Sashe 18
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga mahaifin ta Alaji Abdou har Alhaji Tahir abun baiyi musu daɗi ba amma kuma mai ƴa ɗaya ce da mai ƴar fari. Kowa a cikin su na ji da nashi kaman kifi guda a cikin teku musamman ma Alaji Abdou da auren shi kusan shekaru goma kafin Allah ya azurta shi da samun haihuwa, kuma bayan Aicha har yanzu da take niman shekaru huɗu a duniya shiru babu labari. Ga mahaifiyar tata ma sickler ce yau fari gobe tsumma shiyasa koda yaso ƙara aure ya sanar da ita ciwon ta ya tashi kaman ba zata yi rai ba ya haƙura ya aje zancen a gefe suka ci gaba da manejin abinda Allah ya basu.
Hajiya Fauziyya kam ko a jikin ta don ta san fidda fice ne kawai irin na yara, don haka ta ɗauki Aicha ta ɗaura bisa cinyar ta tana bata abincin a baki suna yi dukkan su suna taɓa hira sama-sama.
Suna gamawa ana kiran La'asar, saida suka yi Sallah sannan Hajiya Fauziyya ta shiga da matan ɗakin baƙin ta, mazan kuma suka wuce study room ɗin Alhaji Tahir.
"Aunty kin san SpongeBob?"
Gyaɗa kai Fauziyya tayi idanun ta a cikin na Aicha da ta ɗale mata cinya ta tsaya sannan ta riƙo fuskar ta cikin ɗan tafin hannunta tana kallon ta ido cikin ido domin ta samu hankalin ta hundred percent.
"Na san shi"
"Ina da ƙaton SpongeBob a gidan mu. Babba ya kai haka" ta ware hannun ta don ta gwada girman teddyn, kana ta sake riƙo fuskar Fauziyya kafin hankalin ta ya bar kanta zuwa ga mahaifiyar ta da suke hirar arziƙi.
"Masha fah?"
Ta sake gyaɗa kai "Reina tana da teddyn ta itama" Fauziyyar ta biya mata.
"Idan naje gida zan saka nawa a dustbin" tace tare da ɓata fuska, abun har ya basu mamaki ganin fa da gaske take yi zancen bata son Reina amma ta liƙe wa mahaifiyar ta.
"Kin san Omar and Hana, da paw patrol?"
"Aicha, sauƙo!" Malika tace cikin dakakkiyar muryar da ya saka ta sauƙowa babu musu amma kuma bata bar hirar ba, sai ma ta shiga bata shirmen labarin duk cartoon ɗin da take kallo.
Mayar da hankalin ta Wurin Malika Fauziyya tayi bata bar gyaɗa ma Aicha kai ga duk abinda tace ba. "..Toh yaya Nijar? Ina sha'awar ziyartar ƙasar kuwa"
"Nijar alhamdulillah, muna miki maraba, sai kice Tahir ya ɗauko ki kuzo mana ziyara"
"In sha Allah da Reina ta ƙara ƙwari muma zamu zo"
Malika ta kama baki "Toh! Kema halin ku ɗaya da Daddyn Nana. Ina Nigeria ina Nijar da za'a ce sai jariri yayi ƙwari? Tafiyar jirgi saboda daɗi yayi muku yawa ko?"
Fauziyya ta jinjina kai "nima ba ra'ayi na bane wannan, na nata Daddyn ne. Unguwa a cikin garin Bauchi ma yace ba yanzu ba sai ta daɗa ƙwari"
"Idan yayi wasa ko sace ta zanyi in gudu saidai ya tsinto ta a maradi" suka saka dariya dukkan su Fauziyya har tana imagining irin rikicewar da Alhaji Tahir ɗin zai yi.
"Yauwa Fauziyya, faɗa mini wani tanadi kinka yi wa baby Reina?" Cewar Malika bayan ta haɗa Aicha da huruful hija'iyya a waya ko zata barsu su zanta ta daina damun Fauziyya da surutun da tana da tabbacin ba ganewa take yi ba.
Dariya tayi "wani irin tanadi kuma? Na aure?"
