗan kallo, yana ayyana haƙurin Alhaji Abdou a cikin ranshi don shhikam ba'a isa ayi masa wannan iskancin ba.
"Ni babu kuɗi a jiki na"
"Janyo wayarka ka tura, kai ko fa bashi ne sai an ɗaura auren nan" cewar ƙanin mahaifin shi da yafi zaƙewa a maganar.
Ƙarshe dai Alhaji Tahir ne ya ɗauki alhakin biyar sadakin ganin zasu kai ruwa rana.
A lokacin da aka sanar da Mariama zancen auren kuwa suma kawai tayi. Ai su Alhaji Tahir basu ƙara kwana ɗaya a Nijar ba suka tattaro suka dawo gida, domin riciki ne ya tashi Mariama harda tada aljanu.
......
A yau aka buɗe portal ɗin booking na hostel, Zuwa ranan Monday kuma za'a fara lectures. Saudat da Kamal kuma sun gagara samun daidaito a tsakanin su game da zaman shi a gida ko hostel har abin yana son kawo musu sabani, domin Saudat kafewa tayi kai da fata na cewa zaman hostel ɓata mata tarbiyyar yaro zai yi, shi kuma kamal faɗi yake yi tana son ya zauna ne don yana yi mata aiki bayan shi a yanzu karatu ya saka a gaba.