Itama saida ta dara kafin tace "kina da abin dariya idan kinka so. Ina nufin tanadin raino, tanadin tarbiyya da kuma tanadin rayuwa irin ta ƴa mace mai buƙatar matuƙar kulawa"
Ajiyar zuciya tayi "akwai wani tanadi ne bayan Allah ya raya mana su da imani?"
Jinjina kai Malika tayi ganin kaman bata da ra'ayi a zancen tace "gaskiya ne, Allah ya kare mana su daga dukkan sharri kuma ya raya mana su da imani"
Sai ta kaikaita hirar ya koma na duniya, Malika tana bata labarin Nijar haka ma Fauziyya na bata na Nigeria sannan suka koma na ƙasa mai tsarki da kuma ƴan yawace-yawacen da suka yi na honeymoon lokacin tana amarya.
Ƙarfe takwas na dare aka sake jere musu dinner suka ci.
Duk yanda Fauziyya da Alhaji tahir suka kaɗa suka rawa firr suka ƙi yarda su kwana a gidan.
"Da gida na da iyali na ka saka ni kwana nan gidan ka Tahir kaman gauro? Lallai ka raina ni" shine abinda Alaji Abdou yace yana ɗaukar Aicha a hannu kana ya riƙo hannun Malika.
"Gobe da sassafe zani Sabon warehouse ɗinnan in duba tare da masu ƙiyasi sai mu kimanta kayan da zai iya ɗauka. In yaso daga baya kuma idan na samu hutawa sai mu zauna muyi maganar shigo da kayan da kuma ɗiban ma'aikata"
Fauziyya na jin maganar ɗiban ma'aikata bata bar shi ya dire ba tace "Yauwa Daddyn Aisha Idan an zo ɗiban ma'aikatan akwai wanda nake so ayi min alfarma a ɗauka"
Maido da hankalin shi gare ta yayi fuska a sake yace "Babu damuwa amarya amma minana ya karanta? Don kin san kula da warehouse munfi buƙatar mai ilimin abin da ya shafi lissafi idan dai ba aikin ƙarfi zai dinga yi ba"
Duban Alhaji Tahir tayi shima ita yake kallo, har ta gaji da ɗago mishi zancen aikin Kamal gashi kuma abun yaƙi barin ranta, kuma har ga Allah shi mantawa yake yi don bai ɗauke shi da muhimmanci ba, yana da ɗaruruwan damuwowin da suka fi wannan girma a kan shi.
Saida ta sauƙe idanun ta daga nashi kafin tace "Ban san me ya karanta ba wallahi, amma akwai takardun shi a wurin Daddyn Reina, diploma ne dai yake da shi, a taimaka ayi mana alfarma dan Allah"
"Haba-haba amarya, ko wanda bai je makaranta ba kinka kawo a bashi aiki sai matsayin da kinka zaɓa, toh ina amfanin damar idan wanda ke jikin naka ma basu amfana ba?. Idan akwai wasu ma ki ƙaro ko su ɗari ne duk ba zai gagara ba in cha Allah".
......
Kusan za'a ce faɗowa gidan Danejo kamal yayi don sallamar da yayi bai jira amsar ta ba ko izini ya shigo yana maimaita kalmar Alhamdulillah a kan harshen shi, fuskar shi kuwa a kallo ɗaya zai gama karantar maka da saƙon farin cikin dake cikin zuciyar shi.
"Danejo da gaske ne, wallahi da gaske ne, naje har sun ɗauke ni aikin alhamdulillahi Danejo" yaje ya zube a gaban tsohuwar dake murmushin jin daɗi itama.
Tun daren jiya kira ya shigo wayan Kamal ɗin wanda babu ɓata lokaci ya ɗauka ake sanar da shi ana buƙatar ganin su interview washe gari kana suka sanar dashi address ɗin warehouse ɗin. duk da hakan ya taɓa faruwa dashi lokacin da yake yaƙin niman aiki kororo-kororo. da suka je wurin aka tara su aka musu tambayoyi kaman abun arziƙi sai da ya dawo aka turo masa saƙo wai daga ma'aikacin wurin ne idan yana so ya shige masa gaba ya kawo dubu hamsin aiki kaman ya samu an gama.
Haka ya kira goggo ya sanar da ita, lokacin itama babu kuɗi a hannun ta don haka ta saka Ragunan ta ƙosassu a kasuwa aka musu siyan kwasha-kwasha ta turo masa kuɗin ya tura musu. Shikkenan kuma yaji shiru, da yayi ƙoƙarin tuntubar layin ma ko tafiya bata yi, yayi tattaki ya tafi wurin amma babu su babu labarin su, rushe tsohuwar ma'aikatar ma ake yi za'a tada sabon gini. Yayi zazzaɓin kuɗin shi a lokacin amma Saudat ta lallaɓe shi ya ɗau dangana.
Sai dai bai yi sanyin guiwa ba a wannan karon ba ma, da safe yayi sammakon shiryawa yaje, ya dai saka ma ransa ko Naira biyar aka buƙata daga gare shi bayi bayarwa.
Sai dai tambari da kuma sunan TK Kingdom da ya gani a jikin takardar da suka bashi na letter of appointment ya tabbatar mishi warehouse ɗin na kamfanin Alhaji Tahir ne.
Kuma information ɗin shi kawai suka ɗauka ba'a yi mishi tambayar komai ba, takardan makarantar shi ma da yaje da ita basu ko karɓa ba balle su duba.
Yaseer da Suhail dake cin abinci ma suka tsame hannun su, murna suka shiga yi, Danejo da Suhail harda taka rawa, ya riƙo hannun yaseer ɗin suna juyi da taku a wurin cikin nishaɗi, Kamal kuma numbern goggo shine abinda ya fara nema ya danna mata kira.
Har hawaye saida ya sauƙa daga idanun shi da yaji irin murnan da mahaifiyar shi ta shiga da kalolin addu'oin Nasara da kariya da ta shiga mishi tun kafin ma ya fara.
"Mahaƙurci mawadaci kamalu, Allah yasa sauƙi ne yazo ma rayuwar ka na dindindin"
_Mukan yi addu'a da dukkan zuciyar mu, da dukkan imanin mu, kuma muna masu yakinin Allah zai amsa mana, amma addu'a sauƙaƙa ƙaddara take yi bata sauya shi, domin babu rayuwa gaba ɗayan ta idan babu ƙaddara, daga ranar da taka ƙaddarar ta yanke daga wannan rana numfashin ka zai rasa makamashi sai ya ɗauke._
Da Kamal ya gama magana da goggo ya kira Saudat bayan ta fashe da kukan farin ciki cewa tayi. "Gani zan fito yanzun nan, zuwa maghriba zan iso gida in sha Allah"
"A'a Saudatu, kisha zaman ki ni zan iso gare ki. Zan iso gida in gwada ma masoya na ribar addu'ar Allah ya taimaka ya shige mana gaba da basu gajiya da yi mana"
Toh tace yana jin yanda take nanata wa mahaifiyar ta abinda yake faruwa cikin ƙaguwa da tsananin farin ciki kafin ya katse kiran.
"In tafi in barku ko Yaseer?." Yace don ya tsokane su.
"A'a Abbah zamu bi ka dan Allah" Yaseer ɗin ya amsa yana rau-rau da idanu.
Dariya Kamal yayi cikin annashuwa yace "kuje ku sauya kayan jikin ku toh, bari naje na siyo muku sabon takalmi ko?"
"Eh Abbah" Suhail yace yana tsalle. "Mai huji-hujin nan nake so" yana nufin crocs domin yana ganin yara a makarantar su dashi yana bashi sha'awa.
Ba canza kaya kawai ba saida Yaseer ya ɗauraye su da ruwan sanyi ya ɗauko musu kayan sallan bara daga ƙasan kwalla ya saka musu sannan ya kusan tittiɗe musu goran turaren shi, ya saka musu hula suka fito suka yi kyau abun su kafin kamal ya dawo da laidan takalman.